37

16 1 0
                                    

     37.

******Sanda Deeni ya koma gida, su Ɗalhat su Ishaq sun tafi, Yaya Bilki ta so tafiya da Maryam amma Ishaq ya lallaɓata akan tayi haƙuri, suma suna san kasancewa da ƴar uwar su, idan ta kwana biyu sai su zo su tafi da ita. Hakan kuwa aka yi ta yarda ta zauna, su Ɗalhat suka tafi suka rabu da ita a nan, duk sai Halima ta ji ba daɗi, ganin irin sabon da suke yiwa junan su. Hakan yasa Zarah tace da daddare za su kawo ta, hakan yasa Ɗalhat yadda ya rabu da ita har Ɗalha shima, suka tafi cike da murna da kuma irin alhinin da wannan bawan Allah yayi musu.

Suna zaune a waje suna hiran su cike da farin ciki da annashwa, ji suke rayuwar su ta gama kammala saboda wannan farin cikin da suke so, haka su Ummu suka dawo daga makaranta suka same su, haka suka zauna tare da su ko uniform basu cire ba suma. Halima sai labarin haushin da suke bata take yi suna dariya. Hafsah ce ta fito itama dan ta sha iska ta gan su suna zaunen suna hira, zatayi magana kenan, taga Deeni ya fito ya buɗe gate ya koma, Taufiq yaje ya tsaya a bakin gate ɗin sai da ya shigo sannan ya rufe ya bishi yana masa sannu da zuwa kayan hannun sa kawai ya amsa ya kai ciki sannan ya dawo, kowa sai sannu da zuwa yake masa.

"Ya dai?

Ya faɗa yana kallon, Hafsah da ta zuba masa ido tana kallan sa. Haɗe rai tayi tana neman waje ta zauna, shima kusa da ita ya samu ya zauna.

"Ina Sabir?

"Yaya Deeni ne yace mana a gidan su Najma zai kwana".

"Wanne irin magana ne wannan ɗin? Gobe fa da school kuma yaje gidan mutane ya kwana?

Shiru suka yi, babu wanda ya tanka mata.

"Dan uwarku ba magana nake maku ba?

"To Dan Allah Anty Yaya Deeni ne fa yace mana haka".

Cewar Taufiq, ba tsammi kuwa ta buge masa baki da wayar ta.

"Ni kake faɗawa wannan maganar?

Shiru yayi mata yana ɗan ja baya dan kada kuma ta kawo masa duka.

"Ke kuma dan Kut****ki da kika zo kika shanya yarinyar a waje? Kin tashi kin wuce ko kuwa?

Ba musu Ameerah ta tashi ta karɓe ta a hannun Zarah ta wuce.  Hannun ta ji an riƙe hakan yasa ta kallan Deeni da yayi kamar be san abinda yayi ba. Sannan ya tashe ta tsaye suka wuce ciki. Ajiyar zuciya Maryam da Halima suka saki a tare yayin da Taufiq yace.

"Irin wannan ajiyar zuciya haka?

"Ba zaka gane ba".

Cewar Halima.

Tace, "Ni wallahi wannan yayar taku ce zata hanani sakewa a gidan nan, ku kan ku tsoron ta kuke ji. Ina ga mu kuma".

Maryam tace, "Ke kina da bakin tsarawa ma".

Zarah tace, "Muma ku tashi mu wuce ciki".

Za su tashi kenan, suka ji horn ɗin Hafiz, Taufiq yaje ya buɗe masa, Maryam kallan Hashim kawai ta tsaya yi ganin haka sai suka tsaya suma basu tafi ba, har suka fito suna nan, sai da suka zo daf da su. Maryam tace.

"Bro H?

Ta faɗa cike da mamaki, shi kan sa mamakin ganin ta yayi sai kuma ya tuna da labarin da Deeni ya bashi tuni ya ture duk wani mamaki da yake yi, ya ƙarasa wajen ta cike da kewar ta da be taɓa tunanin yi ba sai a yanzu da ya ganta. Ƙwallar da ke idan ta kawai ya isa ya sanar da shi yarda tayi kewarsa, sun ta so cikin gida ɗaya,babu wani sabo a tsakanin su, maganar dake haɗa su kawai gaisuwa ce sai kuma idan ba suyi ba daidai ba tayi musu magana, wanda tun tana yi har ta dena yi musu. Suka koma kallan kallo. Amma duk da hakan kuwa sun yi wani irin sabo da junansu domin kuwa naka sai naka.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now