Shut up, shut up nace, cikin tsawa yake fadin tayi shuru tare da fadin saboda wannan katon arnen kike haka? Mutumin daya gujeki, damai ya fini? Kyau? Kudi? Nasaba? Gata? Suna? Takama? Ko me dame ya fini Afrah inada abubuwan da wannan bashi dashi kuma harya mutu bazai samesu ba, nufanta yayi tare da kamota ya rike mata hannu yace mai kike so kuma a duniya? Mai kika nema kika rasa? Fadamun duk bukatunki nayi miki alkawari zanyi miki indai Hakan zaisa ki cire wancan arnen cikin ranki......

Enough karka Kara kiransa da arne, domin ba arne bane ya amshi kalman shahada ya musulunta, kaga dakai dashi duk abu daya ne yanda kake musulmi Shima haka yake musulmi, bari kaci in fada maka wani abu, duk abubuwan daka lissafa bakai karya ba, kafi muhd shi Amma banda suna domin muhd mahaifinsa ba a Nigeria kadai ba harta kasashen duniya an sanshi, maganan kudi ko kyau bana bukatar su indai zan samu kwanciyar hankali, na tabbata inda shine bazai taba aibantaka ba ......

Daga hannunsa yayi zai mareta komai ya tuna kuma ya fasa ya sauke hannun Yana furzar da iska mai zafi, ita Kam harta rufe ido Marin kawai take jira, Jin shuru yasa ta bude ido ta ganshi a gefe sai faman zarya yake a dakin kaman mai parade kallo daya zaka masa ka gane ranshi a matukar bace yake sosai

Cikin sanyin jiki ta fara tafiya domin barin dakin, har takai bakin kofa taji ya kamo mata hannu inda ya dawo da ita cikin dakin yace inaso ki sani komai kike bukata zan miki Amma har sai kin haifa mun bbyna cikin koshin lafiya

Kallonshi tayi zatai magana komai ta tuna kuma tayi shuru tare da girgiza kai alaman yana son mai data karamar yarinya wacce zaima wayau, wato inta haiyu zai rabu da ita, uhm ita a yanda take kallonsa tasan komai zai fada ba gaskiya zai fada ba, ko wannan maganan daya fada na cewa inta haiyu zai rabu da ita tasan yana son ta kwantar da hankalinta ne saboda kar wani abu ya samu bby dinsa, dan tasan inta itace komai ya sameta ko a jikinsa..... Katse mata tunani yayi da fadin Afrah ina son ki sani sonda nake miki gaskiya ne Koda yanzu ko kuma gaba zaki tabbatar da irin son da nake miki may be a lokacin time ya kure miki, sannan ina son ki sani wlh sonda nake miki ban tunanin shi wanda kike so yana miki irinsa......

Aida sauri ta kalleshi alaman karya raina ma kansa wayau, taya zaice sonda yake mata yafi na mohd dinta, uhm wato shi wannan yaudaran nashi ta haka yazo, ya manta duk irin abubuwan da yayi mata wanda mohd ta tabbata koda giyar wake yasha bazai taba mata yanda shi yayi mata ba..... Kaman yasan abunda take tunani yace Afrah duk abunda kika ga inayi miki kishinki yasa nake miki shi

Zama tayi a kasa domin ta gaji da tsawuyan ita ba soja ba, ba kuma matar soja ba balle ace tana taya mijinta aiki lol, ganin ta zauna a kasa yasa shi fadin haba ya zaki zauna a kasa tare da kamo ta yana kokarin dagata sama......... Duk wannan abunda yake faruwa tsakanin Afrah da As Zainab najinsu gaba daya jikinta yayi sanyi sannan ta kuma tabbata Mohd shine matsalan su, ta kuma tabbata har yanzu Afrah tana son Mohd din

