Sai da fatan alheri kawai.

Washe gari daurin aure, tin sassafe me kwalliya tazo ta tsarawa amarya kwalliya ta gani ta fada. Amarya ta shirya cikin wata briwn shadda me adon yellow ajiki  sai milk mayafi da takalmi da ta saka.

Duk wanda ya kalli Najwa sai ya yaba da kyan ta tare  da mata addua.

Ango Najib kuma ya shirya cikin wata milk din shadda wacce ta shadda an mata aikin brown zare. Masha Allah Najib ba dai kyau ba. Bare kuma ranar tashi ce, Najib sai washe hakora yake ya kasa rufe bakin sa.

Karfe 10:30 aka daura Auren *Muhammad Najib Abubakar da Amaryar sa Amina Ahmad.*

Inda daurin auren ya samu halartar manya manyab jama'a banda kusoshin gwammnati har da sarakuna.

Daga nan suka tafi walima inda nan aka ci aka koshi aka sha abarkwanci daga nan gidan su Najwa Angwayen su ka wuce.

Najwa na ganin karfe goma da rabi tayi hankalin ta ya tashi duk ta rasa nutsuwar ta jin take kamar ba ita ba. Dan komai da ake sama sama ake yin sa.

Ana daura aure Mustapha mijin Zahra ya bugu yana fada mata. Buda Zahra tayi, su Talle suka kalle ta suka ce,
"Anty an daura ne."

"Eh an daura su Najwa an zama matan aure."
wajen Najwa ta karasa ta ce,
"Amaryar mu  an daura aure Allah bada zaman lafita. Allah kade fitina."

"Ameen yan dakin suka amsa dashi."
Sai wajen karfe daya su Najib suka karaso gidan su Najwa lokacin Najwa na daki tayi shiru ta rasa me zatayi ma.

Maman Sumaiyya ita tazo ta kira Najwa kan angwaye na sitting room suna jiran ta.

Zahra dasu Talle da Khadija da wasu daga cikin kawayen ta su suka rakata dakin dasu Najib suke.

Najib na ganin shigowar ta ya mike yayo wajen ta. Hannun ta ya kamo suka shiga daga ciki. Hotuna aka dinga dauka sai da suka gama da abokan su sannan suka shiga cikin gida dan yi da yan uwa.

Anan  sukai da kakkanin su da iyayen su. Da kannen mahaifan su da matan yayen su Dady. Sun sha hotu inda Najib duk hankalin sa na kan Najwa da yaga ta canja.

Ita kuwa Najwa sai inda akayi da ita dan duk jikin ta ya saki.

Suna gama hoto yaja hannun ta suka fita harabar gidan. Kallonbta ya tsaya yi, Ya ce,
"Baba lafiya?"

Bata kai ga bashi amsa ba abokan wasan su suka shigo gidan nan fa suka fara jan ango da amarya sukai hoto suna ta hira a hankali Najwa ta zame daga wajen.

Dakin Mami ta shiga dan nan ne ba kowa a ciki kwanciyya tayi akan gado tana me lumshe ido, wani sanyi taji yana shiga cikin zuciyar ta. Kanta kuma kamar wacce aka sauke mata wani nauyi.

Ta jima a kwance anan sannan ta mike ta koma cikin jama'ar ta. Karfe biyu ta ta shiga ta canja shiga zuwa atamfa super pink colour ce an mata adon blue. Tayi kyau ita ma.

Ranar ma dai kamar wani yini aka karayi inda masu kidan kwarya suka zo suka buga aka sha rawa.

Kowa ya watse akan gobe za'a dau amarya akai ta gidan ta.

Washe gari tin safe aka shirya amarya cikin wata Atampa holland riga da zani sannan aka rufa mata wata bakar Alkebba baka me adon golding coolour dakin Dady aka ka ta, tana kuka.

A gefen kafar sa ta zaune, kallon ta Dady yayi shima ya goge yar kwallar da ta zubo masa, ya ce,
"Allah miki Albarka. Allah miki Albarka. Allah miki Albarka."

sai da ya fada sau uku sannan ya ce,
"Ban da abinda zan ce miki Najwa dan nasan duk na gama fada miki a baya. Sai dai Najwa ina me kara fada miki kiji tsoron Allah ki rike mijinki da amana sannan ki masa biyayya. Ka san hanyar da zakiyi ki samo aljannar ki a karkashin kafar mijin ki. Ba abinda zan ce Najwa sai da Allah miki Albrka Allah ya baki yayan da su miki biyayya kamar yadda kikai mana. Allah kuma ya saka miki da gidan Aljanna baki taba min komai ba Najwa Allah miki Albarka."

