39

20 1 0
                                    

39

*******Sai ƙarfe goma da kusan rabi ta tashi daga bacci, wani irin bacci ne tayi me cike da daɗi da annashwa, ta jima batayi irin wannan baccin ba sai yau, wata irin nutsuwar zuciya taji tana ji. Ga wani irin farin ciki da bata taɓa tsintar kan ta a ciki ba sai a yau ɗin nan. Murmushi fal fuskar ta, tayi juyi a karo na ba adadi, sannan ta tashi ta kalli ɓarin sa sai kuma tayi murmushi tana shafa wuyan ta, da'alama bacci yayi daɗi ko juyi batayi ba.

Wayar ta da ta gani akan side drawer ta gani an ɗaura takarda akai, ɗaukowa tayi ta buɗe.

"Idan kin tashi ina fatan kin tashi lafiya, ya kike? Ya kika tashi? Dan Allah ki koma wajen aiki, tun jiya suka turo suke da buƙatar mu. Ni yau na tafi company akwai baƙin da zan yi. Hajiya banda faɗa dan Allah, zuciya ta zata iya tarwatse ta fashe. Ki kula min da kan ki".

"Hashim zai zo, ki kaishi wajen Mu'azzam. Ki kula".

Murmushi tayi ta ajje, ta sake buɗe wata ƙaramar envelope ɗin dake gefe, taga mukullin motar ta ne. Yayi emoji ɗin banda haƙuri yasa am sorry ya kama kunne. Wani irin dariya ce ta ƙwace mata, tare da fara tashi tana gyara ɗakin. Wato mutumin ne ya sace Mata key ɗin motar, yana ji tana ta masifa akai amma yayi burus da ita bece komai ba. Har ta shirya tana murmushi ita kaɗai. Samun kan ta tayi da saka doguwar dake cikin kayan lefan ta, ta yafa mayafi, tare da rataya jakar ta taje gaban madubi tana kallan kanta.

Ita kan ta taga tayi kyau, inaga shi kuma? Ƙara kallan kanta tayi, kwalli tasa ka da lipgloss harda su powder. Da warwaro yau aka saka sai ta fito ɗas a macen ta. Idan ta ne kawai yayi ciki saman idan suka kumbura alamar kuka. Amma kwallin da ta saka sai ya fito da dara daran idan nata. Sake kallan kan ta tayi a karo na uku, sannan ta nemi hanyar fita, har zata fita sai kuma ta dawo da baya da baya tunawa tayi da ya taɓa ɗaura mata ɗan kwalli, hula ta samu ta saka ta sake gyara rolling ɗin sannan ta fita. Fuskar ta cike da murmushi. Sanda ta fita ta tarar da Ɗalhat da Hashim a parlourn na su, an kawo musu ruwa da abinsha.

Murmushin dake kan fuskar ta be ɗauke ba ta amsa musu, tare da samun waje ta zauna suna sake gaisawa, baƙaramin mamaki suka ji ba ganin ta a haka, ba su taɓa ganin tayi doguwar magana da ɗaya daga cikin su ba, kullum fuska a tamke, fuska a ɗaure ga kwarjini da Allah ya zuba mata kai kace wata uwar mata ce idan ta haɗe ran nan.

"Daman kina dariya?

Hashim ya kasa daurewa ya faɗa, zungurar sa Ɗalhat yayi.

Yace, "Kaga barni na faɗa".

Murmushi ta ɗan yi.

Tace, "Ina Maryam?

"Tana shagon Ameerah".

Cewar Ɗalhat, dan shi har yanzu ɗari-ɗari yake da ita. Wani murmushin kawai ta yi tace musu tana zuwa.

"Na rasa dalilin da yasa Yaya Deeni zai ce mu bita wallahi".

Cewar Ɗalhat yana kallan hanyar kitchen ɗin.

Hashim yace, "To wai meye ne? Gashi nan yanzu ta mana tarɓa ta ban mamaki ai. Da har kake gwada yarda zata mana".

"To ai nasan halin ta ne".

"To gashi ta baka mamaki".

Abinci ta ci kaɗan sannan suka fito, ta gaida Umma ita da Baba sannan ta musu sallama ta wuce, suma Sallamar  ta musu suka tafi. Hashim ne ya ce ta kawo ya ja ita ta koma baya, bata musa ba ta basu suka ja, tana kwantanta musu har office ɗin,duk da Hashim ya sani amma be nuna yasa ni ɗin ba.

"Wannan motar Daad ce".

Cewar Ɗalhat yana nuna motar A. Madaki. Hakan yasa ita da Hashim suka kalli wajen.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now