57

18 2 1
                                    

57

*********Suna zaune su dukan su, a asibiti Zarah ta haihu da safe a gida yayin da Hafsah ita kuma tun jiya da daddare suke asibiti ana fama har yanzu gashi wani daren yana ƙoƙarin kawowa, hakan yasa su tahowa har Zarah asibitin. Suka yi zugum da su. Deeni kam wani irin abin tausayi ya zama dan ya fi mai labour ɗin ma shiga tashin hankali, dan be runtsa ba, wata irin doguwar naƙuda take yi har ta gaji ta galabaita. Yana rungume da Noor dake kukan ina Mommyn ta. Itama har ta gaji tayi shiru tayi lamo sai suka zama abin tausayi dukan su.

Likitan ce ta fito tace da shi ya shiga tana san ganin sa.

"Ya Deen mutuwa zan yi ko?

Rungume ta yayi sosai a jikin sa ya kasa magana, sai ga Deeni da kuka.

"Mr. Deen kai da zaka ƙarfafa mata gwiwa shine kai ma zaka yi kukan?

Rungume ta yayi a jikin sa yana girgiza kan sa sosai, ya kasa furta koda kalma ɗaya ce.

"Ka sa a hannu za'a yi mata CS".

Banda girgiza kan nan babu abinda yake yi, yayin da ya kasa sa hannun dole sai Baba akai kai wa yasa hannun. Aka fara shirye-shiryen shiga theater room. Sai a lokacin Allah yayi ikon sa ta zankaɗo ƴaƴan ta guda biyu    duka maza.

Wata irin ajiyar zuciya ta ajje mai zafi tana shafa kan ta, yayin da Deeni ya saki murmushi haɗe da hawayen wanda yasa ƙwallar shiga cikin idan ta, tana kallan sa cike da tausayi. Yadda ta wahala tasan shima zuciyar sa ta wahala.

"Ina san ki Hafsah Usman Madaki".

Murmushi suka saki a tare kafin ta lumshe idan ta, aka ɗauro mata yaran a ƙirjin ta bata da karfin da zata rungume su, shima ba karfin ne da shi ba ji yake kamar iska ta hure shi. A tare da shi aka gyara ta tsaf aka maida ta ɗakin hutu batare da an fitar da ita ba sun gan ta. Da ita da yaran nata, har yanzu Deeni ta matar sa yake ba ta  yaran ba.

"Ka kwanta".

Ta faɗa tana nuna masa wurin kwanciyar da hannun ta, girgiza kan sa yayi yana kallan ta  cike da wani irin tausayi, yana tuno da ta sa mahaifiyar ina ma tana raye? Sai ƙwalla ta zubo masa yana kallan ta cike da wani irin tausayi da kuma bata wani irin girma da matsayi. Yana ganin mazan da ba su san kima da darajar mata ba, mata wa su irin mutane da suke da kima da darajar da ba'a isan an aibata su ba. Mata sune jigon rayuwar mu gaba ɗaya, wanda be girmama mace ba, wanda be bawa mace wani girma da matsayi ba to be cika namiji ba. Domin sune suke sadaukar ga komai na su domin ganin cewar mun amfana.

"Kiyi bacci".

Ya faɗa yana kwantar da ita. Murmushi tayi masa kyau tana kallan sa.

"Gani nake idan na rufe ido na na buɗe ba zan gan ka ba".

Murmushi yayi mata yana kwanciya a kan gadon tare da rungume ta tsam a jikin sa yana raɗa mata addu'o'in da sai a yanzu yake jin suna zuwa masa bakin sa.

Babu wanda ya zo inda suke domin an kawo musu yaran sun gan su, sannan aka ce kada a dame su har zuwa wani lokacin da zata tashi da kan ta. Wannan tsayin lokacin da ya ɗauki Deeni idan sa biyu be rintsa ba, yayin da ita kuma take baccin ta a jikin sa hankali kwance bacci mai cike da tarin gajiya. Sallahr Magriba da Isha yayi sannan ya zubawa yaran ido, yana kallan su, babu wanda zai ce ga kamar su a haka domin ba suyi kama da kowa ba ga su identical da su sai de ɗaya na da tawa a gefen idan sa na hagu, ɗayan kuma a na dama, murmushi yayi ganin cewar Zarah da Sadiq ma haka suke, da mace da namiji ya samu tabbas su zai sawa wannan sunan, domin a Duniya yana ƙaunar farin cikin ƴan uwan sa. Ameer ne ya kasa haƙuri ya dawo shima satar hanya yayi ya gudu daga sallah. A hankali yayi knocking ɗin ƙofar kafin ya shigo da sallama, da kallo Deeni ya bishi har ya shigo.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now