41-45

896 72 0
                                    

*NAJWAH*

BY *MARYAM S INDABWA*
*MANS*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya Online writers*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

Dedicated to Rashida A Kardam
Aunty Rash

*41-45

Washe gari tin karfe sha daya suka nufi gidan su Mami dake tarauni.

Tin daga bakin gte masu aikin gidan ke musu sannu da zuwa tare da musu godiya.

Mami bata shiga bangaren Ummin ta ba sai da ta fara zuwa wajen masu aikin gidan.

Wajen Baba Uwani taje wacce ita ta raini Mami tin tana karama. Har tayi aure ita ce abokiyar shawarar ta

Najib na gaishe ta, ya juya yayi bangaren kakanin nasa.

Suna zaune a falon su, me kyau dashi ko ina a gyare sai tashin kamshi da sanyi AC ke tashi a dakin.

Ya shiga da Sallama. yana cewa,
"Mamah na da Abbah na."

Ya fada yana karaswa cikin dakin. Mamah da Abbah dariya suke.

"Sannun ku da karasowa,"
Abba ya fada.

"Yauwah Abbah. Ina yinin ku?"
Ya fada lokacin da ya durkusa.

Suka amsa da,
"Lafiya lou. Ya kuke kun zo lafiya ya aiki?"

"Duk lafiya Alahmdulilah."
"Masha Allah! Jiya ai sai ga kaya sunzo."
Mama ta fada

"Wallahi. Mamah."

Abbah ya ce,
"Toh madallah angode Allah kara arziki."

Najib ya ce,
"Kai Abbah ba komai. In bamuyi muku ba suwa zamuyiwa."

Abbah ya ce,
"Duk da haka ma angode Allah kara arziki."

Najib ya ce,
"Ameen!"

"Wai yaushe zaka kawon kishiya tane."
Mamah ta tambaya cikin tsokanar jika da kaka.

Murmushi yayi, yace,
"Mamah tukkuna dai, amman an kusa insha Allah!"

Mama ta ce,
"Toh Allah nuna mana."

"Ameen!'
Suka amsa gaba dayan su.

Hirar aikin sa suke da rayuwa. Wani lokacin ya tsokani Mamah ko Abbah.

Abin sha'awa dai Najib yake. Kowa son sa yake, tare da masa fatan alheri.

Najib irin yaran nan ne masu shiga rai, da son yan uwa dan duk karshen wata sai yayo musu da aike.

Mami ma bata sani sai dai a bugo ana mata godiya in ta tambaya ace Najib ne yayi kaza

Najib yazama abin alfahari ga yan uwan sa haka nan ga mahaifan sa.

Dan ba karamin dadi suke ji ba da irin abin alkhari da yake aikatawa.

Najib sam abin hannun sa be rufe masa ido ba. Hannun sa a bude yake, wajen taimakawa jama'a da inganta rayuwar marasa shi

Haka nan wajen kyautatawa yan uwan sa. Dan in azumi ne haka zai ta rabon kayan abinci da tufafi.

Duk da yasan yan uwan sa na da hali amman yana yi ne dan kyautatawa.

Haka gidajen marayu bai dauke musu ba duk wata akwai abinda yake cire musu a cikin albashin sa.

Wannan na dada daukaka shi da sanyawa kudaden sa albarka dan shi ba abinda yake da kudin sa sau taimako tunda a gida an dauke masa komai ci sha da sutura duk Dadyn sa ne ke yi masa.

Wannan yasa kome nasa shima yake karar wa wajen inganta rayuwar wasu.

Mami ta jima a bangaren Masu aiki sanna tayo wajen iyayen ta.

Sun gaisa sannan aka hau hirar yaushe gamo.

Sun jima tare ana ta raha da nishadi.

Mamah ganin Najib na nan da kanta ta shiga kitchen tayi masa dan wake tare da taimakon sa.

Dan tare suka dafa.

Ranar yaji dadin sa dan Mamah akwai iya girki.

Najib ya ce,
"Mamah amma Mami na hannun ki ta dauki wajen iya girki."

