Likitoci sun samu sun samo bakin zaren inda aka ceci rayuwar Afrah da taimakon uban giji, an samu anyi mata alluran bacci wanda yasa bacci ya dauketa mai nauyin gaske hakan yaba mama daman nutsuwa tare dayin sallah tana rokan Allah akan ya yayema yarta wannan damuwar ya kuma bata ikon cin wannan jarabawan daya sameta ya bata hakuri hadi da dangana, Ranan dai mama bata rintsa ba har asuba tayi, still dai Afrah na bacci bata farka ba

Tun wajen karfe 9 hjy Fatima da Zainab suka zo, hakan yaba mama mamaki domin a yanda hjy Fatima take daukan Afrah bata taba tunanin zata iya zuwa yanzu da sassafe ba..... Hjy Fatima ce ta katse ma mama tunani da fadin ya jikin nata???

Mama ta amsa da fadin da sauki sai dai jiya ban runtsu ba domin aman jini tai tayi saida likita yazo tunda ya fita take ta bacci har yanzu dama yace kar In damu zata jima tana bacci

Hjy Fatima ajiyan zuciya ta sauke hadi da fadin Allah ya kyauta sai kici abinci gashi nan mun kawo kije gida ki samu ki kwanta zuwa anjima kya dawo tunda mu munzo

Mama cikin mamakin jin kalaman hjy Fatima yasa tace a'a basai naje gida ba zan zauna inga a wani hali zata tashi

Hjy Fatima tace matsalarki tunda mu bazamu iya kula da itaba sai ke saiki ta zama ai

Mama cikin sanyin jiki tace kiyi hakuri ba haka nake nufi ba, ko naje gidan bazan samu nutsuwa bane,na tabbata bazan iya runtsawa ba, saboda halin data shiga jiya bayan kun tafi ya daga mun hankali sosai kiyi hakuri inga farkawarta

Hjy Fatima tabe baki tayi hadi da cewa toh...... Shigowan Abba da yin sallamarshi ne yasa duka idonsu yayi bakin kofa, Abba gaida hjy Fatima yayi ta amsa cikin fara'a hadi da fadin daga ina haka na ganka kaman an koroka

Yace wlh daga gida nake, ko wanka ban samu nayi ba na fito haka domin inga ya jikin Afrah din Yake

Hjy Fatima tace da sauki amma yanzu kazo ka koma kaje kayi wanka kasan dai sirikin ka zai zo bai kamata su ganka a cikin wannan halin ba, duk da dai ansan halin da kuke ciki, kallon Zainab tayi tare da fadin Zainab maza tashi kuje driver na ya kaiku kisa mishi ruwan wanka in yayi kwa dawo aiba ka zauna haka ba duk datti

Tashi Zainab tayi suka fita kaman yanda Hjy Fatima ta umarta haka suka tafi gida harda Abba domin yayi wankan

Basu dade da fita ba kam Afrah ta farka tare da salati tana mika..... Lokaci daya ta fara kallon dakin tare da kokarin tashi inda dai dai lokacin mama ta karaso tana kiran sunanta da Afrah sannu ya jikin naki

Afrah ido ta kura ma mama tana son yin magana ta kasa saboda bakinta ya mata nauyi, Hjy Fatima itama ta furta Afrah ya jikin naki

Afrah da ido tabi hjy Fatima itama ba tare data bata amsa ba, wani irin hawaye ne kebin kuncinta lokaci daya ta bude baki ta fara magana da fadin Mama ina son David amma ya juya mun baya ni nasan bayin kanshi bane, iyayensa ne suka mishi wani abu domin ya tsaneni, sun cutar dani sun lalata mun farin cikin rayuwata sun ruguza mun duk wani annuri na..... Mama ce ta katseta da fadin Afrah kiyi hakuri ki daina fadin haka, karki manta duk bawa yana da irin tashi jarabawan da Allah ya tsara mishi, inaso ki sani Allah yakan jarabi bayinshi da abubuwa kala kala domin ya gwada imaninsu, bakya tunanin irin taki jarabawar kenan?? Yau danya gujeki wanda kike so kika san mai Allah ya tsara miki??toh in kika kasa hakuri dashi idan Allah ya dauki rayuwarsa ya zakiyi kuma??

Afrah kuka dai takeyi mai taba zuciyar duk wani mai tausayi

Mama taci gaba da fadin Afrah inaso ki sani duk bawa yana da irin tashi kaddarar inaso kici taki ki kuma yi hakuri ki dauki kaddara ki cire yaron a ranki tare da daina tunaninshi domin ke yanzu matar wani ce......

Wani irin dum dum Afrah taji a kanta tare da nana kalman ke matar wani ce?? Mai hakan yake nufi toh??

Mama taci gaba da fadin an daura miki aure a ranar da kikai waya zaki zo kano aka daura miki aure.......

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now