28

19 1 0
                                    

28


*****Alwashi ta ci, da cewar ba zata ƙara masa magana ba, duk abinda zai yi sai de yayi. Itama zata dawo kamar shi sanda gabza masa rashin mutunci iri-iri. Indai irin wannan abun da yake mata ne haka ya ji sanda take faɗa masa maganar da ta ga dama, to baƙaramin ƙoƙari yayi ba, tun ba'a je ko ina ba har ta gaji ba zata iya ɗauka ba. Ya yi tafiya be sanar da ita ba, zai dawo be sanar da ita ba, ya haɗu da ƴan uwan shi be faɗa mata, idan shawara ce kafin kowa ya ji ina ita zata zai fara faɗawa? Amma shine sai a bakin ƴan uwan ta zata ringa ji. Shin daman haka mace take ji idan ta ce tana san namiji? Ko kuwa nata mijin ne ke mata irin wannan gorin, kasa daurewa tayi kawai taji wani irin kuka ya kufce mata, ta shiga rera abinta.

Be taɓa tunanin zai ji kukan ta ba, kawai jin kuka yayi a sama har zai tashi ya koma ya kwanta.

Yace, "Ko kiyi shiru, ko kuma ki tattara kayan ki, ki fice min a ɗaki. Wannan ya zaman karo na ƙarshe da zan ƙara maki wani gargaɗi".

Banza tayi da shi ta cigaba da kukan ta, bata tsammata ba sai ji tayi yayi cimak da ita daga ita har bargon.

"Ka ajje ni, ina zaka kai ni".

Ta faɗa cikin kuka.

"Store zan kan ki, yarda ba zaki damu kowa ba".

Ya faɗa yana buɗe ƙofar.

"Na dena ajje ni toh. Dan Allah".

Murmushi yayi a ran sa sannan ya mayar da ita, ya ajje sannan ya buɗe fuskar ta da ta jiƙe da hawaye ya shafi fuskar ya tashi ya koma ya kwanta. Murguɗa masa baki tayi.

"Zaka sani".

"Na fi haka sani".

********Sun sake jinjinawa wannan mutanen irin karamcin da ƴar uwar ta ba ta musu ba, abinci sai da suka ture shi, sun ci sun sha abinsu sai hamdala suke yi. Ga lafiyayyen gado da aka basu. Suka yi wanka aka Kawo musu sabbin kaya suka sa sannan suka kwanta, sai da asuba aka zo aka tashe su sahur nan ma aka kawo musu abinci suka yi sahur da shi. Sai da gari yayi haske sannan Sakeenah ta zo ta ƙwanƙwasawa Anty, ta zo ta buɗe mata tace tana san ganin su. Shima ta je ta tashe shi.

Gaisawa suka yi da Abban Sakeenah da ya miƙa masa hannu suka gaisa, shi kuma zai fita, haka ma Maman Sakeenah ita ma fita zatayi.

"Yau a kotun Abbah zakiyi shari'a?

"Kema da kin zama Barrister kinga shikenan ko?

"Da har yanzu ban gama karatu ba ai".

"Sai mun dawo ki kula".

"Abba ka kula min da Mommy na".

Fita kawai suka yi suna ɗaga mata hannu ita kuma ta dawo cikin parlourn tana zama akan kujera, su de kawai tsayawa suka yi suna kallan su, wasa da dariya da iyayen ta kamar ba su ne suka haifeta ba.

"Iyayena suna so na. Kun ga Babana tsoho ko? Ya jima yana gwagwarmaya a rayuwar sa, kafin ya samu yayi aure sannan da yayi auren kuma Allah be basu haihuwa ba sai da suka jima sannan aka same ni. Shine suka ɗauki san duniya suka ɗaura min. Duk abinda nake so shi ake bani. Amma idan na yi ba daidai ba, kar ku zo kuga yarda ake bin faɗa, har duka na ana yi".

Sai tayi murmushi tana kallan su.

Tace, "Kuyi haƙuri na fiye surutu ko? Kun bani labarin ku, me yasa ni ba zan baku nawa labarin ba? To wannan shine ɗan labarina a takaice".

Shiru tayi tana kallan su cike da kulawa, kafin itama ta sauko ƙasan da suke.

Tace, "Kunga rayuwa da mai daɗi da marar daɗi. Nasan kun gane darasin rayuwa a yanzu. Kun kuma fahimci abinda Baban Fa'iz yake so ku gane ko?

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now