42.

16 1 0
                                    

42

*******A. Madaki wani irin farin ciki da shauƙi yake ciki. Ya tabbatar da cewar a yanzu komai nasa zai zo da sauƙi tunda Deeni ne yake masu komai, yanzu kuma an kame shi sai yaga waje wannan mahaluƙin da ya isa ya cigaba da gudunar da Z products ɗin da a kullum yake bunƙasa.

Shi kaɗai ne mutumin da ya taɓa hana shi bacci, ya sa masa ciwon kai, ya yi tunanin, shine wannan mutumin de da ya zo ya zautar da shi amma sai de babu wanda ya isa yayi nasara idan ba shi ba. A yanzu yana jin zuciyarsa ta gama ƙeƙeshewar da zai iya yin komai ma meye idan aka taɓa masa dukiyar sa ciki kuwa harda kisa akai. Baya ji baya gani fatan sa kawai yayi nasara, nasarar da zata kawo shi wann matakin da zai je jin sa a gajimare, so yake ya doke kowa da kowa. Idan da zai zama mai kuɗin duk duniya ma da yafi kowa farin ciki.

Yana zaune yana shan shayin sa da ya ɗan jima be sha ba, yana kada cup ɗin yana murmushi idan sa akan TV yana kallon labarai ƙasashe, kawai tunanin yarda zai sake ɓullowa da lamarin yake yi. Babu zance a bi komai a sannu a wannan lokacin kuma. Wayar sa da tayi ƙara ne yasa shi ɗagawa batare da yayi magana ba. Da saurin ya ajje wayar ya tashi ya shiga ya shirya a gurguje dan yana da meeting a daren nan  a cikin gidan sa, haka yasa shi fita ta main parlour, yaga Hajiya na zaune tana kallo ita kaɗai.

"Zan shiga meeting idan anjima a kai mana abinci".

Ya faɗa wucewa, da kallo kawai ta bishi tana hango tsantsan farin cikin da yake ciki, kamar ba jiya jiyan ya gama ɗaga mata hankali ba, sai gashi yanzu yana fara'a. 'yanzu haka wata cutar yayi'. Ta faɗa a ran ta tana tashi.

Yana shiga yaga duk fuskar mutanen a haɗe tamau, sai yayi dariya yana samun waje ya zauna.

"Ba zama ne ya kawo mu ba,wata biyu kenan da jin labarin cewar ka rufe companyn guda na biyu, wanda kuɗin mu ke ciki. Shine muka haɗu dukka wanda muke da share a cikin companyn muka ce zamu karɓe share ɗin mu, a bamu kuɗin mu".

Sanda zai rufe companyn nan kwata kwata be yi tunanin hakan zata faru da shi ba, da tuntuni ya cire musu kuɗin su ya ba su, amma ta ina zai basu ɗin bayan kuma an rufe account ɗin companyn? Dafe goshin sa yayi da yaji lokaci ya sara masa wani sabon ciwon kan na so ya taso masa.

"Ba zai iyu muke zama ba, babu wan babu ƙanin, dole a bamu kuɗin mu".

Cewar wani shima.

"Kuyi haƙuri abinda zamu yi shine, ku zo mu haɗa hannu, mu koma ɗayan companyn inaga hakan zai fi sai a cigaba da baku".

"A'a nide kuɗi na nake so, ina da buƙatar da zan je wani companyn ko na fara wani business ɗin da shi, babu company kenan a maido mana da kuɗin mu?

"Wataƙila ma cinye mana kuɗi kayi, Shiyasa aka rufe companyn, to ba zai iyu ba. Ka kira mana Hashim wanda da shi aka yi deal ɗin komai".

"Gaskiya ne wannan".

Shiru yayi musu yana kallan su, wai ya kira musu Hashim? To shi ina zai ga wani Hashim da Ɗalhat? Yaran nan sun sha a masifa. Ajiyar zuciya ya sauke, yana kallan su suna masifa, su biyar ne har shi na shida, dukan su babu wanda be yi magana ba sai guda ɗaya mai wani company dake Kaduna.

Yace, "Ni share ɗin da ka zuba a companyn Mahaifina nake so na dawo maka da abin ka, domin naga idan tafiya tayi tafiya, jari yayi ƙasa babu kuɗin da za'a baka, a deal ɗin naga cewar za'a bar maka companyn, ni kuma gaskiya ina san company, nima ina so na gina kai na da ƴan uwana, Family business zamu haɗa. Hakan yasa nayi tattaki na zo domin maida maka da duk wani abu da aka sa".

"Me kake nufi kenan? Dole companyn za'a bani, bamuyi haka ba da shi Mahaifin naka".

A. Madaki ya faɗa ran sa ya fara ɓaci jin wani sabon batun.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now