156

756 60 0
                                    

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*156*

*Fee feey kina ina ne, ina cigiyar ki kwana dayawa. Allah yasa lafiya*

*Allah ya dafa*
*Ameen*


Kwanci tashi ba wuya. Rayuwa sai tafiya take yanzu sati biyu kenan da tarewar Najwa da Najib. Jin dadin rayuwar aure ba wanda zai nuna musu ita.

Dan yadda yake gatan ta, da kula da ita ba kowa ke samum irin wannan ba.

Gaskiya Najib ba karamin sangarta Najwa yayi ba, dan ita kanta tasan yana son ta.

Kyau kuwa ta kara shi banda haske da kara murjewa da tayi.

Duk inda ta juya sai yabita da kallo ba karamin birkita masa tunani take ba.

Da in Najib zai kusanci Sumaiyya sai ta ga dama amman yanzu, ya samu gwarzuwar mace zakwakura wacce ko zai neme ta sau goma ne bata nuna gajiyawar ta. Ga juriya ga ni'ima.

Kallon da take masa ma na daban ne, wanda yake kara masa son ta da sha'awar ta.

Ita da kanta in ta gane yanayin sa, ita ke dada masa kwarin gwiwa ta kara janyo masa da sha'awar sa na dabaru daban daban.

Satin su biyu da tarewa amman kowa ga gansu sai yaga canjawar da sukai, ya yi yar kiba ya murne ya kara haske da kyau.

Abincine kullum akan kari ga kula ga tattali. Shi dai babu abinda Najwa zata nema be bata ba.

Kullun sai ta kira Mami sun gaisa haka su Talle suyi ta wasa da dariya abin su. Dan sun zama kamar Yaya da kanne.

Yau tin safe da ya fita be dawo ba har karfe daya.

Tana kitchen tana tunanin me zata dafa ya kira ta a waya, dauka tayi cikin zumudi dan ba karamin kewar sa tayi ba.

"Baby nah!"
"Na'am Honey, ya aikin yau kayi nisan kiwo ina fatan kana lafiya dai ko?"

"Ina lafiya. Yanzu naga missed dinki, mun shiga aiki ne. Amman Alhamdulilah mun fito lafiya."

"To Sannu, Allah kara taimakawa."
"Ameen!"

"Yanzu yaushe zaka dawo?"
ta fada a shagwabe.

Murmushi yayi, ya ce,
"Sai nan da karfe uku, dan wani aikin zamu kuma shiga. Ki kular min da kanki."
"Insha Allahu. Allah bada sa'a a dawo lafiya."

Ta kashe wayar. Shinkafa ta debo fara ta tuwo ta jikata.

Sannan ta bude firij din kayan miya ta dauko naman rago ta yanka ta wanke ta daura akan wuta bayan ta saka masa kayan kamshi.

Kayan miya ta dauko tai blending din su, sannan ta daura akan wuta.

Kaza ta dauko ta yanyanka ta, ta dauraye ta daura akan wuta ta zuba mata attaruhu da albasa me yawa sai kayan kamshi.

Shinkafarta ta wanke ta bawa me gyara musu flower ya markado mata.

Kafin ya dawo har ta soya kayan miyar ta, ta zuba agushi a ciki da kayan dandano. Naman da ta tafasa da kayan kamshi shi ta juye akan miyar ta.

NAJWA Complete ✔Donde viven las historias. Descúbrelo ahora