32

14 1 0
                                    

*****Dukan su suna zaune akan kujera kowa ya ɗaura ƙafar sa akan table ɗin dake tsakiya da su, suna aiki a system. Babu wanda ya ce da kowa komai tun shigowar su da suka shirya bayan sun dawo asibiti sun kai Baba, aka ga jikin sa alhamdulillah ana samun sauƙin, kuma faɗuwar da yayi  tasa jikin sa ɗan fara dawowa.

Cikin wannan sanyayar muryan tasa yace, "Gobe idan Allah ya kaimu zan je zan tafi Anadyr".

Banza tayi da shi kamar ba da ita yayi magana ba.

"Hajiya".

Ta sake yin shiru.

"Hajiya fa".

Namma shiru.

"Hafsah".

Ta sake yin banza da shi.

"Hajiye fa".

"Kina ji ina maki magana kika yi banza da ni?

Ɗagowa ta kalle shi.

Tace, "Daman da ni kake?

Shima zuba mata idan sa yayi mai cike da kasala da gajiyar dake cin sa.

Tace, "A'a na ɗauka waya kake yi kaka faɗawa matar so ai".

Wani shegen malalacin murmushi ya saki.

Yace, "To sai ki sauke".

"Me?

"Kika kin ɗauka. Na ce sai ki sauke".

"Aitoh".

Ta cigaba da abinda take, yayin da a ranshi yace 'ana daf da zuwa zo waje'

"Gobe zan tafi".

Shiru tayi masa.

Yace, "Wai ba zaki yi magana ba?

"Me zance?

"Mijin ki zai yi tafiya amma kike cewa me zaki ce masa? Idan na je na mutu fa?

"Sai naga dama nace  Allah ya jikan ka. Idan ban gani ba kuma nayi shiru".

"Haka kika ce?

"Na sake faɗa ne?

Girgiza kan sa yayi alamar a'a. Sannan ya sakar mata murmushin da bata gane masa ba, ita fa wannan murmushin da yake yi kala da kala ba gane masa take ba, hakan yasa ta ɗauke kan ta, ta cigaba da abinda take yi. Sai de kuma har ran ta so take ta sanar shi abinda idan ta ya gane mata, amma bata jin zata iya yin hakan, bata san ma ta ina zata fara sanar da shi ba duk abin da ta ganewa idan ta. Yayin da ya zuba mata ido yana kallon ta, so yake ya ji meye haɗin ta da Najma da har ta ɗauko musu yarinya ta kawo ta? Haka kawai ba zata zo da yarinya ba batare da dalili ba, sannan kuma yasan halin ta farin sanin, idan aka ɗauke Sabir babu wani yaro da take yiwa wasa, amma wannan yarinyar kafin ta yaga  annurin dake tattare da ita. Sannan da drivern ya zo ɗaukan ta yaga sojojin da suka rako yarinyar duk a ɗaukan mutum ɗaya kawai? Sai de idan da Baban yarinyar suke tare. Kara kallan yayi yaga itama tunani take kafin daga ƙarshe ta rufe system ɗin ta tafi ta kwanta a inda ta yi shimfiɗa.

Shima tashi yayi ya kashe wutar, ya je ya kwanta, sai da ya tabbatar da tayi bacci sannan ya je ya ɗauko ta ya dawo da ita kan gado. Haska fuskar yayi da fitilar wayar sa, yana ƙare mata kallo,  hannun sa ɗaya ya sa ya fara shafa fuskar ta da shi yana murmushi, shi kadai yasa me yake ji akan yarinyar nan. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kashe hasken bayan ya morewa kallan sa, sannan ya ɗauko bargon da tayi shimfiɗa ya rufe su da shi yana rungume ta. Ruwan da aka yi ne yasa garin yin san yin hakan ya bata damar shigewa jikin sa tana ƙudundunewa. Ba su ne suka tashi ba sai da gari yayi haske, a kusan tare suka buɗe idan su ya haɗa cikin na juna, sun jima suna kallan kallan kallo kowa da abinda yake yawo a zuciyar su kafin ta yi ƙoƙarin tashi ya maida ta.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now