19

21 1 0
                                    

*****Biyar nayi ya fito, yau ma tare da  wacce ya kira Hafsah suka fito a gaban idan ta, taɓe baki kawai tayi tana wucewa ta tafi itama ta shiga motar ta.  Suna zuwa ya wuce wurin su Baba kamar jiya.

"Zaman ɗaki da parlourn ba zai dame shi ba?

Deeni ya faɗa yana kallan Hafiz.

Umma tace, "Aikuwa ba, da idan ya ɗan fita zai ji daɗi duka yau ba nepa".

Hafiz yace, "Naji dan fita masallaci ɗazu ana cewa transformern ce ta lalace".

Jinjina kan sa yayi ya tashi ya fara tura Baba. Hafiz yace, "A'a kaga ka je ka huta yanzu ka dawo fa".

"Bari na fita da shi sai na wuce ta can".

Tare suka fito su dukan su, suka yi wajen sabon part ɗin su dake shine da bishiyoyi a wajen irin bishiyar turaren nan masu sanyi da daɗi. Ganin Baba na kallan ƙaramar ƙofar dake wurin yasa shi nufar wajen.

Yana cewa, "Baba muje ka ga, Barun ma kaga yadda suka yi yawa".

Hafiz yace, "Kai de da san kiwo kake har yanzu".

Deeeni yace, "Kiwo da noma da kuma kasuwanci sune albarkar ai".

Hafiz ya jinjina kai, alamar haka ne, ta window Hafsah ta gano su, itama t fito tana yafa mayafin rigar material ɗin da ta saka. Harda gudun ta, damma sun tsaya ɗaga Baba shiyasa ta cimmu musu.

"Ina zaku je haka? Ina ne nan ɗin?

Babu wanda yayi mata magana a cikin su, zata sake magana kenan ta hango Geese ɗin da ya taho ganin Deeni da yayi yana kukan su sai ga ɗayan nan shima ya taho sun haɗu suna gudu za su taho wajen sa, har ga Allah ta ɗauka wajen ta za su kawai ta ƙamƙameshi tana.

"Abokin Yaya dan Allah ka musu magana kar su zo".

"Aka maki wurin ki za su zo?

Cewar Hafiz dan gaske haushin ta yake ji, kawai gani yake cutar Deeni take yi.

"To ba ga su nan ba suna..... wayyo Allah".

Ta faɗa tana shigewa bayan sa, ganin dagaske wurin suka yo yayin da shi kuma ya tsugunna musu kowanne su ya saka kan sa a kafaɗar sa guda ɗaya, yana shafa musu suma shafan shi suke alamar de sun saba. Sandarewa tayi a wajen da ɗumbin mamakin sa, wannan ai ƙazanta ce. Kafin ya kora su, suka fara zagaya wajen, yana da girma wajen sosai ba laifi. Tsuntsaye de ga su nan iri da iri wani ma bata san su ba,  dabbobin ne ya siyar ya bar awakan.

Wurin tattabaru ne a ƙarshe saboda yawan su an ɗan musu gidan su a gefe, ta net ɗin suke kallan su dan ana buɗewa za su fito sai da dabara ske shiga a share musu a ba su abinci. Da mamaki take bin wasu baru su biyu dan tasan ita ce ta musu wannan shaidar, ta alamar H. Da kuɗin sa ya siyo sanda suna tara ɗan kuɗin su shida Hafiz. Ranar da ya dawo a ranar da ta je tagan su a keji kawai ta ɗauke su ta kai gidan su, wai ai shi ne ya bata koda ya gani sai be ce komai ba, shine aka sace su ranar an sha kuka bata ci abinci har washegari sai da suka tafi Islamiyya tagan su s wajen mai siyarwar ta tambaye wa ya bashi yace wani ne, ya fadi sunan sa ta faɗawa Abban su dan Baba b kula ta zai yi ba, Abban yaje ya sake siyo mata su tana zuwa kuwa, ta musu sheda da wuta ta yi jinyar su ta mayar masa sanda ta mayar ɗin yana zaune a tsakar gida yana cin abinci shida Sadiq. Tace, "Abokin Yaya ga tattabaruna ka kula min da su". A lokacin ko kallan inda take be yi ba amma kuma ya jita, kullum zata shigo ta basu abinci ta tafi.

Kallan ta kawai tayi tunowa da abinda tayi, duk sanda ya kalle su sai ya tuna lokacin, yayin da ita kuma ta wani fuske alamar oho bansan me nayi ba. Haka suka gama yawan su suka fita.

"To ya ba ɗawisu kuma".

Yanzun ma shiru yayi mata be ce mata komai ba, suna fitowa suka ga Umma ta shimfiɗa tabarma, shi wucewa yayi ɗaki itama ta bishi a baya.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now