Bayan ya kashe Dija sakan baki tayi tana fadin lallai wannan guy din mugun dan rainin hankali ne wlh amma babu komai zanyi maganinsa tsaki taja tare da jefar da wayar ta kwanta

Washe gari da safe tunda Afrah tayi Sallah asuba bata koma bacci ba, gashi tana bukatar yin baccin sosai domin tana ganin a irin wannan halin da take ciki baccin shine maganin damuwarta dan shine zaisa ta mance komai da kowa, sai faman juye juye take akan gadon wanda shine ya tashi Zainab itama tare da fadin jikin ne???

Afrah tace a'a tare da cewa Zainab ina bukatar inyi bacci yaki zuwa mai zanyi dan Allah inyi bacci?

Nan zainab tace ina zuwa tashi tayi ta fita jim kadan sai gata da wayar hjy Fatima a hannunta inda tasa karatun al'qur'ani

Afrah tace ina maganin baccin

Zainab tace gashi nan kina ji. Sauraran karatun al'qur'ani zai yaye miki duka damuwarki zaisa miki nutsuwa inaso kiyi shuru ki dinga saurara

Afrah bata kuma cewa komai ba inda take ta sauraran karatun sai dai kuma abun mamaki wannan radadin da takeji gaba daya taji yana raguwa ga wani bacci da yake son dauketa, aiko ba'afi 30 mnt ba wani bacci mai dadin gaske ya dauketa' ganin haka yasa zainab yin murmushi tare da fadin tabbas duk wata waraka yana tare da Allah ganin tayi baccin yasa ta tashi domin maida ma hjy fatima wayarta inda suka ci karo a kofar dakin hjy fatima tazo shigowa ita kuma tazo fita

Hjy fatima tace tayi baccin

Zainab tace eh tayi baccin, wayar ma nazo kawo miki

Nan hjy fatima ta amsa tare da fadin toh bari inje in dawo ana jira na ga breakfast can akan dimming itama inta tashi ki tabbata taci abinci tasha magani kinji

Zaimab ta amsa da toh sannan Hjy fatima ta kara da fadin koda na fita idan akwai abunda kuke bukata ku gayama jummai wato daya daga cikin masu aikin Gidan kenan, in kuma ana bukatar magana dani kisa ta kirani saina dawo

Zainab ta amsa da a dawo lafiya sannan hjy fatima ta fita

Zainab na zaune a falo tana kallo bini bini taje ta duba Afrah taga Kota farka amma bata tashi ba tana bacci har wajen karfe 12 da wani abu tana ta baccinta,..,,,, sallama akayi aka shigo falon Hjy Binta ce da AS suka shigo harda Kamal nan Zainab ta tashi tana gaidasu cikin girmamawa hjy Binta ta amsa da fadin Zainab yanai jikin take

Zainab tace bacci takeyi tun dazu danko breakfast bata yiba balle tasha magani

Hjy Binta tace ah aiko ya kamata ta tashi taci abinci sai tasha magani ai bazai yihu ta zauna a haka ba ga ciwo babu abinci ba

Ina hjy Fatima??

Zainab ta amsa da tafita

Ganin Afrah sukayi ta fito sanye da hijab tana tafiya dakyar saura kadan ta fadi wanda ta rigada ta sadakar ta fadin ta lumshe ido tare da sakin kara jin an riketa yasa ta fara bude ido a hankali wanda suka sauka akan na AS da take manne a jikinsa

Aida sauri ta fara kokarin jan jikinta daga nashi, shima sakinta yayi tare da fadin ke kin san jikinki babu kwari amma kike tafiya da kanki u have to be very careful.......

Dariyar mum ne yasa Afrah yin shuru daga maganar da taso yi, mum tace in banda abunka in batayi tafiya da kafarta ba dana wa kake so tayi? Ai hakan da tayi shine dai dai ta dinga motsawa sai tafi jin dadin jikin akan mutum ya zauna waje daya, nufanta mum din tayi tare da kamo hannunta ta zaunar da ita akan kujeran falon sannan ta kalli Zainab tace plz hada mata tea ta fara sha , Zainab ta amsa da toh

Hjy binta ta kuma kallon Afrah tace ya jikin naki da fatan dai da sauki? Afrah gaba daya nauyin mum take ji maimakon ta amsa saita gaida Mum din da ina kwana

Mum ta amsa da lafiya hadi da shafa mata fuska tace yanzu yini ne kwana ya wuce, koda yake daga bacci kika tashi...,,,, kawo tea din Zainab tayi mum ta amsa ta fara bata, tana ta lallabata harta shanye tea din duka sannan ta bukaci zainab ta kawo mata maganinta tasha, shima maganin mum ce ta bata suna cikin haka hjy Fatima ta shigo cikin Gidan ganin hjy binta yasa ta saki murmushi tare da fadin yaushe kuka zo

