27

17 1 0
                                    

27

*****Tun sanda suka gama waya da Hashim yake riƙe da wayar a hannu, kafin ya danna kiran Paa sai de layin a kashe yake, duka layin sa na Brazil ya kira amma a kashe, be da numbern Antyn na su sai kadai ya ya fito ya nufi main parlour. Su Safiyya suna kwance yanzu an dena fita yawo sai azumi kuma ya wuce, sai de tana kwance tana kallo haka ma Musaddiq wai azumi wahala. Hajiyar su ya kalla.

Yace, "Kira min Saratu".

"Lafiya?

Ta faɗa tana nemo numbern ta, sai de itama a kashe.

"Me ya faru?.

"Tabbas wani ya faru".

Ya faɗa yana zama a gefen ta.

"To meye ne ya farun?

"Baki da numbern kowa a gidan?

Numbern Akram ta kira, itama a kashe, haka ma numbern Yayar su ta America.

"Kira min Maryam".

"Maryam ai tunda ta tafi ba mu nema ta ba".

"Shi yasa matsalar ta faru ai".

Ya faɗa yana tashi da komawa part ɗin sa, haka ya ringa kiran waya yana cewa a nemo masa numbern Paa, ta Nigeria hankalin sa be kwanta ba har sai da aka nemo masa ɗin. Ya kira shi amma be ɗaga ba. Daga karshe ya ɗaga.

"Ina Maryam? Ina ƴa ta Maryam".

Dariya ya ji Paa nayi, cike da mamakin ƙarfin hali irin wannan mutumin wai ina Maryam. Ba gaisuwa bakomai,babu ya ibada.

"Ya kake min wannan tambayar? Bayan nine ya dace nayi maka ita?

"Bangane ba?

"Maryam tun yaushe ta dawo wajen ka? Nima ko sallama bata min ba ta tafi".

"Kana so ka ce Maryam ta dawo gida? Nigeria? Abuja?

"Kai kana so ka ce min Maryam bata dawo gida ba? Nigeria? Abuja?

Kan sa gaba ɗaya ya ƙulle, kafin Paa yace, "Maryam ta sami matsala da Fa'iz hakan yasa ta rikicewa ta taho, dana bincika sai naga ashe nan ɗin ta dawo shiyasa ban tashi hankali na ba".

Kashe wayar sa kawai Paa yayi yana jin wani irin abu, to ina Maryam? Ina Ɗalhat? Shi damuwar sa a yanzu be wuce yarda zai yi da jama'a ba, idan aka ɗauki tsawon lokaci ba su dawo gare shi ba. Tabbas Hashim ya san wani abu akai shiyasa ya kira shi. Kiran sa ya ringa yi ana ce masa busy, lokacin shi kuma yana waya da Jalal. Fitowa ya sake yi ya tarar da Hajiya na waje, wai wata mata sun zo sun hanata shiga securities ɗin shine aka kira ta domin ta je ta gan ta ko ta san ta, hakan yasa shi ma bin bayan Hajiyar.

"Saratu?

Ta faɗa da mamaki tana kallon ta, duk ta koma wani iri kalar tausayi. Haka de, yayin da shi kuma Fa'iz yake baza ido yana washe baki na ganin cewar ya zo gidan hutu.

"Me ya kawo ki nan? Lafiyar ki kuwa? Ina mijin naki".

"Ke de Yaya mu shiga daga ciki mana".

"Wanne irin mu shiga daga ciki, ina kallan ki wani iri da ke, zaki ce min mun shiga daga ciki? Idan mun shiga daga ciki me zaki min, ko me zan yi maki".

"Amma Yaya kya bari ki ji abinda ya faru ko?

Alhaji ne ya matso yace ta shigo da ita mana. Hakan yasa ta shigowa, duk su Safiyya miƙewa suka yi suna kallon su, ganin yarda Antyn su ta koma daga ƴar gayu zuwa tsumma, duk kayan jikin ta sun yi wani iri da su.

"Ina Maryam take?

Cewar Fa'iz.

Hajiya tace,"Kamar ya ina Maryam?

ZARAHADDEEN Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang