10

20 1 0
                                    

*ZAHARADDEEN* ✨

          
                   By

       *Hijjartabdoul*

                 10.


*****Washegari da safe Ameerah ta jima tana kallan sa, tun da asuba take masa ya tashi yayi sallah be tashi ba har rana ta fito. Duk yarda ta so ga ƙin rashin jin ba daɗi sai da ta ji ba daɗi a ran ta. Haka de ta tashi ta sake yin wanka ta shirya tsaf abin ta. Tana kallan sa har yanzu be tashi ba, sai ta sake tashin sa, shine ya tashi yana kallan ta.

"Ko baka da lafiya?

Banza yayi da ita, yana ya wuce daga ɗakin, jiki a sanyaye ta gyara gadan tas sannan ta baɗe jikin ta da tauraru ka masu sanyin ƙamshi sannan ta fito ta zauna. Can sai ga shi ya fito ya yi wanka ya shirya, har sai shareta sai kuma ya fasa ya zo kusa da ita ya zauna yana riƙe mata hannu.

"Kin tashi lafiya?

"Alhamdulillah".

"Ya daren jiya?

Sai kawai tayi ƙasa da kan ta, bata ce komai ba, sai ya samu kan sa da murmushi yana bata side hug tare da Pecking goshin sa, shi kaɗai yasan me yake ji a jiyan nan, shi de yasan zuciyar sa ce take so ba shi ba, gashi ya rasa ta maimai abinda yake ji game da ita, duk wani shirin sa da borin sa na ƙi wannan auren sai gashi a jiyan ma tun ba'a je ko ina ba, komai ya faru.

"Lafiya?

Ta faɗa tana kallan sa, ganin kallan yaƙi ƙarewa. Murmushi yayi mata yana miƙar da ita.

"Mu je mu ci abinci".

"Ina zuwa".

Ta faɗa tana komawa, mayafin da zai shiga da kayan ta ɗauka ta yafa, sannan ta fito suka tafi. Ba ƙaramin kyau suka yi ba sanda suka fito gashi shima sai murmushi yake yi da'alama wani abun ya faɗa wanda ya sata ƴar dariya tana jin kunya. Tunda suka fito idan Hajiya yake kan su, wani ƙullutun abu na tokare mata wuya, amma haka ta yi dariyar yake har suka ƙaraso.

"Kun fito?

"Ina kwana".

Ta faɗa yana zama a ƙasa, ba kunya yasa hannu ya ɗaga ta, ta zauna a kusa da shi.

"Mom kin tashi lafiya? Ya gajiyar ki?

"Lafiya ƙalau. Ya kike?

Ta maida tambayar tana kallan Ameerah.

"Alhamdulillah".

Kawai Ameerah ta amsa mata tana mai jin ta a matuƙar takure.

"Kuje ku ci abinci".

Shine ya miƙar da ita tsaye sannan suka nufi dining ɗin. Da kan sa ya zuba mata sai jan ta yake da hira dan ba ƙarya cikin wani irin farin ciki yake jin sa. Duk yadda ta so share ta abin ba sauƙi, sai da suka gama sannan Hajiya take sanar da su Abba su na kiran su.

Yana hakimce a parlourn sa, yana kallon labarai, hannun sa kuma jarida ce yana karantawa, zuwan su yasa shi cire glass ɗin dake idan sa ya naɗe jaridar yana mai amsa mata sallamar da tayi masa. Sai da suka gaida shi sannan ya kalli Ameerah da ta zauna a ƙasa shima a ƙasan ya zauna yanzu. Shayi ya zuba mata ya miƙa mata, tasa hannu ta amsa sannan ya zubawa Ɗalhat.

"Sha mana ƴa ta".

Ɗan murmushin jin kunya tayi sannan ta ɗan sha kaɗan ta riƙe a gaban ta.

"Wani abu nake son ki min".

"Hope za ki yi min shi ?

"In sha Allah Daddy".

"Na farko".

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now