Hjy binta tace tun dazu gaskiya yau da yata zan tafi taya za'a bar mara lafiya bata ci abinci ba balle tasha magani ba, yau kafata kafar diyata gskya

Hjy Fatima tace wlh wani urgent fita ne ya kamani sai yasa ma na fita kin san harkar siyasa in kasa kanka

Hjy binta tace toh na hutarshe ki tare da Afrah zamu tafi yau ni tunda ina gida kullum zanfi bata kulawa har ta gama samun sauki insha Allah, Hjy fatima tace toh babu damuwa duk yanda kika ce hakan za'ayi

As ne ya gaida hjy Fatima haka kamal ma ya gaidata inda hjy Fatima ta amsa cikin sakin fuska, ita kam Afrah gaba daya jinta take wani kala tun sanda taji ance zata koma gidan hjy binta da zama harta warke

Hjy binta ce ta katse ma Afrah tunani da fadin Afrah bari zainab ta hada miki abunda kike bukata sai a tafin miki dashi koh

Afrah murmushi tayi tare da fadin toh cikin wata murya mai kama da kasala

AS dago da kai yayi ya dan kura mata ido lokaci daya ya kauda kai hadi da sakin gajeran tsaki mara sauti tare da kallon mum yace mum inta bimu bazamu koma abuja ba kenan

Mum tace zamu koma mana tare zamu tafi tunda flight za mubi ba zata sha wahala ba, jin haka yasa gaban Afrah ya fadi tare da fadin shikenan kaddarata ta fara

Hjy binta ta kalli hjy Fatima tace inaga zamu tafi Abuja jibi afrah ta zauna sai tayi sallama da iyayenta gobe insha Allah sai inzo da kaina in dauketa inaga hakan zaifi

Hjy fatima tace babu damuwa ai insha Allah amma inaga bari muyi wata magana a ciki

Tashi sukayi inda suka nufi dayan falon gidan aka rufe kofa wanda hakan bai bani damar jin mai suke tattaunawa ba

Falon ya rage daga Afrah sai kamal da mai gayya mai aiki AS, kamal ne ya katse shurun da fadin Amaryar mu ya kikai shuru kodai jikin ne

Murmushin yake tayi tare da fadin eh

Shi kam AS danna wayarsa yake amma yana jin abunda suke fadi

Kamal yace sannu Allah ya kara sauki na daiga alama da amaryar da angon dukanku bakwa son magana lallai ina tunanin zamanku da kuma yaran da zaku haifa...,,, aida sauri Afrah ta tashi tayi ciki domin jin maganan kamal din tayi kaman saukar aradu taya ma zaice ita dashi zasu haifa yara god forbid bata tunanin a yanzu da soyayyar David ta kamata akwai wani namiji da zata iya hada jiki dashi indai ba David dinta ba...... wani kuka ta saki tuna alkawarin da tama mahaifiyarta akan zata bi mijinta kuka take sosai tana fadin why why me mai yasa mai yasa zan fuskanci wannan mummunar kaddarar wani laifi na aikata na shiga uku bazan iyaba bazan iya jurewa ba son Mohd zai kashe ni zai zautar dani zan mutu.....,,,,,, kirjinta ta rike tana rusga kuka sosai nan da nan idonta ya kumbura kanta ya fara mata ciwo, ta tabbata koda tace zata iya yaudarar kanta kawai take domin kuwa son muhd ya gama tafiya da ruhinta bata ji bata gani...... jin karar an bude Kofar yasa tayi saurin goge hawayenta dan kar aga tayi kuka hadi da lumshe ido alaman bacci ya fara daukarta hjy fatima ne da hjy binta ganin kaman bacci ya dauketa yasa suka bar dakin dama hjy binta tazo mata sallama ne akan sai tazo daukarta gobe

Shi kam uban gayyar tun sanda tabar wajen yaja wani tsaki tare da fadin mad girl kaman nason mishi magana ya dakatar dashi tare da fadin karka fara sannan wannan shine last warning karka kuskura ka kara mun magana akan wannan yarinyar sanin kanka ne bana son raini hope ka fahimta

Kamal yace amma AS kai kace kana son aurenta miye,.,,,,,, enough ya furta cikin bacin rai karka manta I hate to much question so u better keep your mouth shut....... Tashi yayi ya fita cikin fushi kai tsaye mota yayi yana huci shi harga Allah baiyi niyan zuwa inda yarinyar nan take ba, Mum dinshi ce tasa yazo inda badan mum dinshi ba toh da babu abunda zaisa yazo kafada ya daga tare da fadin barin in cimma burina in cire mata girman kan da take ji dashi sannan in sallameta domin bazan iya zama da abun da zai zamar mun damuwa ba..........

Mai son Complete din wannan littafin zai iya samu a YouTube channel mai Suna "Al'AMARIN DUNIYA"

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now