117

579 58 0
                                    

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE *117*

Summy bata tashi ba sai la'asar alwala tayi, tayi sallah azahar da la'asar, falo ta fito.

Ganin dakin tayi tsaf da shi ga kamshi dake tashi.

Murmushi tayi ta kare masa kallo, daining ta nufa inda taga an jere kulolon abinci.

Can ta nufa ta zauna ta ci ta koshi sannan ta mike tayi falon babbn falo.

Ba ta dauke kayan da taci abinci ba.
Kallon mamaki nake mata dan ban taba ganin amarya haka ba.

Ace ki tashi daga bacci baki gyara wajen da kika kwanta ba bare sake wanka ki fito haka.

Sannan kizo kici abinci, ki tashi kibar wajen ba gyara.

Wani kamshi taji yana tashi na daban falon tayi ta zauna tana yin kallo.

Motsi take jiyowa a kitchen tare  da kamshi girki.

Mikewa tayi ta nufi kitchen din. Yan mata ta gani suna girki kallon su ta tsaya yi.

Su kuwa da suna can aiki kuma ba sallama tayi ba yasa bama su san da zuwan ta ba.

Aikin su suke suna hira abin sha'awa dasu.

Bara'atu ce ta juyo, Kallon Summy tayi, ta ce,
"Ina yini Antyn mu?"

Baki ta ya mutsa ta ce,
"Lafiya!"

Ta juya zata fita. Kallon ta talle tayi ita ma ta tabe baki ta saki tsaki.

Juyowa Summy tayi ta kalle ta, kallon ta itama tayi ido cikin ido ta tsame hannun ta daga aikin da take.

"Bara'atu in kingama ki fito mu tafi ina waje."
Talle ta fada mata.

Kallon ta Bara'atu tayi, ta ce,
"Bafa mu gama ba."

Ko kallon ta batayi ba, tayi hanyar waje tana tambayar ta ina wayar ta.

"Tana falo akan kujera."
Ta fada mata.
Summy wacce ta sandare a gun ta bita da kallo har tazo daidai in da take.

Wani kamshi taji tana fitar wa kamshin turaren da Najib ya aika mata dashi.

Falo tayi ta zauna ta dauki wayar ta. Missed call din Najib ta gani.

Ido ta bude, ta fara kiran sa.
"Ya Najib!"

Ta fada, Summy kallon ta, ta tsaya yi, bata ji me ya fada ba amman sai taga ta saka dariya ta ce,

"Muna kitchen muna muku girki, dan yaya yaci abincin da yawa ne."

Shiru tayi, ta ce,
"Toh mu dai muna gamawa zamu tafi, munyi missing Mamin mu."

Shiru ta kuma yi, sannan ta ce,
"To Yayan mu sai anjima."

Ta katse wayar. Bara'atu ta kwallawa kira.

Amsawa tayi ta ce,
"Ki sauri ki gama muje gida Mami na jiran mu."

Summy kuwa kallon talle ta cigaba dayi na yadda taga suna waya da Najib suna wasa da dariya.

Abinda basu taba yi ba. Zama tayi a gefen tana kallon TV.

NAJWA Complete ✔Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz