12

20 1 0
                                    

✨ *ZAHARADDEEN* ✨

          
                   By

       *Hijjartabdoul*

                     12.

******Kawai kallan sa Abban su yake yi yana mamakin Ɗalhat ɗin, gaba ɗaya ya sauya fiye a cikin seconds kamar ba wanda suka sani ba, idan sa yayi jajur jijiyar kan sa ta fito raɗau. Yayin da Hajiya suka yi carko carko suna ganin sarautar Allah.

"Faɗa mata".

Ɗalhat ya faɗa yana kallan Abban su tare da nuna Ameerah.

"Ka faɗa mata cewar kai ta zo yiwa aiki a cikin gidan nan ba wani ba. Aikin ka take ba aikin wani ba".

"Duba fuskar ta, kalli kaga yarda suka sauya mata kamanni akan me? Dame zata ji? Da izayar ka zata ji ko da su?

"Ina so daga yau ka sanar da su cewar, aikin ka, zaman ka take, ba su babu musu kallan banza, babu su babu muzguna mata".

"Idan ma baka sanar da su ba, to tabbas ni zan musu da yaren da za su gane".

Safiyya ce ta so da ƙafar ta da ga bugu. Tana kuka sosai kamar wanda aka cire ƙafar.

"Yanzu Bro D akan wannan abar kake aibata ni...

Tas! Ya ɗauke ta da wani irin mari na bayan bannu mai shegen zafi, gashi daman a zuciye yake ga marin unexpected ne bata zata ba taji shi. Gigicewa tayi tana rasa inda zata sa kan ta dan azaba sai da Hajiyar su ta tare ta. Ta rungume tana rarrashin ta.

Hajiya tace, "Baka da hankali ne?

"Bangama magana ta ba".

Ya daka mata tsawa musu tsawa yana nuna su da hannu, Ameerah kam kulle idan ta tayi gam hawaye na cigaba da zubar mata. Ya janyo ta jikin sa yana bata side hug irin da ƙarfin nan.

Yace, "Kuma daga yanzu duk wanda ya sake ko da mata kallan banza ne, to tabbas uwar sa zata haifi wani".

"Ɗalhat ina Mahaifiyar zaka wulaƙata ni? Zaka ɗaga min murya.?

Hajiya ta faɗa tana wani tsuke fuska irin abin ya ci ta rai ɗin nan.

Yace, "Mahaifiya kika ki kan shi da shi? Kuma mahaifiyar ma tawa?

Sai yayi dariyan takaici ya matso daf da ita.

"Bana jin kin haife ni, kin haifi wanda kika haifa de amma bani".

Zata kuma magana ya ɗaga hannu itama zai mare ta.

"Ɗalhatu".

Abban su ya kira shi a zafafe, yayin da Hajiya da ƴar ta suka rungume junan su gam, har ga Allah ta zaci marin nata zai yi, jin shiru yasa ta buɗe idan nata. Sai gani tayi ta yaja Ameerah sun fita. Akan gado ya wurga ta kamar wani kayan wanki shi kuma ya zauna a baƙin gado yana dage kan sa, duka zuciyar sa ba daɗi yake ji ya rasa  me yake ji a rayuwar sa daga shekaran jiya zuwa yau. Ameerah kuwa kuka take harda shassheka sai da tayi mai isar sa sannan ta share hawayen ta ba dan ta gaji da kukan ba sai dan tana ji zata illata kan ta. Ba dan ace kisan kai babu laifi ne ba babba da a yanzun nan zata kashe kan ta komawa ya huta. Ace tun da ta zo babu kwanciyar hankali, yanzu kam ta gane dalilin da yasa Anty take faɗar maganar da take faɗa. Sulalewa tayi ta kwanta a wurin daga haka bacci ya kwashe ta.

Sai da ya ji nutsuwa na zuwar masa kafin ya fita a ɗakin, ya je ya sake wanka ya fice daga gidan, rasa inda zai je yayi sai kawai ya fara yawo a gari daga nan yayi nan haka ya wuni yana yi ba sallah bare salati. Sai can magrib ya sami wani masallaci yaje ya faka sallolin sa.

*****Ga ɗayan su fitowa suka yi domin rakiyar su, sai suke jin babu daɗi ko kaɗan kwanankin da suka kwashe suna tare, shi kan sa Baba ba daɗi yake ji duk da cewar sai dare yake dawowa amma a weekends ɗin da suka kwashe su ci tare a zauna ayi hira sai yake ji ba daɗi kwata-kwata.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now