31

21 1 0
                                    

31

******Washegari yace za su tafi saboda zai je Anadyr jibi. Kawu Isubu yace kwana ɗaya gaskiya ta musu kaɗan, yace shi ya tafi ya bar musu su  Ameer, dan yaran akwai shiga rai. Ga shi ba ruwan su, musamman ta wajen abinci komai aka kawo musu ci suke babu tsarabar abinci ba komai, ruwa ma da yasa aka siyo musu pure leda leda, ko ɗaya babu wanda ya sha randa suka ringa buɗewa suna shan abinsu, kwata-kwata ba su nuna ƙyamar su ba. Abin ya yi musu daɗi ba kaɗan ba su kan su matan gidan matan su Kawu Isubu da Kawu Bala sun ji daɗin hakan matuƙa dan sun san sune suka tafka kuskuren da ba zai gyaru ba a lokacin da ba sa garin. Ƙiri suke hana mazanje su zuwa wai ba abinda za su je su ɗauko a ƙauye, sai gashi suma na su ƴaƴan sun tafi sun bar su ba da ziyartar su. Ba kuma wai kuɗi ko abin duniya za su ba su ba, dan suna da arzikin su dai-dai da gwargwadon da ba su nema sun rasa ba. Hasalima har kyautar wa suke, amma ka zo a gan ka ma ai daɗi ne da shi.

Washegari suka  haɗa kayan su, suma wannan kwana ɗaya nan ba ƙaramin daɗi yayi musu ba, sai murna suke yi ganin yarda kowa ke hada-hada da su ake yin nan nan da su, ga wani irin tattali da ake bawa Ameerah ganin tana dauke da juna biyu, aka ringa mai take so, yayin da ita kawai girkin yayar ta take so, amma haka ta daure ta ce musu komai ma, da aka kawo mata Ɗanmalele kuwa ta zage ta ci yayi mata daɗi a baki haka wainar filawa mai manja. Da za su tafi kuwa har ayi mata aka yi aka bata.

Mazan ne suka biya company  dan ƙara dubawa dakyau kafin su tafi, suka ga wani mutum na jiran su, yana ganin su ya ta so, suka gaisa cike da mutuntawa. Yake ce musu shifa wannan abin da aka bashi jiya be ishe shi ba da kuma wanda ya siya sai mutum ɗaya biyu aka yi.

Ameer da baya shiru yace, "Gidan marayu ka kai?

Sosai abin ya bawa mutumin dariya yace, "Wanne marayu kuma? Gidana de gidana".

"Kuma duk aka shanye naga Boot aka cika maka".

"Ina da iyali da yawa ai".

"Duka yaran ka ne? Matan ka hudu?

Dariya Ameer ya bashi yace, "Ehh mata na hudu, yarana hamsin da shida".

Ba Ameer da ake faɗawa ba, har Deeni sai da ya sake kallan sa bare su Taufiq da suka hangame baki suna kallan sa. Ameer kada haƙuri yayi yace.

"Kuma duka ka san su? Yaran naka?

"Nifa na haife su, ba zan san su ba".

"Nufina kowa ka gani kasan ya yake, kasan halin shi, kuma gida daya suke?

"Ya sunan ka nikam?

Cewar mutumin da'alama de babu ruwan sa da wani ne ai ba zai tsaya yana masa bayani ba.

"Zaid. Amma Ameer ake ce min".

"Zaidu zaka ce min, ina da Zaidu, ina da Ameer kuma yarda kake ɗin nan haka suma suke".

"Yauwa, wurin sa suna fa".

"Babu sunan da babu".

"Akwai Ziyada?

"Akwai mana".

"Sunan Ameerah ta ce".

"Zaid da Ziyada zan so itama nagan ta naga haka take?

"Laaa ina ruwan dunkum ni ba ruwana".

Taufiq yace, "Kuma suna aiki?

Kallan Deeni yayi da da'alam wata maganar suke mai muhimmancin da yasa ba su masa magana ba, suna daga gefe abin su, shima mutumin gajiya yayi ya samu kujera ya zauna suma su Taufiq suka nemo suka zauna.

Yace, "Me zan maku ne?

"Labarin gidan ka zaka cigaba da ba mu".

Murmushi yayi musu.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now