30

18 1 0
                                    

30

*******Washegari da sassafe ta shirya ko sani be yi ba dan ta riga shi tashi. Tare da su Sabir suka wuce, yayin da su Ummu suka biyo ta primary section dan ba'a haɗe su ke ba, primary daban haka ma Secondry. Hakan yasa suka biyo ta dan su gane wa idan su, suna zuwa suka ga wata itama masifaffiyar an daki ƴar ta.

"Ke ma baiwar Allah zuwa kika yi?

Cewar matar dake riƙe da wata yarinya sa'ar Sabir.

"Ehh kema haka?

Cewar Hafsah.

"Ehh zuwa nayi, ayi ta ta ƙare na ɗauke ƴa ta daga wannan makarantar, naƙuda nayi na haihu banga dalilin da zai sa a yiwa ƴa ta wannan dukan ba".

Hafsah tace, "Nima abinda nagani kenan, duba ki ga fa?

Cewar Hafsah tana nuna mata wuyan Sabir. Itama mini hijab ɗin dake jikin yarinyar ta nuna mata.

Tace, "Duba ki fa".

"Ba'a kyautawa sam ai".

Suna nan a tsaye sai ga Headmistress  ɗin nan ta zo. Da sauri ta zo inda suke tana tarbar su da cewar su yi haƙurin lattin da tayi tare da ce musu su shigo.

"Ba zama muka zo yi ba. Mun zo ji dalilin da yasa ake dukar mana yara".

Cewar Hafsah tana matso da Sabir jikin ta, yayin da Sabir aka yi kalar tausayi. Headmistress ɗin tace.

"Kuyi haƙuri ku shigo mu zauna, ayi magana".

"Kut****magana zamuyi ba magana ba, Malamar da tayi wannan dukan nake so na gani na ci Kut******ta, tunda ba ita ta haifa min yaron ba da zata ke dukan su".

Ummu da Taufiq kallan juna suka yi, kai ka ace ita ce ta haife shi, yayin da wannan matar ta zubawa Hafsah ido, tabbas ta ga wacce ta fi ta masifa da jaraba a duniyar nan.

"Ai b**** ce zai sa ake dukar mana yara".

Ta sake faɗa tana riƙe ƙugu. Yayin da Headmistress ɗin take bawa Hafsah haƙuri. Ganin tana ɓata mata lokaci, yasa ta kallan agogon ta, tasan yanzu de kowa ma waye ya zo. Kallan Ummu tayi.

Tace, "Wuce mu je ki nuna min Antyn ajin na su na ci kan uwar ta".

"Madam kiyi haƙuri don Allah don Annabi. Zamu doba ba zai sake faruwa ba".

Tayi Hausar ta alamar inyamura ce.

"Nifa ki dena bani haƙuri, kina ɓatawa kan ki lokaci...."

"Kinga Antyn nan".

Cewar Sabir yana sake ɓuya a bayan ta.

"Don Allah mu shiga daga ciki".

Cewar shugabar makarantar haɗe rai Hafsah tayi, tana sakin hannun Sabir suka shiga office ɗin ta, yaran kuma a waje itama matar sai ta bi su a baya. Suna shiga Hafsah ta kifawa Malamar mari. Daga Headmistress ɗin har Maman yarinyar tsayawa suka yi cike da mamaki suna kallan Hafsah.

"Me ɗana ya yi da kika mare shi?

"Amma kyatsaya ki ji me yayi ko?

Ta faɗa tana dafe kuncin ta.

"Shi yasa yanzu na tambaya". Itama ta  faɗa tana harɗe hannun ta yayin da ta kafe ta da ido tana ƙara matsowa daf da ita.

"Ya dace ki mare ni?

"Shi yasa na mare ki ba'a gaban ɗaliban ki, kada na zubar maki da mutunci. Da ban mare ki zuciya ta ba zatayi sanyin abinda kika wa ɗa na ba".

"To wallahi ƴan sanda ne za su raba ni da ke. Kin san waye ce ni?

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now