1

137 2 2
                                    


✨ *ZAHARADDEEN* ✨

          
                   By

       *Hijjartabdoul*

                 1.

PARIS
  Charles de Gaulle (CDG) Airport.

Matashin saurayi ne da ya amsa sunan sa na saurayi mai jini a jika wanda zai kai a ƙalla shekaru ashirin da takwas, yana zaune a cikin jirgi, daga zaunen da yake zaka ga ne cewar dogo ne shi ɗin, kuma kyakkyawa da shi tufarkhallah gwanin burgewa. Kalar fatar sa ba wai fara ba ce ba kuma baƙa ba alamar de hutu da jin daɗi sun bayyana a tare da shi ba shi da wata makusa ko da ta ƙwayar zarra ce a tare da shi. Gashin sa ba'a kwance yake ba irin lumai ɗin nan na larabawa irin na ƴan 9ja ne, dake kan na shan gyara yasa sumar har wani ƙyalli take yi ita kaɗai. Idan sa na kan ipad ɗin sa da yake dannawa ga dukkan alamu aiki ne yake yi.

"Zaharaddeen be careful".

A hankali ya ɗago da kan sa daga abinda yake ya kalli yaron da ba zai wuce shekaru goma ba ya kusa faɗuwa yana kan kan ba, aka kira da wannan sunan wanda ya kasance iri ɗaya ne da shi, ɗan murmushin gefen baki yayi yana tuna sanda yake kamar wannan yaron sam be san wani abu ba wai shi wasa, saboda kishiyar Maman sa wacce suke ce mata Ummi sam bata san yawo ba kuma tasan tarkacen abokai bata san ƙiriniya, ba wai tayi maltreating ɗin sa ba ne, a'a kawai ita haka take tunda can da Mahaifiyar sa tana raye yasan da hakan sam bata san wasa ba kuma ta san yawan magana dan Ummi sam bata fiye yawan dariya bama. Ummi ta riƙe shi tamkar ita ce ta haife shi ta kuma nuna masa abubuwa da yawa da ko da Mahaifiyar sa na da rai ba lalle ne ta iya abinda tayi masa ba. Ummi ce mutum na farko da ta fara zama ta koya masa wankan janaba, ta fara lusar da shi game da canzin abubuwa a jikin sa na alamun balaga a tare da shi na  girma  ya fara zuwa masa ita wannan matar, tana  kuma yawan yi  masa nasihar da zai tsira da mutuncin sa. Shi kam be zai ce mata? Ummi tayi masa abubuwa da dama da be saka mata da komai ba itama ta mutu ta bar musu duniyar hakan yasa shi duka kulawar ɗan ta Sadiq da shi da Zarah ya dawo ƙarƙashin kulawar sa. ( Dayawa daga cikin iyaye basa damuwa da ɗan su namiji, wa su macen ma kunyar yi mata bayani suke, sai de kuma hakki ne babba akan iyaye da su gane fa cewa zama ka koyawa yaron ka wanda ya fara girma abu ne mai muhimmanci domin kuwa hakan ne zai gane ya fara girma idan ma baki faɗa masa to zai je ya ji ne a waje ne. Dan haka a farga a cire wanna abun wai shi kunya, a tarairayi yara maza asan me suke ciki? Me suke yi? Allah ya shirya mana zuri'a)

Zaman da wata matashiyar budurwa tayi a kusa da shi ne ya katse masa tunanin sa yana kallan ta, kafin ya maida kallan sa ga abinda yake. A kallo ɗayan da yayi mata ya gane ta, a kallo ɗayan da ya yi mata ya tuno da zaman da suka yi na tsawon shekaru takwas tare, a kallo ɗayan da yayi mata ya tuno da gaba ɗayanta ma na wacece ita?

"Shegu ƴan iska marasa kunya kawai".

Ya ji ta faɗa tana jan uban tsaki bayan ta ɗauke idan ta daga kallan wasu da suke kusa da su suna sha'anin su ba su san ma da ita ba. Kallan sa ya kai inda ta janye idan ta kafin ya maido da kallan sa gare ta.

"Kai kuma meye kake kallo na, da wasu idan ka masu kama da na jemage".

A hankali ya janye idan sa daga kallan ta ya mayar kan ipad ɗin sa.

"Shegu suyi ta kallan mutane dan su ana wani yaren da ba na su. Ƴan masu da farar fata. Shide kamar ɗan Afrika. Oho shi ya sani da wata sumar ka da baka askewa".

Sarai yana jin ta, wato ta zaci baya jin Hausa shine take zagin sa. Girgiza kai kawai yayi a fakaice 'wato mai hali ba zai taɓa fasa hali ba' ya faɗa a zuciyar sa, sanin da yayi mata da can ma haka  take da wannan masifar da faɗa.

"Dalla Malama faɗi abinda zaki faɗa ina jirgi ne".

Kallan ipad ɗin ta yayi yaga tana Video call da wata yarinya. If he's not mistaking sunan yarinyar Ameera tana da Ameer ɗin ta su ɗin ƴan biyu ne aka haife su sune suke bin ta.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now