43

16 2 0
                                    

*******Mu'azzam yana tashi yaga be ga Hashim ba, sai yayi tunanin ko yana bayi ne, jin shiru yasa shi nufar toilet ɗin, ya ɗan yi magana alamar da mutum? Ya ji shiru sai kawai ya shiga, duk be kawo komai a ran sa ba ya tashi su Umma yana fita. Sai da ya dawo daga masallaci take tambayar sa ina Hashim yace be gan shi ba. Tunan tayi ko ya tafi gidan su Ɗalhat daga haka suka kwanta suka yi bacci da ba su yi ba.

Sai da suna naɗe shimfiɗa yaga takardar nan da ya ajje masa.

"Umma Hashim Abuja yaje".

Ya faɗa yana nuna mata takardar dake hannun sa.

"Hashim haka yake?

Ta faɗa cike da mamaki.

"Bana so ya je ya wufun tar min da shi fa".

"Umma ki masa addu'a in sha Allah yadda ya tafi zai dawo".

Ajiyar zuciya ta sauke, tana masa addu'ar a cikin ran ta sai de kuma gefe na zuciyar ta yana mata zafi sosai, tana fatan da addu'ar ba riƙe shi A. Madaki zai yi ba.

"Bari naje na sanar wa da Ɗalhat daga nan sai na je, naji ya ake ciki na zancen su Oga Deeni".

"Allah ya kiyaye".

Ta faɗa jikin ta a sanyaye, ko wanka be yi ba, kawai kayan jikin sa ya sauya ya tafi gidan su Ɗalhat, lokacin sun fito za su tafi kasuwa kenan cikin mutunci suka gaisa.

"Hashim ya tafi Abuja".

Dafe goshin sa Ɗalhat yayi yana jin kan sa na sara masa lokaci guda.

"Ya bani wannan na baka".

Ya faɗa yana bashi takardar, juyawa kawai yayi, to me zai ce masa kuma? Bayan jiya ya gama haɗa shi da Allah da Annabi amma shine zai tsallake ƙafa ya yi tafiyar sa ?

Ran sa ya ji yana ɓaci sosai, ji yake kamar yayi tsuntsawa ya je ya sami Hashim su yi wacce za'a yi. Anya yasan halin Dad kuwa? Yasan rashin imanin sa kuwa? Tunda ya iya raba shi da iyayen sa baya tunanin a yanzu zai iya raba shi da duniyar gaba ɗayan ta?

"Innalillah wa'inna ilaihirraji'un".

Ya samu faɗa yana dafe bango, da sauri Mu'azzam ya taimaka masa ya zauna a ɗan dakalin dake ƙofar parlourn yana jin wani irin ɓacin ran Hashim na ƙara yin yawa a ran sa.

"Ya gaji da rayuwar ne, rabu da shi idan ya mutu Allah ya jikan sa".

Ya faɗa yana soke takardar a aljihun sa tare da tashi tsaye wai zai tafi.

Mu'azzam yace,"A'a ba haka zaka ce ba gaskiyar magana, ka kira shi idan be je ba kar ya je, idan ya je kuma ya gaggauta dawowa, muna da buƙatar sa, Umma zai yiwa ba mu ba".

Wani irin kallan baka da hankali Ɗalhat yayi masa.

Yace, "Dan Allah kar kayi fushi da shi ka kira shi".

Ɗalhat yace, "Mu'azzam kasan waye ni kuwa? Idan nace ba zan yi abu ba, to ba zan yi ba. Be ga Umman ba, be duba halin da take ciki ba, da kuma irin soyayyar da ta fara nuna masa ba? Shine ya sa ƙafa ya tsallake ya tafi batare da tunanin komai ba. Bashi da hankali Shiyasa".

"Amma...."

"Ka bari Daad ya koya masa hankali".

Ya faɗa yana ƙarashe maganar da goge ƙwallar da ta zubo masa. Duk yadda zai musu bayanin waye Dad ba za su taba ganewa ba, gwara ma yayi kukan nasa tun kafin gawar Hashim ta iso, shi kuma sai ya fara lallashin mutanen da zasu yi kuka bayan sa. Mu'azzam sakar baki yayi kawai yana kallam Ɗalhat, duk kallan da yake masa, ganin sa yake mutum mai haƙuri da rashin hayaniya, ashe kowa idan aka taɓoshi masifa ce da shi. Da kallo kawai ya bi shi har ya hau machine zai tafi ya bishi yake maganar Deeni, jin yace masa ta can zai biya yasa shi ya hau suka tafi tare.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now