36

23 1 0
                                    

******Gaba ɗayan su ba ƙaramin mamakin ta suka yi ba, gashi de suna kallo aka cinnawa takardar wuta kafin sun karkaɗe ta ƙone sai ɗan map ɗin companyn na su na can ne kawai be ƙone ba. Ba su taɓa tunanin ko tsammin cewar ba original ne ba, kuma ga dukkan alamu original ɗin ta ƙona.

"Daman nace gwara duk mu rasa ai, kuma gashi mun rasa".

"Yanzu abinda kika yi kin yi dai-dai kenan?

Cewar kawun Aisha.

"Ku abinda kuka yi kun dai-dai kenan?

Ta mayar masa da amsar sa tana barin wajen tare da nufar inda ta saƙale wannan takardun na su na resigning,ta ajje musu akan table ɗin tare da juyawa shi har ya zagayo wurin Director.

Tace, "Mun ajje aiki".

Daga haka ta fara tattare kayan su, yayin da Deeni ya tsaya yana kallan ta kawai, yasan zata iya yin abinda ya fi haka ma, indai ita ce.

"Yanzu kai baka ji kunya ba ace mace ke juya ka? Mace ce zata sa ka bar aiki?

Cewar Kawun Aisha. Yayin da ɗaya daga cikin Directorn. Yace.

"Gaskiya de kam, asara da  kunya sun tabbata akan ka. Kuma idan ka ajje aikin ku ci me? Me zaka nemo muku kuke ci, kuna ciyar da junan ku?

Tace, "Sanda kuka so korar mu kun yi tunanin me za mu ci muke ciyar da junan mu?

Ta kafe su da ido tana zabga musu harara, kowa shiru yayi dan ta fi su gaskiya kam. Gashi nan ba su kore su ba, su sun kore kan su da kan su.

"Idan kuma asara da kunya kuke faɗa wannan kuma personal issue ne, bana ji ya shafe ku".

"Muje ko?

Ta faɗa tana kallan Deeni harda su riƙe hannun sa, alamar tare da kai zan fita.  Haka suka tsaya suka ga ikon Allah, Deeni ya bita zugum zugum suka fice daga wajen. Sai da suka je har wurin zaman ta kafin ta saki hannun sa tana zama, tana zabgawa Aisha da ta Zainab harara dagaske haushin su take ji, ta kuma rasa dalilin yin haka. Shi kuwa Deeni duk wani files masu amfani ya tattara ya kwashe ya kai mota a wurin motar ya ganta ta jingina da jikin motar, tsabar haushi da takaici kamar ta fashe take ji. Allah ne kaɗai yasan yarda wannan shirun nasa yake ƙuntata mata.

"Fisabilillahi haka zaka zauna a rayuwar ka?

Ta faɗa tana kallan sa, ganin tunda suka taho be ce da ita komai ba game da abinda tayi, kamar ma abinda be sani taɓa shi ko ya dame shi ba. Wai shi wanne irin mutum ne?

"Ace mutum ba zai buɗi baki yayi magana ba, ba zai ce komai ba, komai aka ce shi akan dai-dai yake. Komai aka yi dai-dai, komai aka ce mutum yayi sai yayi.  Shikenan a duniya kai baka da wani ra'ayi naka na kan ka sai na wani?

"Ka duba kaga yarda mutanen nan suke treating ɗin ka, kamar wasu ɗan su. Kai ne nan, kai ne can. Kai ne workaholic, agogo sarkin aiki baka tsaya idan ba lafiya ce baka da ita ba ko?

Ɗan shiru tayi tana cigaba da kallan sa. Ko zai ce wani abu.

"Kana ji ina maka magana amma kayi banza ka rabu da ni?

Yanzun shirun yayi mata, be ce da ita komai ba, kamar yarda tasan daman ba maganar zai yi ba. Sai ma hannu da yasa ya kunna radion motar.

"Ga mahaukaciya tana magana ko?

Ƙwafa tayi tare da juyar da kan ta,ganin ta dena kallan sa yasa shi ɗan kallan ta kaɗan yana mai da hankalin sa ga tuƙin da yake, duk da cewar yau ɗin tayi masa magana ne cikin sanyi ba kamar yarda ta saba. Ba masifa ba tsiwa ba hargowa da ɗaga murya. 'ko me yake damun ta?

Wata hanyar taga sun nufa, har zata kalle shi tayi masa magana sai kuma ta gimtse bakin ta tayi shiru. Har wani ɗaci take ji a ran ta. Na haushin abinda suka yi musu sannan shima ya kuma bata wani haushin. Dan kallan sa tayi ta ɗauke kan ta tana sake yin wata ƙwafar, a fuskar sumi-sumi kamar bashi ne yake gasa mata maganganu ba, yanzu sai sunje ɗaki ya ringa faɗa mata duk abinda ransa ke so.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now