136

585 56 0
                                    

*NAJWA*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya online writers*
*Allah kara hada kanmu. Allah kara mana hakuri da juriya*

*Ameen*

Dedicated *Rashida Abdullahi Kardam*
*Aunty Rash*

*Really love's u. May Allah bless you.*
*Ameen*🙏🏻😘😍

Page
*136*

*Barrister Halima. Kawata yar uwa. Ina matukar kaunar ki. Nagode sosai da kwarin gwiwar da kike dada bani. Addu'a da kulawa. Nagode sosai. Allah ya bar mu tare ya hadamu a Aljanna.*
*Ameen*

*Really love u*




Kallon ta ya tsaya yi hannun sa harde a kirjin sa.

Kanta ta dauke ta cigaba da aikin da takeyi. Gefen ta ya karasa, yana kallon ta.

"Najwa!"
Ya kira sunan ta.

"Na'am!"
"Najwa lafiya kuwa?"

Shiru tayi, kallon ta yake yi yana jin son ta na daduwa a cikin zuciyar sa.

"Baby ki juyo ki kallen man."
"Hamma ka bari dan Allah baka ga aiki nake yi ba."

Murmushi yayi, ya ce,
"Kawo na taya ki."

Ido tayo waje dasu ta ce,
"Ka iya ne?"

Dariya yayi, ya ce,
"Dai dai kun abubuwa ne ban iya girkawa ba."

Kai kawai ta jinjina. Ta dauko fulas ta juye a ciki.

A babban faranti ta zuba masa duk abinda zai bukata, yana tsaye yana kallon ta.

Komai takeyi cikin nutsuwa da tsabta. Juyowa tayi ta fuskance shi, amman kanta a kasa, ta ce,

"Muje ka karya."
ta juya tayi gaba.

Bayan ta yabi, har suka karasa karamin falo.

Sai da ta zuba masa komai sannan ta mike zata fita.
"Najwa!"

"Na'am!"
Ta fada tana juyowa.

"Zo nan ki zauna."
Ya nuna mata gefen ta.

Komawa tayi ta zauna, Tura mata kayan da ta hada masa yayi.

Idon ta, ta dago tana kallon sa. Kallon ta yayi, idon ta sun kumbura sunyi ja.

Ba komai yake gani ba sai sonsa da kishin sa.

"Baby na me ya same ki."
"Ba komai. Dan Allah kaci abinci tukunna."

"Baby na ke kin karya ne."
"Eh naci."

"Baby na da gaske."
"Eh na sha tea."

"Tea kadai?"
Kai ta girgiza, ta ce,
"A'ah da cake."

Shiru kawai yayi, yana kallon ta. Tura masa kayan tayi, ta ce,
"Dan Allah kaci kar yunwa ta maka illa."

Ja yai gaban sa, yana ci yana kallon ta har ya koshi.

Kallon ta ya cigaba dayi ita kuma tana can duniyar tunani.

"Najwa! Najwa! Najwa!!"
Sai da ya kira sunan ta sau uku sannan ta dago.

Kallon sa tayi, ta amsa da
"Na'am!"
Ido ya tsare ta dashi yana kallon ta.

Kasa tayi da kai,
"Najwa dan Allah ki fadan damuwar ki."

Murmushi tayi, ta ce,
"Hamma wallahi, ba komai."

"Kince wallahi fa."
"Eh!"

"To shikenan dan Allah ki daina tunanin kinji."
"To!"

"Amma fa zan ta damuna na rashin sanin abinda ke damun ki."

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now