45

16 1 0
                                    

45

*******Murmushi Hashim yayi musu dukan su dan babu wanda yayi hakuri bari wani ya shiga wani ya fito, babu abinda ya same shi a haka banda ƙwarjanewar da yayi ɗan yi a fuska, wani murmushin ya sake musu tare da ɗan riƙe hannun Umman sa.

"Umma na so ace ina da lokacin da zan tsaya na kula da ke, na koyi rayuwa, amma ko yanzu Alhamdulillah, na gane rayuwa, na gane akwai mutane iri iri a duniyar nan ta mu. A tunanina talaka shine wanda baya da kuɗi. Amma ban sani ba a talakawan ma ashe iri daban daban ne. Umma tunda nake ban taɓa ganin wuri inda kuke rayuwa ba, amma gashi a sanadin wani bawan Allah Umma na gane ke ce Mahaifiyar da ta haife ni. Ko ba komai a hakan nasan rayuwa".

Sai ya kalli Mu'azzam."ka kula da Umma a lokacin da baka san kana da wani Yayan ba, a yanzu kuma zan baka amanar ta a hannun ka. Wannan karon kulawa biyu zaka mata, kada ta ji cewar ta rasa wani ɗan ta".

"Ɗalhat da ni da kai duka munga rayuwar mutane, munga yadda kuɗi ke masu wahala, munga yadda wutar lantarki ke musu wahala, munga muhallin su, munga shiga kasuwa mun ga ya suke shan wahalar rayuwa.  Kai kan kasan wani gidan be wuce rabin toilet ɗin da muke amfani da shi ba. Suturar da muke sawa bata wuce wacce za'a ciyar da wasu ahalin ba har ta musu yawa. Daga sanda naga yadda suke rayuwar nasa a rai na cewar zan zama shugaban da zai share musu hawayen su, hakan ba zata faru ba sai na fito takarar siyasa. Zaka iya min wannan alfarmar dan Allah?

"Ai babu inda zaka je Hafiz, kana nan babu inda zaka tafi".

Murmushi yayi da wani irin tari a haɗe da jini nurse ɗin dake saman sa ne ya goge masa jinin, ya bi su kowa da ido har ya sauke idan sa akan Hafsah. Murmushi ya sakar  mata.

Yace, "Mijin ki, mutumin kirki ne, tun ranar da muka fara haɗuwa dashi na gane haka? Kin tuna? Ranar da kika mareni? Kiyi haƙuri da abinda ba maki lokacin kar kiga laifi na".

Hawaye take yi haɗe da murmushin tuna mata da komai ya da ya faru a lokacin. Daga ita shi kowa murmushi yake. Ameer dake gefen sa ne yasa hannun ya kamo shi.

"Ni tafiya zan yi na barka da ita kana san ta ko?

"Wa?

Ameer ya faɗa masa a hankali ganin shima a hankali yake masa magana.

"Ita wacce idan ka ganni kake basar da ni mana, magana ma fa baka iya min sosai, ko sunana bana jin ka taɓa faɗa. Burina bece naga an kula da ita ba sosai, kada ta rasa komai na rayuwa, idan ma ta sa wani abun kada ta rasa farin ciki. Ina san naga tana farin ciki kamar yarda kake sata a kullum. Daga kai har ita zuciyar ku a haɗe tun tasowar ku. Banji labarin komai ba sai yau da Deeni ke faɗa min tarihin rayuwar ku, ashe kuɗin ba ƴan uwan juna ba ne".

Hawayene ya zubo masa Ameer ya goge masa tare da rufe masa bakin, shi kuwa tunawa yayi da irin yarda ɗan uwa ya cuce dan uwa, ɗan uwa ya ci amanar ɗan uwan sa, gashi su kuma ba su san juna ba, maƙwabta kawai ce ta haɗa su me ya fi wannan?

"Ba sai ka ce komai ba, nifa kawai shaƙuwa ce bakomai ba, ka dena faɗan hakan. Ni ƴar ku zan aura".

Dariya maganar ta bawa Hashim, sai ya kalli Zarahn da bata iya haɗa ido da shi, ta ɓoye a bayan Halima tana tsiyayar hawaye dai de ga leƙo shi. Murmushi ya sake yi ya fara tari yana so yayi magana. Sai da ya lafa masa aka goge jinin dake zubo masa ta baki.

"Ka saurari abinda zuciyar ka ke faɗa maka ko sau ɗaya ne.....

Wani tarin ya sake sarƙe shi, likitan ne ya zo yace ya fita za su sake duba shi, yana so yayi musu magana amma babu halin yin haka, da kallo yake bin su yana da buƙatar ya sanar da su abinda yake zuciyarsa yana da tarin zancen da yake so ya sanar da su, da hannu yake miƙa musu akan su dawo amma innaa, Ameer kam ƙara damƙe hannun sa yayi sosai, dan Ameer mutum ne me san mutane duk da ace faɗa kuka yi indai baka da lafiya to yana kusa da kai, hakan hasa yaƙi ficewa ya tamke hannun sa gam yaƙi ya sake, wani irin yana yi yake kallan sa a cikin yake cusa masa kalmar shahada a bakin sa ganin ƙoƙarin sa na so yayi magana. Haka ya ringa nanata masa yana biyawa bakin Ameer ɗin kawai yake kallo shi hawaye shima hawaye ga wani irin jini dake ɓulɓulo masa ta baki amma duk da be saurara ba da abinda Ameer ke ƙara sanar dashi, yayin da likita da nurses suke aikin su. Ganin jinin ya fara fitowa ta hanci yasa Ameer sakin wani irin kuka yana miƙewa tsaye akan sa, ɗiiiiiii suka ji injin na'urar dake amfani da bugun zuciyar sa ya faɗa ya kuma ji lokaci guda ya saki hannun sa dake cikin nasa. Tsak ya tsaya yana kallon sa ga idan sa a cikin nasa yana masa murmushi, amma bega ya ƙifta ba.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now