140

717 49 0
                                    

*NAJWA*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online WRITERS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH DAUKAKAKI YASA KI GAMA DA DUNIYA LAFIYA.*

*REALLY LOVE U ANTY NA*

*THANKS FOR UR LOVE ND SUPPORTING*

*PAGE*
*140*

*Anty Alawiyya*
Allah ya kara miki lafiya. Yasa ki gama da dubiya lafiya. Allah ya raya Ya'yan mu Ameen.

*Ina kaunar ki irin da yawan nan*


Kallonta Mami tayi, ta ce,
"Najwa ba ma wannan ba. Ni kaina sai yau da aka kai lefe naji. Shima dan xaku hada miji da sumaiyya ne."

Ido Najwa ta kuma zarowa tace,
"Mami wacce Sumaiyya?"

"Sumaiyya jikata."
Kai Najwa ta jinjina tana zama a gefen gado.

Kallon ta Mami tayi, ta ce,
"Kada kisa damuwa kinji."

Kai kadai Najwa ta gyada mata.
Fita tayi, a ranta tana cewa baza ta taba raba wanna hadin ba.

Najwa kuwa ta ma rasa tunanin da zatayi. Kuka kawai ta fashe dashi.

Ta jima tana kuka, dan bataaan sanda bacci ya dauke ta ba.

Sai wajen karfe uku ta farka, missed call din Najib ta gani guda 10."

Zama tayi ta rasa tunanin da zatayi ma. Kanta gaba daya ya kulle.

Ga ciwon kai dake damun ta.

Alwala ta mike tayi,
Sallah tayi, har bayab asuba taa kan sallaya.

Anan bacci ya dauke ta inda bata farka ba sai karfe sha biyun rana.

Wanka tayi, tai wanka, ko mai bata shafa ba dan bata jin daxin jikin ta ga wani nauyi da kirjin ta yayi.

Idon ta ya kumbura yayi jajir dashi.

Ita a zahirin gaskiya bama tasan me yake damun ta ba kuma bata san me zata yi ba.

Tana zaune Mami ta shigo dakin.

Daga kallo daya ta gane Najwa na cikin damuwa.

Gefen ta, ta zauna, ta kalle ta.

Zamewa tayi daga kan gadon da take zaune, ta ce,
"Mami ina kwana?"

"Lafiya lou Najwa. Kin tashi?"
"Eh!"

Ta amsa mata kan ta a kasa.
"Najwa kinsa abin a ranki ko? Bana son ganin damuwar ki. Tinda ba haramun bane ai sai mu godewa Allah ko? Su Mama ma duk sun sa albarka da sun ji dadin hadin nan."

Shiru Najwa tayi, hannun ta mami ta kamo taji shi zafi rau.

Kallon tayi, tace,
"Najwa kefa baki iya sa abu a ranki ba. Mene na sa damuwar."

Kuka ta fashe mata, ta fada jikin ta. Rarrashin ta take yi.

Har tayi shiru, mikewa Mami tayi, ta fita abin kari ta hado mata, da magani a gefe.

Dakin ta shiga ta hada mata tea me kauri sai dankali da ta zuba mata,

A baki ta dinga bata abincin har sai da taga ta koshi.

Sannan ta bata magani, ta kwantar da ita a kan gado.

"Kiyi bacci ki cire damuwa kinji."
"To Mami."

Ta juya ta fita, Wayar ta, ta zaro, wasu missed din nashi ta kara gani.

Ido ta lumshe aranta tana tunanin Najib. Tin farko shiyasa taki fara soyayya dan ita bata iya son abu ba.

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now