111

627 52 0
                                    

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHODA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE 111

Dai dai lokacin da su *Najwa* suka gama biyan kudin su kenan. suka fito rike da ledojin su,.

Karba drivern yayi ya saka musu a mota sanna suka shiga ciki. Kamar ance yayi gate din fita ya nufi can yana amsa waya.

Lokaccin *Najwa* ta dago tana murmushi tana kallon hanya. motar ya tsaya kallo se kace wanda aka ce, ga yarinyar aciki ya hange ta, tana ta zuba murmushi.

Sandarewa yayi a wajen, ya rasa me zeyi. Sai daga baya ya nufi motar sa da sauri, ya bi bayan su.

Amman ina yana fita yaneme su rasa. Kai ya dukar kasa. Hawaye na zubar masa a idon sa.

"To wai ma me ya hanashi tsaida motar har ta tafi."

Ya jima a wajen dan anna yayi sallar magariba ya nufi gida duk jikin sa a sanyaye.

Su Najwa na zuwa gida suka zube kayan da suka yi. Kayan zakin ta ta kwashe zuba a firjin dakin ta.

Wacce Mami.

Mami suna ta na gaskiya Maryam, 'ya ga Maalm Isah da matar sa Hafsat.

Malam Isah babbsn malami ne dan garin maidiguri kasuwan ci ne ya kawo su kano har ya zama kamar dan garin.

'Yayan sa hudu suka haifa. Ado shine babba, yana da ya'ya shida, Amina itace babba wacce take da ya'ya uku, Summaiyya itace babba sai, Khaleel da kanwar ta Nusaiba.
Sai, Maryam, da Aminu, Huwaila, da  isah. duk sunyi aure kuma kowa yana da rufin asiri.
yana aiki a ma'aikatar tafiya.

Sai Ahmad wanda yake da ya'ya biyar, kamfani yake, dashi. Marzuk, Adnan, Shuaib, Sani, Halifa.

Sai Mami wacce ya'yan ta, Uku. Salim, *Najwa* Basma.

Sai Hauwa, wacce ke da ya'ya biyar, tana aure a katsina. Zahra itace babba sa'ar *Najwa* sai, Jabir, Hamza, Haidar, Abbasa sai auta Khairat.

Mami ta tashi cikin tarbiyya da kula. Ta samu ilimi na addini da boko.

Yanzu haka Anty Hauwa, ta nemi Dadyn *Najwa* da ya bata *Najwa* tayi karatu acan.

Dady ya amince dan duk sun zama daya.

Summaiya (Summy) ta kasance jika wajen Mami. Dan Baban Maman, Summy shine babba wan su Mami.

Suna da zumunci sai Summy da bata kaunar yan uwan ta, sam bata son zumunci bari *Najwa* da sam jinin su be hadu ba.

Dan ko magana bata yiwa *Najwa* Duk yadda Maman ta ke mata fada sam bata dauka.

In taga *Najwa* kamar taga mutuwar ta ne, ko dan taga kowa nason tane, kuma tana da ilimi da farin jini.

*Najwa* yar gata ce, daga dangin Mami har na Dady kowa son ta yake, dan akwai ta da hakuri da hankali da nutsuwa.

Kakannin ta na son ta, itama tana son yan uwan ta.

Sai dai bata fiya shiga yan uwa ba saboda harkar makaranta, sam *Najwa* bata son fashin makaranta. Kullun tana makaranta.

Kowa son ta yake da alfahari da samun ta a matsayin 'ya ko jika. *Najwa* bata da son hayaniya akwai ta da hakuri da riko da addini.

Miskila ce, dan sai ta yini a gidan bata ce komai ba.

*Najwa* fara ce, doguwa, bata da kiba, tana da idanu tana da dogon hanci, bakin ta karami.

Kanta gashi ne, mai tsayi da yawa, sai gefen fuskar ta da ya lulube da gashi a kwance.

Daka ganta, kasan bafulatana ce usuli.

Sai isha'i ya shiga gida. Yana zuwa gida ya kwanta akan kujera dake falon.

Ido ya lumshe, yana tunanin abin da ya faru na rashin samun damar ganin ta. Gashi jibi yake son su tafi saboda yana son da sun koma zai yi tafiya

Ya jima kwance akan kujerar Mami ta sauko kasa.

