11

20 1 0
                                    

✨ *ZAHARADDEEN* ✨

          
                   By

       *Hijjartabdoul*

 
                     11.

*****Ya jima akan ta yana kallan ta, ya rasa takamaimai mene yake ji a game da yarinyar nan, duk iskanci sa da mace iya riƙe riƙen hannu ne kawai amma ko kiss baya haɗa su da kowa, ba kuma wai ba zai yi ba kawai harkar ce baya so shide barshi a dating yarinya idan yaga tana neman wuce gona da iri kuma su rabu, ba lalle ba dole....

Ajiyar zuciya ya sauke yana zama a kusa da ita, kafin ya shafi fuskar ta, cike da tausayin ta, ganin yarda fuskar ta, ta wani irin tashi ta kumbura tayi jaa da ita, jin ana shafa mata fuska yasa ta buɗe idan ta a hankali tana kallan sa. Bata ce masa komai ba ya janyo wayar ta da tunda yau ta waye bata kalle ta ba,tama manta da wata waya ita kam. Ganin har ƙarfe biyar tayi yasa ta dirowa daga gadan cike da sauri saide rashin ƙwari jiki yasa ta kusan faɗuwa sai da ya tarota tana cewa tayi a hankali. Bata tanka masa ba ta wuce bayi, sai da ta sake gasa jikin ta da ruwa mai zafi taji dama-dama sannan ta fito, sanin cewa yana ɗakin yasa ta rufa towel biyu. Yana kwance akan gadan ya faɗa duniyar tunani, kwata-kwata ya ma rasa mene ya dace da yayi. Zancen Maryam zai ɗauka ko kuwa zancen da ƙasan zuciyar sa yake cewa kar ya ɗauka.

Har ta zo ta shirya be san tayi ba, sai da yaji ƙamshi ba turaruka sannan ya buɗe idan sa ya zuba mata su, tana kallan ta, ta shirya ta zo ta fara sallah, iya sallahr na ta ma kawai abin burgewa ga wata nutsuwa da yaga ta ƙara yi. Shide yasan ba haka yake sallahn sa ba, kawai fakawa yake yi daga ya tada zai kai, daga ya kai ruko kuwa zai ɗago. Amma ji ita yarda take yi, wani irin burge shi tayi sai ya bata dukkanin wani hankalin sa har ta idar, yanzun kam ta tayi azkhar sai ta haɗa da na yamma duka tayi. Naɗe abin sallahn tayi kawai ta  fice daga ɗakin. Shima bin bayan ta yayi ganin tana ƙoƙarin fita yasa kiran sunan ta.

"Zaki je ?

"Abinci zan ci".

Ta faɗa tana ƙara yin gaba.

"Dawo ki zauna, bari na ɗauko maki".

Ba musu ta dawo ta zauna, dan bata san ina ne Kitchen ɗin ba a gidan.

Yau anyi sa'a dukan su suna zaune, babu wanda ya fita har Hajiyar, kai tsaye dining ya wuce, ganin babu abinci ya sa shi yin hanyar Kitchen babu wanda ya lura da shi, Saboda kowa abinda ya shafe shi yake yi, a kitchen ɗin ma ba abinci dan sai sun ce suna so ake yin na dare, na rana kuma anyi har sun ci. Kiran wayar dake Kitchen yayi maid ɗin ta zo ya faɗa mata abinda zata girka sannan ya fita ya sami waje a parlour ya zauna.

"Lafiyar ka kuwa?

Cewar Hajiya, girgiza kan sa kawai yayi yana gyara zaman sa ya lumshe idan sa.

Safiyya tace, "Ita abar taka bata faɗa maka irin rama marin da nayi ba?

Daman yayi tunanin hakan, tunda yaga fuskar ta tashi. Ko buɗe idan sa be yi ba bare ta sa ran tanka mata.

Hashim yace, "Mari kuma Sofi?

"Eh mana, Bro bata da hankali just imagine ni zata haɗa jiki da ita? Wata kuca ka da ita".

"A'a sis, abinda kika be dace ba, ki dena wulaƙata mutane mana, mutane fa suna da daraja".

"Ai kaima naga kana yi".

Yace, "Duk abu na Sofi,bana taɓa marin mutum, ba kuma na wulaƙata shi, ki bar ne da rashin mutunci na shima sai na ga dama. Amma ke bansan wacce iri ba ce. Kumar matar yayan ki".

"Kuma wallahi ko kallo na ta kuma yi sai na rama".

"Zaki iya".

Daga nan be kuma cewa komai ba ya cigaba da danna wayar sa. Shi de Ɗalhat na jin su be ce da su komai ba haka Hajiya.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now