Kenan Afrah tana kokarin Mohd ya aureni saboda ya zaman mata dole ta cireshi a ranta tunda yana auren kanwarta jininta kuma, in kuma bai aureni ba tana sa tsammanin zai dawo gareta kenan? Sai faman kaiwa da komowa take a dakin ita daya tana nazari tabbas aure na dashi shine zaman Afrah da As lafiya, Zainab ta tabbatar da soyayyar da As yake ma Afrah gaskiya ce, badan kuma wannan cikin na jikinta yake sonta ba, kaman yanda ita Afrah din tayi masa mummunan fahimta, lallai an sani a tsakiya idan muhd ya auri wata bani ba akwai matsala tabbas dole in ceci wannan jaririn da yake shirin zuwa duniya wajan hada kan iyayensa tare da toshe duk wata hanya da zata zama hanyar barazana ga rabuwan auren su ba. Wani kwalla ne ya zubo mata tare da furta zan tura kaina garesa har in samu shiga cikin ransa koda da digo ne, domin nasan bazai taba mun sonda yake ma Afrah ba duk da shi ban san irin sonda yake mata ba, Amma a yanda ita Afrah din ta bata labarin tasan yana matukar sonta

Wata zuciyar ce take hanarta da fadin karki kai kanki ga halaka, domin iyayen Yaron ba zasu barki ba, kaita girgiza tare da fadin zanyi komai saboda yar uwata Koda Hakan Yana barazana ga rayuwa ta ne, Ina matukar son Afrah ita daya gareni banda wani Dan uwa sai ita, dole inyi komai dan ita....... Daukan wayanta tayi ta kira Mohd kira biyu ya dauka tare da fadin my sis

A hankali ta furta masa kalman barka da wannan lokaci, ya amsa da yauwa, nan taita jansa da hira...... Tun daga wannan rana koda bata kira saba yana kiranta Koda saboda yana jin muryanta kaman na Afrah sunyi mugun sabuwa da ita sosai ta waya sau tari Zainab sai taga Afrah tana zaune zata kirasa suyi ta fira suna dariya, inda ta lura da Afrah Hakan na mata zafi tana jin Hakan zata bar wajan tayi daki tana kuka tare da rokon Allah ya cire mata son Mohd din daga zuciyarta

Zainab tana mata hakane domin ta cire son muhd din daga ranta tasan ita matar wani ce, taba mijinta kulawa, kuma babu laifi Hakan da Zainab take mata ya fara tasiri domin wani zubin in Zainab tana waya da muhd a mai makon tayi dakinta sai tayi na As in yana nan ta fada jikinsa tana hawaye inya tambayeta maike damunta saita kuma fashewa da kuka tana fadin ita ta kosa ta haiyu ta daina shige mai wai cikinta yana son ta dinga manne mai saboda tana son turaren jikinsa, wanda kuma ya Bata baya mata irin kamshin wanda yake sawa, in yaji haka sai dai yayi murmushi, kaman yau yana daki ta shigo inda ta nufi gadon dakin da yake zaune akai yana danna system domin ya fara aiki shima a nan, ta zauna kusa dashi tare da kallon abunda yake dubawa wanda hoton wata baturiya ce wani irin kallo ta watsa mai wanda yayi dai dai daya kalleta shima

Ganin irin kallon da take mai yasa yace lafiya madam. Tace dama aikin ka kenan sai yasa inka fara danna system baka son bari aita kallon matan mutane

Murmushi yayi tare da kamo mata hannunta biyu, sai wani cika take tana batsewa, yace toh ya zanyi Afrah ina kokarin zaba ma bbyna wacce zata miye mishi gurbinki ne?

Da sauri ta kalleshi Tare da fadin mai hakan ke nufi

Yace karki manta alkawarin dana miki idan kin haiyu lafiya zanyi miki abunda kike so..... Wani hawaye ne ya siraro mata a fuska tare da fadin kar kayi yunkurin rabani da abunda zan haifa Dan Allah ka barni da abunda zan haifa zan kula dashi a matsayina na uwa

Yace Afrah bazan miki wannan alkawarin ba domin bazan taba bari d'ana ko y'ata suyi agolanci ba a halin ina raye ba

Cire hannunta tayi daga nashi tace nice nake fama da laulayi da kuma Shan walaha ka gane Hakan mana

Yace nima ina son ki gane cewa duk wani d'a ko y'a burinsu su taso gidan ubansu ba gidan wani ba, inaso kibar wannan maganan plz kiyi fatan Allah ya saukeki lafiya Ina son zama dake har karshen rayuwa ta nida abunda zaki haifa Amma ke kina kokarin gudu na,

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now