14

25 1 0
                                    


✨ *ZAHARADDEEN* ✨

          
                   By

       *Hijjartabdoul*

                        14.







***** Brazil Belo Horizonte.

    Universidade Federal de Minas Gerais (UFMG).

Tana zaune kamar yarda ta saba, ita kaɗai a cikin makarantar tayi isolating kan ta kamar yarda ta saba a duk sanda bata da class, sai de yau maimakon karatun da take yi tunani ta tafi tunanin da sai zata kwanta take yin shi, babu wanda ya kira yace ya zata zo gida, babu wanda ya kira ya ce mata ya hanya. Anya suna san ta kuwa?

A hankali ta ja ajiyar zuciya ganin drivern ta ya zo ɗaukan ta, tashi tayi ta tattara kayan ta ta shiga motar suka tafi. Nan ɗin ma da ta zo ba jin daɗin zaman gidan take ba. Kusan ma tarbiyyar gidan su da take ganin ta tayi ƙaranci gwara ita sau dubu akan wacce take gani muraran a gidan. Kwata-kwata bata jin daɗin zaman gidan. Shirin ta sai ya fi ya linka na da, ta tabbatar da idan tana zuwa asibiti check up to tabbas tasan bazats rasa wata cutar dake damun ta ba, ta rasa yarda zatayi da rayuwar ta sai yaushe ne komai zai yi mata daɗi?

"Maryam".

Ta ji Anty ta faɗa, wacce ta kasance ƙauwa ce ga Mom ɗin su. Tana da yara huɗu uku maza daya mace amma ita tayi aure a America sannan ɗayan ɗan nata shima yana can yana karatu sai biyu ne suke gaban ta.

"Yau da wuri kika dawo?

Ɗaga mata kai kawai tayi, tana  shigewa ɗakin ta, tana zuwa ta cire kayan ta, ga ɗaura towel zata shiga wanka aka shigo ɗakin, kulle ido tayi tana sauke ajiyar zuciya ko bata juyo ba tabbatar da Fa'iz ne ya maida ɗakin kamar wani nasa, daga ta shigo daga shima ya shigo. Tayi masa faɗan a banza ta bata ran a banza, hakan yasa ta ƙin juyowa ta cigaba da tafiya.

"Ana san magana dake".

Ya faɗa mata yana ajje wayar akan gado, batare ta juyo ba sai da ta ji fitar shi sannan ta juyo ta ɗauka wayar, bata ga sunan ba kawai a kunne ta kara wayar batare da tayi magana ba.

"Maryam".

"Bro D?

Ta faɗa cike da mamaki kafin ta kalli wayar taga shine sannan ta mayar kunnan ta, tana jin yadda numfashin sa ke fita da ƙarfi yana sauke ajiyar zuciya.

"Lafiyan ka?

Murmushin ƙarfin hali yayi mata bata bashi damar yin magana ba.

"D lafiya kake kuwa? Mene ya ke damun ka? Bro D Ameerah? Kuna tare da ita ? Bro baka cutar da ita ba? To me yake damun ka? Ko wani abu ne ya faru da ku? Wai ma Lafiya kake? Ka ji yarda kake kuwa?

Be taɓa tsintar kan sa a wani yana yi na farin ciki ba tare da ƴar uwar sa irin wannan, jin sa kawai tayi amma hankalin ta ya tashi wanda suke kallan sa ma ba su masa wannan tambayar ba sai ita da ya kira ta. Me zai ce mata a yanzu yana damun sa?

"Kayi shiru ko wani abu ne ya faru da su Daad da Mom?

"To wai ma ina Ameerah, ka kai mata wayar idan kai ba zaka yi magana ba".

"Maryam meye tarbiyya?

Cak ta tsaya tana damƙe towel ɗin ta, tare da samun waje ta zauna cike da mamakin tambayar da yayi mata.

"D lafiya?

"Please Maryam help me out".

"I should help you out like how D?

Hawayen da yake ta dannewa ne suka zubo masa be damu da ya goge ba.

Yace, "Just tell me,  meye tarbiyya".

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now