Yayi shiru Mami ma kasa magana tayi sai dai albarka da take sanya mata kawai.

Mama Bilkisu yayar Dady matar gwamann Kaduna ita ta kamo ta zata mikar da ita. Da sauri Najwa ta fada jikin mahaifin ta. Tana kuka.
"Dady ka yafe min."

"Ba komai Najwa na yafe miki baki taba min komai ba Najwa na yafe miki. Alherin Allah ya tabbata a gareki Najwa. Allah faranta miki. Allah bada zaman lafiya."

Jikin Mami tayi tana kuka tana neman yafiyar ta. Mami dauriya kawai take dan ita ma gab take da yin kukan.
"Baki taba batan ba Najwa kullun burin ki faranta min. Allah kima ya baki masu faranta miki. Allah ya kare ki ya bada zamab lafiya."

Ta daga ta, ta mikawa Mama Bilkisu ita. Karbar ta tayi tana rarrashin ta dai dai zasu fita kenan sai ga Hamam Salim nan tare da Basma.

Da gudu Basma ta karaso gun yayar ta ta tana kuka ita ma. Najwa na ganin su ta rumgume su tana kuka kamar ranta zai fita.

Suma kukan suke, lallashin su, aka dinga yi. Tare suka shiga dakin Mamamah wato Takwarar Najwa mahaifiyar Mahaifin Najwa.

"A'ah ya haka kuma. Haba Najwa ta. Haba Najwa ta ai sai ki dagawa iyayen ki hankali. Gashi kin sa ya  uwan ki kuka ko nima kina son nayi ne."

Kai Najwa ta girgiza. "To In dai bakya son nayi kiyi shiru ki daina kinji."
Kai ta gyada mata.

"Yauwah koke fa kuma kuyi shiru ai Najwa bata bar ku ba. Bakwa ganin wanda ta aure yayan kune wanda rayuwar sa ma yayi a cikin gidan ku duk kun zama daya. Dan Allah ku daina kuka."

Ta karasa maganar tana lallashin Najwa sai da ta dan tsagaita da kuka sannan  ta fara mata nasiha akan aure da zama da kishiya.

Ta ja hankalin ta sosai akan ta rike abokiyar zaman ta lafiya kuma sosai maganar Mamamma ta shige ta.

Mamama da kanta ta saka ta a mota dan kai ta gidan Baffah inda shima nasihar ce da jan hankali akan zaman aure tare da hakuri da juna.

Ummah kuwa cewa tayi ai ta gama da ita tin ba yau ba. Daga nan gidan su Mama aka kai ta daga can suka shige gidan Su Mamin Najib inda iyayen ta suma sukai mata nasiha da jan hankali.

Gaskiya inda Nasiha na fitowa a jiki da tini ta fito a jikin Najwa dan jama"a da yawa sun mata kuma duk ta dauka ba ta wacce ta yada.

Daga nan suka shige filin jirgi, da Mama Bilki da Maman Zahra kanwar Mami da Kawayen Najwa Zahra da Khadija da mutun biyar yan  ckul din su sai Salim da Basma da wasu yan uwan su, su goma haka suka tafi.

Suna zuwa aka turo motocin da zasu dauki Amarya. Gidan Mami aka shige da Najwa inda suna zuwa, Mami da kanta taje ta kamo yar ta.

Daki aka basu a sama ita da kawayen ta. Aka tarbe su da duk abinda suke bukata. sai da akai sallah sannan suka sakko da Najwa dan kaita wajen Mami.

Mami nasihar tai mata inda Baba ma ta mata ta ta.  Sama suka koma inda Mami ta ce bayan magariba zasu je reception dan haka za'a aiko da me shirya ta.

Najib kuwa ana can an shiga busy ga amarya an kawo ta yau gashi yaune tashin su.

Yanzu haka sabon gidan da ya kera shi yaje yana ganin yadda aka shiryawa Sumaiyya bangaren ta. Da mn komai shi ya sake mata.

Katon gida ne gari guda. Me ginin zamani, Bangare biyu ne a cikin gidan daya na facing din daya.




*Indabawa*

NAJWA Complete ✔Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang