26.

22 1 0
                                    

                 26

*****Bayan sun sha ruwa ya tara su ya sanar da su komai game da abinda ya je yi da kuma abinda ya tarar acan, dukan su sun yi na'am da wannan zancen.

"Yanzu nake ganin zamu buɗe gidan abinci bayan azumin nan, a kusa da su Sadiq".

Ameer yace, "Shikenan gani ga Hajja na je nake cin abinci a wurin".

Ya faɗa yana kallon Hajja. Tace, "Ba wanda zai ci min abinci sai ya bani kuɗi".

Gwaggo tace, "Wannan haka yake, daman ba su san mutum bama bare ya nuna ya san mu".

"Ni daman Gwaggo na lura bakya so na, tunda kika zo gidan nan kike ware ni wai ni ba ɗan gidan ba ne ba".

"To da maraba".

"Ameer".

Deeni ya kira shi, alamar ya takura masa. Yace, "Kai idan ana magana sai kake kawo wata maganar ko?

"Na dena".

"Uhm".

Kawai yace masa, kafin ya kalli Hafiz yace, "Bana jin muna da buƙatar ka a wajen domin kujewa idan mutane dole zaka dena zuwan wajen nan".

"Wai Deeni dan Allah ka fito ka sanar da mu me kake nufi game da duk wannan abunda kake samu yi. Deeni kawai zuba maka ido nayi ina kallan ka, gwara ka sanar da ni tun da wuri kafin mu zo mu samu saɓani da kai".

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallan sa, tare da sakar masa murmushi, so yake yaga ranar da shi ko Hafiz ɗin za su iya samun matsala, amma yasan ba za su taɓa domin kuwa kowa ya iya zaman da kowa, shi kan sa Hafiz ɗin baya da faɗa akan mutane sai akan ƙannan sa suma sai sun yi laifin da zai tsawatar musu ne, amma haka kawai bashi da faɗa, gani yake bazai taɓa yin faɗa da shi ba.

"Kayi shiru, nima ina san ji".

Cewar Hajja. Su de su Ameer shiru suka yi kawai ba su ce komai ba.

"Akwai lokaci".

Ya faɗa yana murmushi kawai, tare da cewar su ta so kar su rasa Sallah.

******Gaba ɗaya yau bata samu ta huta ba, ta rasa wanne iri abu take ji game da Deeni, haushi ko takaici tasan duk iya shegen ta tana jin tsoron mutunen da ya lissafa musamman ma Hafiz da ta rasa me tayi masa, a da yakan kira ta suyi hira mai tsayi amma yanzu kam, tunda ya mare ta ranar nan batare da ta san me ta aikata ba be sake mata magana ba, ko gaida shi tayi ma a takaice yake amsawa. Haka ita ma Umma take yi mata sun ɗauke mata wuta sosai, bare yanzu idan suka ji irin abinda ta ringa masa bata san me za su yi mata ba.

Juyi ta sake yi ta kwanta, ta rufe idan ta, tana jin wani irin zazzaɓi na kamata na murar da take, wanda daman tana yi da azumi indai ta sha ruwan sanyi sosai, bare wannan azumin da take jin ba kamar a Abuja ba da kusan kullum sai anyi ruwa, amma anan an yi ruwan ma rana ake yi. Tunanin ina ya tsaya kuma ta fara yi ganin tunda ya fita Tarawi be dawo ba, ita de ba damuwar ta ba ce. Bata wani jima ba bacci ya kwashe ta, dan ta gaji yanzu ne ta samu ta kwanta tunda garin Allah ya waye. Baccin ta ya fara daɗi kenan tana jan majina cikin baccin sai ya zamana kamar mun shari take yi. Ya jima a tsaye akan ta yana kallan ta, sai ya ga kamar tayi haske ta ƙara masa kyau a idan sa. Tsugunna yayi dai-dai fuskar ta yana kallan ta, ya kai hannu ya shafa fuskar cike da wannan kulawar ta sa. Sannan ya tashi ya shiga wanka, vibrating ɗin da wayar sa ke yi ne ya tashe ta lokacin shi kuma ya gama sharyawa.

"Ana kiran ka".

Ta faɗa da muryar dake nuna tana jin jiki.

"Ni zan zo na karɓa?

Ya faɗa yana kallan ta cikin mirrorn dan ta mayar da ɗakin yarda yake a da. Sai da ta zuba masa harara sannan ta ta so ta ɗauko masa lokacin har ta katse an sake kira. Miƙa masa tayi ya tsaya yana kallan ta yarda ta riƙe ƙugu ta juyar da kai ta miƙo masa wayar ne ya bashi dariya. Har zai sa hannu ya amsa.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now