29

19 1 0
                                    

29

********Sun shafe fiye da minti talatin kowa na kai kawo a zuciyar sa, yayin da wasu daga cikin ƙananan ma'aikatan wanda ba su damu da abinda ake yi ba suke darewa ɗaya bayan ɗaya, domin ba su da ta cewa, dalilan kiran meeting ɗin gaggawar ma ba'a yi ba. Suka fara wani abun daban. Yayin da Hafsah take s tsaye har yanzun bata motsa ba, kawai bin su da ido take yi, so suke ta fice ta ba su waje, suyi yarda suka ga dama da Deeni dan sai abinda suka ce masa, amma ta kafa ta tsare bata bada duk wannan damar ba. Shi kuma Deeni babu wani abu da yake tunani sama da labarin da Maman su Mu'azzam ta bayar.

Ganin babu wanda yayi magana yasa Hafsah cewa.

"Idan kun amince da abinda na zo da shi shikenan, idan baku amince ba kuma yau a kuma yanzun nan zamu tattara yana mu yana mu, mu bar maku companyn nan".

"Wanne abu?

Babban Directorn company ya faɗa yana kallan ta.

"Zai zama Director bayan ya je ya dawo. Salaryn sa ya tashi daga 30k zuwa 250k".

Kallan kallo aka fara tsakanin su, suna mamakin wannan yarinyar, yayin da Deeni ya ɗago ya kalle ta da tarin mugun mamakin dake kan fuskar sa, amma sai de babu wanda ya lura da hakan har ita uwar gayyar bata gane meye akan fuskar sa ba, kawai de tasan yana mata wani kalar kallo da idan ta kalle shi zata kasa yin komai. Koma ta fice a wajen.

"Muna da buƙatar yin tunani".

"Duk wani tunani kuyi shi anan, babu wanda zai fita".

"Ke fa ƙaramar ma'aikaciya ce, dan haka ki ja bakin ki, kiyi shiru. Baya ga haka ke baki da kunya ne? Duka nan bamu girme ki ba? Wasu ma sun haife ki".

Murmushi tayi mai kyau, tana komawa wajen projectern ta tsaya tana naɗe hannun ta.

Tace, "Bana jin kun haife ni, domin wanda ya haife ni ba zai yi irin abinda kuke yi ba. Dan haka kar nake ganin ku, marasa mutunci kawai".

Wani Inyamuri ne ya tashi yace, "Bana jin ta faɗi ko tayi ba dai-dai ba, laifi ne, kuma hakan abin yake, a yanzu mu kuke so, dole mune a ƙasa. Idan kuka yi duba da irin abinda Ya samo mana zuwan sa Anadyr nasara ce babbar Nasara muka yi, kuma duba da shi suke da buƙatar gani ba mu ba, dole shi ɗin ne zai je domin nasarar mu".

"Maganar ka gaskiya ce, dan kuwa ko idan Oga Deeni ya tafi bamu da wanda ya fishi har yanzu a companyn nan namu".

Cewar wani shima yana faɗar ra'ayin sa. Ita de taɓe baki tayi.

Tace, "Daga baya kenan".

Ta faɗa tana takowa wajen sa, kallon ta yayi kawai yaga me zatayi, biron dake gaba rigar sa ta cire ta miƙa masa.

"Sa hannu".

Kallan ta yayi alamar me? Ita kuma ta haɗe fuska tamau, tana tsuke baki alamar ko wanne lokaci zata iya fashewa ta gasa masa magana, hakan yasa shi yin signing babu musu, ta je wajen Mu'azzam shima ya saka hannu. Sannan itama ta zo ya saka hannu a nata takardar, ta mayar masa da biron sa inda ta ɗauka, zata koma kenan ta ji ya riƙe hannun ta, cak ta tsaya tana addu'a cikin ran ta Allah yasa ba dizgata zai yi ba, su de jama'a kallo ne na su kawai. Juyowa tayi a hankali tana ƙara tsuke baki, wani ɓoyayyan murmushi yayi yana sunkuyo da ita ya gyara mata hijabin ta da ya zame, ana ganin sumar ta. Dan shima ji yayi ya kasa daurewa kowa na kallan fuskar ta, hakan yasa shi gyarawa dan sai yake ganin yarda yake ganin sumar kan ta haka ma kowa ke gani, haka yarda ya masa kyau sai yaga kamar yayi duk sauran jama'ar kyau.

Sakin hannun ta yayi tana wucewa wajen projectern nan ta maƙala papers ɗin a  cikin board ɗin dake wajen.

"Ko da zaku sauya shawara, muma a shirye muke da mu sauya ta mu shawarar".

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now