46-50

844 73 0
                                    

*NAJWA*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya Online writers*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
AUNTY RASH

LOVE SO MUCH



PAGE *46-50*



Tun da suka shigo Kano, kullun sai sun fita, bayan gidan Su Mami da sukaje, sunje gidan Uncle Marzuk dake Naibawa, Uncle Adana dake, Zoo road, sai Uncle Usman dake nan Court Road.

Gidah Uncle, Ahmad ne kadai basuje ba, saboda basa kasar sunje Umrah. Amman a cikin satin zai dawo.

Hajiya Maryam kawar Hajiya Aisha ce tare sukayi makaranta tin daga firamare har sakandare, haka jami'a ma tare sukayi karatu.

Sai gashi Allah ya hada su auren zuri'a daya wannan ya kara saka zumuncin su daurewa, dan Najib kamar dan Hajiya Maryam ne (Mamin Najwa)

Ita ta yaye sa, kuma da ya samu hutu gun ta yake zuwa sai da ya tafi waje karatu sannan ne ya rage zuwa gun ta.

Amman Najib dan Gidan Mamin Najwa ne.

Yau dake ba inda zasu, suna zaune a babban falon su.

Sanye yake, da wando wanda da kadan ya wuce gwiwar sa, sai riga wacce take kamar ves duk hannayen sa a bude suke.

Kansa akan cinyar Mami! suna hira. Mami ta ce,
"Son kaje gun Khaleel kuwa?"

Najib ya gyara kwanciyar sa, ya ce,
"Yau nake son zuwa, so nake nai masa zuwan bazata tinda sai baya yin zumunci."

"A'ah fah! Kasan kuwa Khaleel akwai zumunci yanzu ma nasan aiki ne."
"Mami ai dama ke, haka zaki ce."

"Ba hakan bane?"
Shiru yayi,

Mami ta ce,
"Yauwah Yaro, yau Hajiya Ikilima zata turo yar ta, Rumanat."

Murmushi yayi, ya ce,
"Toh Mami mene, na fada min."

"Kasan ai abinda nake nufi."
"A'ah! A'ah! Mami ni bansan komai ba."

"Zaka sani ne, in har nai maka auren."

Dariya yayi, yace,
"Haba Mami, dan Allah kada kimin haka."

"Allah *Najib* in har na gaji to zan aura maka ko ma wacece kasan daman Nabila, Rahmatu da Rumanat duk son ka suke ko?"
"Nasani Mami!"

"To ka zabi daya a ciki dan baza ka hadani da kawaye na ba."
"Mami kenan! Kinsan dai irin matar da nake son Aure, kuma kinsan fa'idar auren mace ta gari."

Karar shigowar mota suka jiyo, lekawa yayi ta taga.

Wata hadadiyar mota ce ta shigo cikin gidan. Motar kadai abar kalla ce.

Labulen tagar ya saka, ya koma kan cinyar Mamin Sa ya kwanta.

Ido ya lumshe, yana me tunanin samun cikar burin sa.

Dakin aka budo aka shigo, wata kyakyawar yarinya ce, fara doguwa wacce ta cika mace, duk abinda ake nema ga 'ya mace tana dashi.

Sanye take da wasu damamun riga da siket na atamfa, daga gani Super ce, amman an yagalgala ta da wani dan iskan dinki.

Wanda fin rabin bayan ta a waje yake, hannun ma an kwakwashe shi, haka gaban rigar ma an yashe shi duk kirjin ta na waje.

Sikket din kuwa kamar in tayi taku zai yage ne, sai wani takalmi me tsinni sosai.

Kanta ya sha gashin doki (attachment) an mata kitso ya zubo ta gefen wuyan ta har kasan kirjin ta.

Fuskar ta tasha kwalliya, an xuba foundation dasu ja gira da uban jan baki.

Hannun yasha kari na farce ta saka musu (nailpain) haka ma kafar ta. Bakin ta sai taunar cingam take kas kas sai kace wata karuwa.

Ba sallama ta shigo dakin. tana tafiya kamar kugunta zai karye, Wajen Mami ta karasa, ta zauna a kujerar kusa da ita.

Ta kasan idon sa yake kallon ta.
A ransa, yana tir da ita da iyayen ta da suka barta ta fito a haka.

Wai kuma har tazo gidan wanda take so a haka, zuciyar sa tayi baki na tuna wai dashi take son suyi aure.

Ido ya kara rufewa yana addu'a cikin ransa, dan shi sam Rumanat ba tayi masa ba, zubin ta kaf na karuwai ne.

Cinkun yanga da iyayi, ta ce,
"Mami ina yini?"

ta fada tana daga kan kujerar da ta zauna.

Murmushi Mami tayi, ta ce,
"Lafiya lou. Yasu Maman taki."

Ta dan ya mutsa fuska ta ce,
"Suna lafiya. Mami Ya Najib din bacci yake ne?"

Kallon sa Mami tayi, ta girgiza kai. Mikewa Rumanat tayi, ta karaso kusa da inda ya daura kai a kafar Mami.

Kansa ta daura akan kujera, ta mike tayi bangaren masu aiki.

Laure ta aika ta kai mata abin motsa baki.

Bayan gidan su. Tayi can wajen shakatawa.

Kallon sa ta tsaya yi, kafin daga bisani ta dauki hannun ta, ta daura a cikin sumar sa.

Idon sa ya bude a zabure, ta ce,
"Oh ashe Sweety na ba bacci yake ba."

Wani kallo ya watsa mata na tsana da kyama.

Ido ta kashe ta matsa kusa dashi tana daga hannun ta da nufin shafar fuskar sa.

Hannun ta ture sannan ya mike zaune.

Fuska ta shagawabe,
"Haba Honey wai kai bakayi missing (kewata) dinna bane, haba na kashe abubuwa dan nazo na ganka tinda kai baka zo ba amman kuma kana min haka."

Ido ya bita dashi, kara narkewa tayi ta mike ta nufi cinyar sa da niyar zama.

Gane abinda zatayi, yasa cikin zafin nama, ya mike.

Idon sa jajir dasu, dan ransa yayi mugun baci. Ya ce,
"Look (kalli) Rumanat! Bana son shashancin banza, ke ko kunya bakya ji ne wai."

"Kunya kuma?"
"Eh! Ita,"

Ya fada cikin tsawa, sannan yaciga da magana cikin bacin rai.

"Abu na farko, dan Allah kalle ki, kina diyar hausawa kuma musulma kika fito a haka, ke a tunanin ki kin burge ko. Kin fito da tsirai cin ki ko kunya bakya ji wani yaga abinda be dace ya gani ba ko?"

"Secondly (na biyu) kin shigo ko sallama, ke kinsan ma'anar sallamar ma kuwa, da har bakya neman wa mutane amincin daga wajen Allah, bare kema a samu a nema miki ko ke samu."

"Na uku! Dan Allah ko kunyar, taba ni da son kusanta ta bakya ji.
Haba Rumanat, ki dawo cikin hayyacin ki da nutsuwar ki mana, kinsan duk abin nan da kike yi babu kyau, ki tuba ki koma ga Allah."

"Haba sweet nazo ba maganar soyaya sai zancen banza."

Ido ya ware cikin mamaki, yana mata maganar gyara tana cewa maganar banza.

Tab lallai Rumanat tayi nisa. Fuska ya bata, ya ce,
"Dawa zakiyi zancen soyayyar, ina kawo miki abinda zai sa ki rabauta amman kina cewa zancen banza ko?."


*Muje Zuwa*

*INDABAWA*

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now