130

627 60 0
                                    

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*

*AMEEN*

PAGE
*130*

*Hadiza Saban tnc for love. Nima ina son ki. Allah bar zumunci da kauna. Ameen.*

Really appreciate wit ur care.


Zama yayi a gefen ta, yana kallon ta,
"Shine kika kashe da ki bani mu gaisa."

"Kai Hamma."
Tayi kasa da kai.

"A ina yake ne?"
"A Abuja."

"Wane aikin yake?"
ya kuma tambayar ta.
"Likiti ne?"

"Yaushe kuka hadu?"
Kallon sa tayi,

"Eh! Mana ni dana yi budurwa ke nake fadawa kuma komai sai na fada miki. Kinga kuwa ke tinda baza ki fada min ba sai nai ta tambaya ko?"

Murmushi tayi, ta ce,
"Hamma ka bari ai zaka san shi ne?"

Murmushi yayi, ya ce,
"To shikenan! Dady ya ce, ki  bada Number Dadyn Abuja, da Number wayar sa."

"To nagode!"
Dariya yayi, ya ce,
"Sai da safe to."

Ya fita. wayar ta kashe dan kada Najib ya kirata. Dan kunyar sa ma take ji.

Najib tin kafin ya dawo ya sanar da Dadyn sa komai, ya fada masa gobe da safe zai turo Number dan ya fadawa Dadyn Kano ya sani.

Dariya Dady kawai yayi, ya ce,
"Sai ya turo."



Washe gari da safe ta tura masa, be duba ba kawai shima ya tura mata.

Dady na ganin sakon da daya turo yayi dariya, ya cewa Mami.
"Wallahi Najib ya mai dani kakan sa dai."

"Me yayi?"
"Wai ya ce, zai turon Number da Address din gidan yarinyar da zai aura shine ya turo number ta da address din gidan nan."

Dariya Mami tayi dan indai Najib ne haka yake shi kowa ma kakan sa ne.

Wannan tafiyar ma kaya sosai ya jidowa Najwa banda na lefe da ya kara hadowa.

Allah Allah yake ya dawo yaji labari a wajen Dady game da gidan su Najwa.

Sumaiyya likafa tacigaba dan kawayen ta sai suyi kwananki a gidan ta bama da Najib baya nan.

Yanzu a kalla ta zubar da ciki yafi biyar tin Najib na damuwa da rashin haihuwar har ya fauwalawa Allah.

Dan yasan ana samun irin haka.

Gashi 'dan Khaleel Najiib har ya shekara biyu da wattanni.

Yaro ne kyakyawa dashi, ga kuzari.

Zaman Khaleel da matar sa zama ne me tsafta.

Dan Khadija akwai iya girki ga tsafta ga ladabi da biyayya.

Sunje Abuja dan su hada su kawance da Summaiyya amman sam sai wani shan kamshi take.

Wannan yasa Khadijan itama ta janye jikin ta.

Duk abokan Najib nason su hada matan su da matar sa amman Sumaiyya bata bada fuska.

Wannan yasa duk suma suke janye jikin su sai dai suyi zumunci da Najib din kawai.

NAJWA Complete ✔Onde histórias criam vida. Descubra agora