46

19 1 0
                                    

46

********Gaba ɗaya parlour kowa shiru yayi yana kallan Proff. Tahir. Kowa da abinda yake saƙawa a ran sa yayin da shi kuma yake jin kukan da ƴar sa ke yi har cikin ran sa, kafin ta tashi ta wuce ɗaki dan sautin kukan ta kawai ke tashi a parlourn. Oga Ajiya kuwa shiru yayi, ko da ace a mafarki ake be taɓa tunanin cewa Proff zai aikata haka ba. Idan kuwa aka ce masa Major Kabir zai aikata to tabbas zai yarda, saboda Major Kabir irin yaran nan da suka ta so cikin rigima ba ruwan sa duk wanda ya masa dukan sa yake yi, ga zafin zuciya da yake da shi. Hakan yasa basa wani ƙara jituwa. A yanzu kuma gashi ya san komai shekara da shekaru amma be yi magana ba akai har sai da yayi kuskuren shiga gonar sa ya taɓa masa yaran da da'alama yake matuƙar ƙaunar su da san su. Gefe ɗaya kuma wani irin son su Sadiq ya ji yana yi dan da dukkan alama yaron akwai wadattaccen tarbiyya da ilimi. Tafiyar sa ma kawai abin burgewa ce bare kuma da ya buɗe baki ya gaida shi cikin girmamawa mai tarin yawa. ( Wai dan ma bega Deeni ba ).....

A hankali ya ringa jin ƙananan magana suna tashi a parlourn ana neman watsewa, dakatar da su yaji ta hanyar cewa me suke magana akai? Kowa shiru yayi bece komai ba, sai da yace babu wanda zai fita har sai sun sanar da shi ƙusƙus ɗin me suke, anan fa kowa ya fara warware irin zaman da yake yi a gidan sa da matar sa na haƙuri da juriya. Matan kuma suke sanar da irin abubuwan da mizajen ke masu, wasu ma har an sake su amma saboda tsoron sa ya sa kowa yayi shiru be faɗa ba. Sai yau da ya titsiye su ganin kamar suna da abn faɗa ba. Nan fa ƴan parlourn kowa ya fara cewa shi baza'a masa irin wannan auren ba. Daman dukkan su wanda yayi ɗin jikokin ne. Abinda yake bashi mamaki be wuce jin cewa wai Major Kabir ke taimakon su ba da wasu abubuwan na rayuwa, Major Kabir ɗin da ya fi nesa da su amma shine yasan wasu abubuwan na buƙatar rayuwar su.

"Ajiya abin nan ya tsaya iya nan. Ka bari ka ci zamanin ka, ka ci na Iyayen mu yanzu kuma ba zaka ci na mu ba gaskiya abin ya tsaya haka".

Cewar wann matashi da ko kawowa a fara maganar auren sa be yi ba, ya faɗa yana miƙewa da ficewa, bece da su komai ba dan bashi da abun faɗa, ya sallame su. Shima Proff Sallamar sa yayi, dan rashin maganar Ajiya watarana tana ɗaya daga cikin hukunci ne mai tsanani zai biyo baya. Yana tashi ya ce a kira masa Ishaq kamar yadda suka saba gaisawa Ishaq ya gaida shi, batare da ya nuna masa komai ba.

"Kayi haƙuri Ishaq".

Sai Ishaq yayi murmushi yana ɗan sosa gefen wuyan sa. Da mamaki yake kallon yaron sak irin sa yadda yake yi idan abu be masa ba. Amma duk kular da yake yi da shi be taɓa ganin hakan ba sai a yau.

"Uncle Proff me ya faru?

"Dan Allah Ishaq ka bari, mu fuskanci gaban mu, kayi haƙuri komai ya wuce, ka dawo gidana da zama".

Murmushi Ishaq yayi yana sakin murmushi.

Yace, "Ai ni uncle ba ɗan ka ba ne ba, yaron ka, ka riga da yar da shi, ka jefar da shi Uncle. Ni a yanzu iyaye na sun rasu, Abba ni kuma wanda ya ɗauki kula da ni. Kai kawai haifa ta kayi kuma ka yarda ni".

"Ka ɗauka cewar baka san inda wanda ka jefar ba yake, amma tabbas ni matacce a rayuwar ka".

Sai yayi murmushi yana miƙewa tsaye.

"Ka saurari kalamaina hakan suke, wanda ya mutu kuma baya taɓa dawowa".

Daga haka zai wuce yayi saurin riƙo shi yana kuka.

"Dan Allah Ishaq kar ka min haka, kai ɗa na ne Ishaq".

Girgiza kan sa Ishaq ɗin yayi yana ƙoƙarin maida ƙwallar dake shirin zubo masa ta hanyar dariya kadan.

"Sa'a ɗaya ka ke ci ta mahaifi a waje na, tunda ba zan sauyawa tuwo suna ba, amma da tuni da jima da kwashe ka da maruka, ka barni the way  am I".

Ya ƙwace hannun sa.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now