158

817 50 0
                                    

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*158*


*Makawa* marubuciyar *Furen Juji* jinjina gare ki, da fatan Alheri gareki Allah kara basira. Allah shige miki gaba.

*Ameen!"

Kallon ta yayi, ya ce,
"Wannan kayan fa?"

Murmushi tayi, ta ce,
"Nasu Mami ne."

Bai gane me take nufi ba, dan haka ya saka a mota kawai.

Ya bude mata gidan gaba sai da ta shiga sannan ya rufe ya koma dayan bangaren.

Suna tafiya suna hira, Najwa tace,
"Honey ina jin kunyar Mami wallahi, Allah yasa kar ta gane wani abu ya shiga tsakanin  mu, wallahi ba zan iya hada ido da Mami ba wani irin nauyin ta nake ji."

Murmushi Najib yayi, ya ce,
"To mu koma tinda kunyar ta kike ji."

Hannun sa ta kamo ta ce,
"Haba dai ai kuma ina son na ganta, kasan ita ce kamar Mami na a garin nan."

Murmushi yayi yana jin dadin inda Najwa ke son Mamin sa.

Shiru sukai, can ya kalli Najwa ya ce,
"Na fada miki yau Antyn ki zata dawo ko?"

Kallon sa tayi, ta ce,
"Eh Allah kawo su lafiya."

"Ameen! Kinga yau bangaren ta zan koma kenan."

A ranta tayi tsaki ta ce,
"Har wani zumudi ma kake."

Kan ta, ta dauke tana kallon waje! Duk maganar da yake jin sa kaawai take amman sam ba fahimta take ba.

Wani abu ne ya danne mata kirji, da tana tunanin bata da wannann zafafen kishin amman yanzu ta gane ba haka bane.

Ba dole ba, ta kishin wani ya samu soyayyar da take samu daga mijin ta.

Yanzu fa sai tayi kwana koma ta ce kwanaki bata ganshi ko jin dumin shi ba.

Cikin minti kadan duk mood dinta ya sauya, yana lura da halin da ta shiga, to amman me yafi ta shiga halin saboda sam baya son yin nesa da ita.

A haka suka karasa gidan Mami da saurin ta, ta fita tayi cikin gidan.

Mami na falo tana jin sallamar Najwa ta mike ta taro ta, Jikin Mami ta fada tana murnar ganin ta.

Suna daga tsayen yan aikin gidan suka fara shigo da kayan da tazo dashi.

Kallon su Mami ta tsaya yi ta ce,
"Kayan waye wannan?"

"Mami nice na kawo miki."
"Kai Najwa bakya gajiya ko?"

Kai Najwa tai kasa dashi, sai da suka gaisa, Mami take tambayar ta,
"Najwa ya kuke ince dai kuna zaune lafiya?"

Cikin nauyin da kunya ta ce,
"Lafiya lou ba komai Mami."

"A'ah fa in yana miki wani abun na fada miki ki sanar dani ko?"
"Mami ba abinda yake min sai kyautatawa."

"To masha Allah Najwa naji dadi abinda nake so kenan. Allah kara baku zaman lafiya da fahimtar juna. Allah tsare mun ku."

Najib da yake shigowa, ya ce,
"Ameen Mami,"

NAJWA Complete ✔Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu