35

24 1 0
                                    

35

******Bayan an gama meeting ɗin jirgi ya hau ya dawo Abuja, sai de me? Yana zuwa yaga irin kuɗin da aka kwashe a companyn Hafiz, ya duba mana na Ɗalhat ma, shima yaga an kwashe duka kuɗin cikin sa. Gashi za'a biya ma'aikata wannan watan. Be ƙara tabbatarwa ba sai da ya hau mota yaje duka companyn ya yaga haka ne, ga ma'aikata sun tashi bare yace ko sune aka samu wani mayaudarin ya kwashe. A wani irin hargitse ya dawo gida, yana shigowa main parlour yaji Musaddiq na ihun an kwashe masa kuɗi, ya ƙaraso mana ya ji ba'a si, ita ma Safiyya ta fara ihun waye zai kwashe mata kuɗi.

"Daad kalla?

Ta faɗa tana nuna masa wayar ta, haka ma Musaddiq.

Hajiya tace, "Kamar ya kwashe kuɗi kuma ana zaune ƙalau?

"Kinga fa Mom".

Musaddiq ya koma wajen ta ya faɗa mata.

"Taya hakan zai faru?

Cewar Hajiya, yayin da A. Madaki yake a tsaye kawai, yana jimamin wannan al'amari, ashe Hashim da gaske yake, idan kuwa haka ne to yana ina?

Karɓar wayar Safiyya yayi yaga babu sunan garin da aka yi haka, tabbas wanna abun ba'a nan gida Nigeria ba ne ba, tunda su har yaushe ma transfern ta zo da za'a fara kwashe kuɗi from bank to bank. Babu makawa Hashim ne, kuma wannan ba tunanin Hashim ba ne ba, idan bana Hashim ne ba to na waye?

Wucewa kawai yayi ya shiga ɗaki, ya zauna, Safiyya ta biyo shi tana kukan taɓara.

"Yanzu Dad haka zan zauna kenan babu kuɗi a account ɗina? Kuma yau zamu fita Party da ƙawaye na".

Kawai kuɗi ya ciwo  a jikin table ɗin sa ya miƙa mata, yana jingina kan sa da jikin kujera. Sai ta Musaddiq nan ma shima kuɗin ya ɗauko ya ba shi. Hajiya ce ta shigo ɗauke da shayin sa.

"Wai yau Alhaji lafiya?

Gyara zaman sa yayi yana kallon ta tare da cswa.

"Fitar min da wannan shayin bana san shan sa".

"Yau kai ne kake cewa a fitar maka da shayin ka?

"Nace bana so fa".

Ya faɗa yana dafe kan sa dake tsananin sara masa sosai.

"Ko taron ne yau be yi maka ba yarda kake so?

"Be yi ba, ta wani wajen kuma yayi".

"Kunna min TV nan".

Ba musu ta kunna masa, ya kai channel ɗin sa, dan basa yin live sosai, saboda kada a samu matsala. Ba su fara sai ya kai wata, inda aka gama shirin ana cewa, wani company a wani can ƙauyen da ba'a sani, sune suke yin wannan abun, sai aka ɗaga yogurt ɗin da fresh milk. Abin mamakin ma sai ka sha zaka ji  daɗin dake tare da shi, biyo mu domin ziyaryar wannan company mugani zuwa jibi laraba mun gode.

"A wurin taron wannan abun ya faru?

Banza yayi da ita, shi a yanzu be wuce kuɗin sa da Hashim ya kwashe ba. Tashi yayi ya wuce ɗakin Hashim ɗin babu abinda ya suma a ciki, haka ma ɗakin Ɗalhat, babban kuskuren da yayi be wuce barmusu companyn da yayi a hannunsu ba.

"Haba Alhaji wai meye hakan kake yi ne? Ko wanne abu da ka sani, zama ake yi, ayi nazarin sa a kuma gane inda ya dosa sai a warware shi a hankali. Kar ka manta fa, kullum muke da nasara, kullum mune a gaba da komai haka zamu cigaba da tafiya".

Jinjina kan sa kawai yayi.

Musaddiq yace, "Daad kai ne ka kwashe mana kuɗin mu?

"Nayi me da su Musaddiq? Nima ban san wanda ya kwashe ba, amma zan nemo shi".

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now