Kallon sa ta tsaya yi, sannan ta samu gefen sa ta zauna.

Kansa ta shafa, ta ce,
"Najib lafiya?"

Ido ya bude wanda suke jajir dasu, murmushi ya dan kwakwalo, ya ce,
"Mami yau ma na ganta, amman ban samu damar mata magana ba."

Kallon sa tayi, ta ce,
"Garin yaya?"

"Mami kafin na karasa har sun bace min."

Kai Mami ta girgiza ta ce,
"Haba Najib kabi komai a hankali, insha Allahu koman daren dadewa zaka hadh da yarinyar kuma rabon ka ce insha Allah. Ji yadda ka koma duk ka rame, kana son hankali na yana tashi ne. In naganka a haka."

Hawayen idon sa ya goge ya rumgume Mami, ya ce,
"Mami kiyi hakuri, nima ban son damuwar nan da nake ciki. Insha Allahu bazan kuma saka damuwar ba. Ki cigaba da yin addu'a."

"Toh Najib, Allah ya kawo maka dauki. Tashi kaje kaci abinci. Gobe zamu jewa su Umma sallama."

"Toh Mami!"
ya fada Yana mikewa.

Sallamar Khaleel ita ta tsayar dashi. Kallon sa yayi, ya ce,
"Sannu da zuwa."

Ya fada yana yin saman bene da gudu. Yana dariya

Murmushi Mami tayi ta ce,
"Ya maka laifi kenan."

Dariya Khaleel yayi, ya ce,
"Mami kenan ni da Najib sai Allah."

"Shiyasa nake sa muku ido ai."
Dariya yayi, sannan suka gaisa.

Sama ya nufa.

Najib na hawa sama ya cire kayan sa ya shige ban daki.

Khaleel na shiga ya samu waje ya zauna, laptop din sa ya janyo ya fara danne danne.

Yana zaune Najib ya fito rike da tawul yana goge jikinsa.

Kallon sa Khaleel yayi, ya dauke kai ya cigaba da danne danne sa.

Gefen sa Najib ya zaune, ya ce,
"Haba Bro menene?"

Kai ya dauke, ya cigaba da danne, dannen sa.

Hannun sa ya riko ya ce,
"Wallahi bana son fushi nana naka."

"A hakan ne baka son fushi na. Bayan kai kasa nake yi. Yarinya na je na gama shawo kan ta da kyar amman na baka number ta ko kira ba kayi ba, gashi jibi zaku tafi ko son zuwa kayi baka yi."
Khaleel ya fada cikin fada da bacin rai.

Tin da ya fara maganar Najib yayi kasa da kansa. Shima yasan be kyau ta ba, amman ya zai yi, ya kasa saka yarinyar aran sa ne, duk da ko hoto ta da ya bashi be kalla ba.

Kai ya dago ya kalli! Fuskar sa da alamar ban hakuri.
"Dan Allah kayi hakuri ban 'ki kira dan na bata maka rai ba, kawai na kasa sakin jiki da ita ne, amman insha Allahu zan kira ta, sannan gobe zan samu lokaci sai muje."

"Kaje dai!"
Khaleel ya fada yana dauke kai daga kallon abokin nasa, dan yasan da wuya ya iya sakin jiki kamar yadda yake son yayi.

"Ina kara baka hakuri dan uwa, kasan bazan iya va ni kadai. Ka taimakan nasan kai me sona ne da har kake son cire ni daga cikin damuwa."
Najib ya fada yana kama hannun sa.

Damke hannun sa Khaleel yayi, ya ce,
"To shikenan amman dan Allah kana kula da ita."

"Insha Allahu. Nagode!"
"Mene na godiya mun zama daya fa."

Ido daya ya kanne ya dage gira. Jallabiya ya saka sannan ya feshe jikin sa da kamshi.

Kallon Khalleel yayi, ya ce,
"Tashi muje muci abinci."

Mikewa Khaleel yayi, yayi gaba Najib yabi bayan sa.

*INDABAWA*

NAJWA Complete ✔Donde viven las historias. Descúbrelo ahora