3

26 2 0
                                    

           ✨ *ZAHARADDEEN* ✨

                            3.

*****Ameer yace, "Yaya Deeni tare da kai zamu tafi fa".

Taufiq yace, "Yaya Ameer ka nace sai ka je Kanon nan".

Hajja tace, "A'a kaga bar shi yaje ya samu kuɗin sa, tunda ku kuna zaune a gida zaman kashe wando nima da kuke gani na nan ba'a zaune nake ba. Da idan Banda zamani ma goɗai-goɗai da ku kuke zaune sai an baku. Samu kuka yi ai".

Deeni yace, "Me zai je yayi acan ɗin?

Hafiz yace, "Rabu da shi dan Allah. Shirmen sa ne wai shi kasuwanci zai yi".

Murmushi Deeni yayi yace, "A'a idan har Baba ya yarda shikenan, sai mu tafi".

"Wai idan yaje me zai yi ɗin?

"Ka manta Sadiq yana nan yana cigaba da aikin su Baba ? To shima ba sai ya cigaba da kula da wajen ba. Kaga daman Sadiq ne kawai ɗan gida shi kuma yanzu service yake yi, dan Ameer yaje shima kafin ya tafi shi kuma Sadiq ya gama".

"Makarantar ma sai yayi acan idan ya samu".

Ya kuma faɗa.

"Ni Yaya Deeni ba zan yi makaranta ba, ta isa haka makarantar".

Hajja tace, "To mun ji wannan. Idan kayi kuma ka zo kana jin daɗi kada naji kada nagani".

"Kina ina lokacin? Ai lokacin ƙasa ta gama binni ki kuma ma ni ba zan yi ba. Kawai ayi ta karatu ana sake maimatawa?

"Yaro kenan, to ina nan sai naga auren ka".

Dariya kawai yayi ya rabu da ita. Yayin da suka cigaba da magana har Hafiz ya yarda akan cewa zai bishi ɗin. Sosai hakan ya yiwa Deeni daɗi. Ya roƙi kar a sanar da Baban ma kawai  idan ya dawo zai ji. Dake Baba da Umma sun tafi Umara idan suka dawo kuma za su tafi amma banda  Hafsah.  Daƙyar ya yarda zai kwana ana shima sai da Hajja tayi magana tukunna ya yarda, sosai Mamancy take ganin kimar yaron da kuma darajar sa, tun suna yara har yau be sauya hali ba daga wanda ta san shi da shi daga shi har Hafiz tana kuma yi masa addu'ar dacewa a rayuwar sa tare da yi masa addu'ar mace ta gari dan mace tsab zata iya sauya masa halin sa.

***"Ta jima tana gunguni ita ɗaya musamman  idan ta tuno amsar da ya bata 'ga wanda ban sani ba' haushi abin nan take ji kamar tayi kuka haka take ji. Ita kaɗai tayi ta ƙunci abinta. Ta gama, ba su ƙara haɗuwa ba sai washegari da ya zo tafiya ba kuma tasan da Ameer za'a yi tafiyar ba, kawai de ta gan su ne tare da ƴan gidan su za wai za su raka su airport, gaida su kawai tayi ta wuce kitchen. Tana ƙara tuno abinda yace mata. Wai ita aka faɗawa haka? Ƙwafa kawai tayi.

Deeni ne ya dubi Hafiz yace, "Zancen auren Ameera ka ƙara dubawa fa. Kar ka manta".

Murmushi Hafiz yayi yace, "Ka damu da auren nan har haka?

Sanin kan sa be taɓa damuwa da wani abu ba, koda ya na damun sa, shi kaɗai yake warware abin sa, amma wannan batun auren yasan rayuwar yarinya ƙarama za'a jefa a cikin garari duba da irin tarbiyyan shi kan sa yaron. Bama shi kaɗai ba duka gidan na su kowa da irin yarda yake rayuwarsa. Hakan yasa shi murmusawa kawai be kuma cewa komai ba. Har suka ajje su a airport be ƙara magana ba sai sune da suke maganar su.

*****Zarah ce a zaune a waje wurin ajje motar su an baza tabarma anyi mata ƙunshi ana mata kitso, Sadiq a kusa da ita yana aiki a system  kuma babu nepa dan indai da nepa ba abinda zaka ga Sadiq a waje yana ciki. Kallan ta yake yarda ake mata kitson, shi sam be yarda da zuwa gidan kitso da ƙunshi ba gwara su zo ayi mata, tun suna talaucin su ya tsani sallah ta zo ace su je su ɗauko su daga gidan ƙunshi wani lokacin sai karfe biyun dare za su je su dawo dasu wannan abun haushin sa yake ji sai dai be taɓa nunawa ba. Yanzu kuwa da ke ya kai kuma Allah ya hure musu kuɗin da za su biya su zo har gida ayi musu alhamdulillah sun gode Allah....

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now