137

1.5K 54 0
                                    

*NAJWA*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya online writers*
*Allah kara hada kanmu. Allah kara mana hakuri da juriya*

*Ameen*

Dedicated *Rashida Abdullahi Kardam*
*Aunty Rash*

*Really love's u. May Allah bless you.*
*Ameen*🙏🏻😘😍

Page
*137*
*Anty Bilkisu Yakub. Marubuciyar Sarah ko Aidah.*
*Ummu Mohammad*

*Allah ya raya mana Muhammad ya bar mu tare. Ameen.*
Nagode sosai.

Sai magariba yaje gida, yar mulkin na zaune a falo tana cin fruit.

Ko kallon sa batayi murnushi yayi, ya karasa kusa da ita.

Kai ta  dauke, kallon ta yayi ya saki murmushi.
"Uwar gida sarautar mata, ya kike na same ku lafiya."

Banza tayi dashi, murmushi yayi ya tashi ya bar dakin.

Ita fushin da biyu ya dadu, ga aure da zai yi. Gashi wannan tafiyar baya kiran ta kamar yadda ya saba.

A da zai kirata da safe da rana da dare, amman wannan karan in ya kira da safe shikenan.

Kallo tabishi dashi. Ya kara kyau da gogewa.

Najib abin burgewa ne, sannan abin so ga kowa. Ba karamin kewar sa take ba. Gashi kuma taga alamar yau shima bazai dau raini ba.

Tsaki tayi ta mike tayi cikin daki.

Ji tayi bazata iya jurewa ba dan ganin san da tayi ba karamin kara tada mata da hankali yayi ba.

A daki ma juyi kawai take dan marar ta ba karamin daurewa tayi ba.

Da kyar tta samu bacci ya dauke ta. Da asubar fari ta kuma tashi da wata matasananciyar sha'awa.

Har ta nufi bangaren Najib kuma ta tuna da shawarar kawayen ta da suke bata.

Akan bin sa da take yi.
Tsaki tayi ta juyo ta dawo, daki ta koma.

Wayar ta, ta dauka ta kira kawar ta Bebilo, dake ita a Abuja take.

Bebilo cikakkiyar yar lesbian ce, dauka tayi, tana tambayar ta lafiya.

Kuka ta fashe mata dashi, tana fadin,
"Bebilo Najib wani sabon iskanci ya shigon dashi, wai ya dawo amman ko ya neman."

Tsaki Bebilo tayi, ta ce,
"To shine me?"

"Haba Bebilo, kinsan kwanan sa goma sha uku ai dole nayi kewar sa."

Wani tsakin ta kuma ja, ta ce,
"Shiyasa nifa na ce bazan yi aure ba ko rayuwa da mazan nan. Sun fiya gadara ko dan sun ga anan son su ne oho. Malama ki bar wannan mijin naki kizo ayi harka, Allah kika hadu da manyan mata sai kin raina ko wane na miji."

"A'ah Babilo, ki daina fadin haka ni bazan iya ba. Yanzu ya zanyi."

Tsaki taja ta kashe wayar ta.  Wayar Sumny ta tsaya kallo, kiran ta ta kyma yi.

"Haba Bebilo, ki ban shawara man."

"Shawara daya ce, ki ajiye Najib a gefe kizo mu shiga harka."

Shiru Summy tayi, tana nazarin abin da Bebilo ta fada mata.

"Kinga mayi magana anjima kije kiyi tunani."
Ta kashe wayar.

Kan gado ta fada, tana juyi, aranta kuma tana cewa baza ta tsaya Najib yai mata illa ba.

A ranta take magana
"Haka kawai, gashi da jaraba sai yaje ya tsufar dani, gashi zai yo aure ya samin hawan jini dan kishi. To bazan iya ba gara na san nayi. Dan ma yaga ina biye masa ne."

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now