Dariya sukayi dukkan su.

Mamah ta ce,
"Najib kai dai akwai santi."

"Mamah da gaske ba zancen santi bane"
"Toh kaima Allah baka mace wacce ta iya girki."

Najib ya amsa da,
"Ameen Mamah, dan kuwa in bata iya girki ba ta fadi."

"Yo ai duk mace da bata iya girki ba, ta ragewa kanta daraja sosai."
"Wallahi Mamah abin na damuna ace wai mace bata iya girki ba. To me zata iya kuma."

"Lalaci ne wannan kuma ai."
"Wallahi Mamah ina son mece me Ilimi dukka biyun, hankali, nutsuwa, tarbiyya, tsabta. Iya girki. In Allah yaba mace me wadan nan abubuwan ba abinda zan rage ta dashi na kulawata wallahi."

"Toh Allah ya baka."
"Ameen Mamah."

Basu suka bar gidan basai karfe taran dare.

Bayan Najib yayiwa kakan nin nasa kyauta kamar yadda yayiwa mahaifan Dadyn sa.

Haka Baba Uwani ma ya bata.

Sun tafi ana ta sa musu albarka

*Waye Najib*

*Muhammad jauro,* ba fulatani usuli ne, da matar sa *Khadija* wanda suke mazauna garin rimin gado.

Allah ya musu arziki ta hanyar kiwo, inda Muhammad ya kasance, me kudi

Ya'yan sa biyu, *Amina da Tijjani.* Dukkan su ya sanya su a makaranta, inda Tijjani ya karanci bangaren lafiya. Ya zama baban likita.

Amina kuma ta karanci koyar wa, dan NCE tayi.

Ta aure abokin Tijjani ne, wanda bayan auren su suka koma Landon da zama saboda acan yake kara cigaban karatun sa.

*Tijjani,* kuma ya auri kanwar Suleiman, mijin Amina. Fatima inda suka zauna anan gidan shi dake sharada.

Ya'yan sa hudu, Marzuk shine babba wanda yanzu haka yake lawyer da matar sa daya da ya'ya hudu.

Sai Adana me binsa, ma'aikacin gidan TV ARTV ne da matar sa daya, ya'yan sa uku.

Sai Usman, dake aiki a banki, da matar sa daya da ya'ya uku shima.

Sai Abubakar dake Minister ne, matar sa daya Aisha, da 'dan sa daya *Najib.*

Yana zaune da matar sa a Abuja. Zuria'ar nan abar sha'awa da alfahari ce.

Sai *Amina* kanwar *Tijjani* da ta haifi ya'ya biyu.

Bilkisu ita ce babba, inda yanzu, take auren governor din Kaduna tana zaune a can Kaduna. Ya'yan ta hudu.

Sai Ahmad da yake baban likita, da matar sa daya Maryam da ya'ya uku. Salim shine baba sai *NAJWA* da autar su Basma.

Ahmad shine sa'an Abubakar kuma aminan juna dasu.

Zuri'a ce wacce suke son junan su da zama lafiya.

A ciki ba wanda zai ce ga ya'yan Tijjani ko Amina saboda hadin kansu da zaman lafiyar su.

*-*-*-*-*-*-*-*
Iyayen Mami kuma *Alhaji Mudammad* da mahaifiyar ta *Hajiya Rashida*

Ma'aikacin gwannati ne, kuma dan siyayya, dan yayi commissioners ma.

Abokin *Alhaji Tijjani ne,* ita kuma *Hajiya Rashida* kawar *Hajiya Amina* ce kanwar *Tijjani*

Haka nan Mami ita kadai ce wajen iyayen ta, dan sun haihu yaron ke mutuwa.

Aisha wato Mami kawai ta rayuwa, Dady yaga Aisha ya nuna son ta. Kuma iyayen ta suka aminta.

Suna Son Mami, wannan yasa son da suke ya koma kan danta.

Haka Su Ummah ma suna kaunar Mami da Najib da duk surukan su.

*INDABAWA*

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now