DAGA ALLAH NE! 01

3.6K 128 10
                                    

💖💖💖💖💖💖💖

💞💞💞
*DAGA ALLAH NE*
💞💞💞

*FATIMA ZOIS*

Dedicated to *MY PARENT*

*Bismillahir rahmanun raheem*

Page1⃣

Zaune suke a gaban doctor kowannensu fuskarsa babu walwala hade da tsantsar damuwa,

idan ka dauke kyakkyawa koma mafy kyau daga cikin kyawawa karamin yaro da yake ta wasansa a wajen cikin nishadi da annushuwa Wanda baxai wuce 7years ba,tamkar ba don shi aka zo wajen doctor dinba

"Likita ya kake ganin zaayi? kullum abin haidar gaba yake karawa ba baya ba! Magana daya ake fada a koda yaushe haidar lapiyarsa kalau alhalin ni banga alamar lapiyar ba! ynxu ina alamar lapiya take anan?"@mum

   "Doctor karka manta pah haidar da sunan *zahra* ya fara iya magana koma shine sunan da a kullum sai ya kira sau ba adadi,
Doctor haidar koni mahaifiyarsa da nike mafi kusanci dashi akan kowa bai kiran suna na kamar yanda yake kiran sunan zahra
Ga yayarsa nan yayi wasa da ita bai iyawa saidai kullum yace da zahra yake wasa alhalin bamu taba ganinta ba har shi dinmah..."

Haidar da yake wasansa kamar baima san don shi aka zo ba shine ya katseta cikin sauri ganin azo kan zahransa koma ace ko saninta bai taba yi,inah!

"mum wayye yace miki ban taba ganin zahra ba? Ai bamu Dade mah da gama wasa da ita ba yanxu koma nasan zata dawo."

"Oh my gosh! Doctor mai irin wannan maganganun shine zaace lapiyarsa klau,koma har ace yarinta ce abinda ba yau ya fara yi ba shekara da shekaru kenan."@mum

Doctor ne cikin kwantar da hankali yake fada mata "please hajara kiyi hakuri insha Allah komai zai dawo daidai kowanne yaro da kika gani da irin yarintarsa."

"Hajara kema doctor ce koma a gabanki muke bincike akan yaron nan amma Abu daya ne babu sauyi lapiyarsa kalau tun daga lokacin da yake watanni wato sanda ya fara maganah kike fada min nace miki may be yarinta nan zuwa shekara Biyar zai daina........"

"Doctor kana kallo har yaxo shekara bakwai amma babu abinda ya canja na game da xancen zahra, saima abinda yayi gaba." Cewar dad da sai yanxu yayi magana shima cike da damuwa wacca daga gani kawai dauriya ce irinta maza

"Na gaji da jin xancen yarinta haka ace Abu yaki ci yaki cinyewa,"

"A tunanina yarinta ana yinta ana mantawa ne,amma haidar babu alamar mantuwa dangane da wannan xancen zahra da yake yi,"

"Please mana doctor u are my last hope manyan manyan likitoci na duniya tare da manyan malaman addinin musulunci a zatonmu ko sharrin jinni ya sameshi,munje wajensu amma gaba dayansu maganah daya suka fada,"

"Doctor ina son kai ka canja daga maganar da sauran masana irinka suke fada don Allah da koma wannan da guda daya tal! Da muke dashi please doctor Kaine fatanmu." @hajara still tana maganar ne hade da kuka

Wannan karon kam saida dad ya lallasheta Wanda shima kawai karfin hali yake amma abun na haidar akwai sarkakiya

Haidar kam da yake wasa a wajen ko a jikinsa asalima wasansa yake still koma yana kiran zahra irin alama na ba shi kadai yake wasan ba

"Haidar wacce zahra koma a ina take?,idan ka fada min ga chocolate nan sai Wanda ka zaba." @doctor

"Doctor ni ba saika bani komai ba idai akan zahra ta ce, Doctor kasan wacce zahran haidar kowa?" @ haidar

Aah haidar saika fada....."@doctor

"Zahran haidar ita abokiyar haidar da kullum take xuwa min a mafarkina wani lokacin mah harda ba mafarki ba,koma muna wasa tare."

Haidar ya karasa maganar cikin tsantsar farin ciki da annushuwa Wanda iya amsar daya bayar akan zahra ita ta sashi wannan farincikin

"Doctor don Allah ka kalli mai wannan halin har zaka ce lapiyarsa kalau yaron da ba zaka taba ganin farinciki da walwala a tare dashi ba sai anzo wani Abu game da zahra" @ dad cike da damuwa shima

Da kyar doctor ya basu hakuri tare da lallaba su,suka tafy akan zai kara yin bincike na sosai akan matsalar bawai don yasan mafita ba

Shima kansa doctor wannan abun yana matukar daure masa kai cos babu inda baa bincika a jikin haidar b,amma lapiyarsa kalau sakamakon yake nunawa

Toh mi hakan ke nufy don bai taba haduwa da ko kwatankwacin irin case din ba a iya yawon rayuwarsa na babba likita da duniya take ji dashi bama kasarsa kadai ba

💖💖💖💖💖

Zaune take ita da yaranta tana shafa cikin dake jikinta Wanda yake haihuwa yau ko gobe

A kullum fatan ta da adduarta shine Allah ya bata diya mace domin tana matukar son diya mace Wanda Allah bai azurtata da ita ba

"Umma wannan cikin ina son ki Haifa mana baby girl muma mu huta da xuwa gidan anty usaina raino."

Daya daga cikin yaran hudun da suke zaune tare da matar ya fada cikin tsananin damuwa daga gani suma suna son diya mace

"Insha Allah usman maxa kullum kayi sallah ka dinga min addua Allah yasa mu samu baby girl."@umma

"umma nima kullum nayi sallah sai nayi adduar pah koma ga yah sadeeq nan ki tambaye shi."@aliyu gadanga ya fada kamar ance shi baiyin adduar

"kun San dai kaf cikinku babu Wanda ya kaini yin adduar koh! kudan in nunawa su anty jummai muma nuna da baby girl ba iya ameena bace."@umar faruk tamkar Wanda yasha damarar yin fada

"Umma nidai Ku baki samu a asibity ba ki siyo mana a inda anty jummai take siyowa tunda kinga suna da diya mata da yawa koh?"

"Ka bari kawai yaya sadeeq ai kodan saboda dukanmu da anty habiba take akan ameena zanso umma ta Haifa mana baby girl."

Nanfa yaran suka fara lissafin abubuwa da koma aikin da zasu yiwa baby girl idan umma ta haihu

"Nidai umma kika sake haifu mana namiji gidan anty usaina zan komah tunda ga zuhra sai inyi rainonta."@sadeeq

"Daman kai ai yah sadeeq ko umma ta haifu baby girl ai kai na zuhra ne."@umar kamar zai bugeshi

" Toh ina ruwanka naga umman zuhra ita ke bani rainonta."

"Zaka ga tamu ai muma."

Haka dai yaran suke ta nuna tsantsar kaunarsu ga diya mace tare da taallaka burinsu akan cikin dake jikin ummansu


*ZOIS CE*

DAGA ALLAH NEWhere stories live. Discover now