Chapter 32

1.1K 158 12
                                    

*_KOME DA LOKACIN SA_*
  https://my.w.tt/aA7f7uPeZab
            Chapter 32
A wise woman wishes to be no one’s enemy, a wise woman refuses to be anyone’s victim.

Ina kukene maza da Mata masoya kasuwanci, ga dama ta samu! Nesa tazo kusa! Ina masu sayan d'ai d'ai ko sari karku sake a baku labari, da arziki a garin su har gwara a garin mu, kai gwara a  dakin mu, karku sake wannan damar ta wuce Ku
Ku garzayo kampanin *Greenleaf biotech* domin ya tanadar muku kayayyaki sama da guda 4500, Kama daga abubuwan amfanin yau da kullum kamar sanitary pad, pampers, baby wipes, sabulan gyaran jiki, man shafawa, magungunan qarin lafiya da magance cututtukan zamani kamar (infection, BP, diabetes da sauransu), kayan kwaliyya, sinadarin rage kina da tumbi, takalma, jakunkuna, air frying pan (baya buqatar Mai wajen suya) da ma wasu da dama.

Zaku iya siya domin amfanin kanku da iyalan ku, sannan kuma zaku iya yin sari domin saidawa ku samu riba me albarka.

Domin qarin bayani ku biyo mu ta wannan link din👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

https://wa.me/message/XMECES32SQEPK1

Ko ta WhatsApp group👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
https://chat.whatsapp.com/BebpPIrkAPj1bfiqfZkkjH

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Murmushi nayi, sannan nace mata. "Toh Ammyn duk yadda kika yi duk daya ne, Bani da abin da zan iya miki musu a kai, dan da kai da kaya duk mallakar wuya ce." Taji dadin abin da nace, har zata min magana sai ga Dr Ishaq dasu Mariama tare da Khady, kallon su nayi. Na rasa wacece zan runguma a cikin su. Dan haka na mike naje gaban Ishaq, na tsaya tare da dunkule hannun na duk biyu, nace Mishi. "Nagode Nagode sosai, ban san me zan kuma ce maka ba, amma Nagode matuka gaya." Sannan na juya gare su, hawaye na zuba. Na ma rasa wacce zanwa magana kawai dukkan su uku, suka rungume ni, ina kuka suna kuka. Daga Nesa Khady ta hango Anoosh, janye jiki tayi tare da nufar shi, ta mika Mishi hannu yazo ya zauna kusa da ita. Hawaye ne ya shiga zuba mata, ta rungume shi tana faɗin. "I miss You! Lovely." Murmushi nayi, suma Mariama da Nusaiba, suka tawo gurin yaron, tare da rungumo shi, suna haka sai ga Anoosha ta fito tana kallon su. Dai-dai fitowar Ammyn, itama murmushi take, ta kalli Nusaiba tace. "Ikon Allah! Kinyi maka da Zakiyah, kanwata ce." Murmushi suka yi sannan Dr Ishaq ya zauna aka shiga gaisawa, sannan na dauko abinci dan sunce a falon zasu ci, idan suka shiga ciki ba zasu fito ta dad'i ba. Haka na saka musu abinci murmushi, tsakanina da Dr Ishaq, sai murmushi, tare da satar kallon juna, sako ya turo min. *Don Allah barni na ci abinci mana!* Murmushi na mai da mishi, tare da tura mishi sakon. _Kai da wani idanun ka ga na kalle ka, dan bani da bakin magana!_ dariya ya min sannan ya sake kallona,  da wutsiyar ido. *Kin haɗu da shigar jikin ki, gaskiya kinyi kyau*.  _Har na kaika? Dube ka yadda kayi kyau ranar har ce maka nayi bishiyar kuka 🤭_   da sauri ya kalle ni! Sannan ya cigaba da abinda yake ya wani b'ata rai, sai na kalle shi na rike kunne na, ɗaya. Amma yaki kallona asalima turo min sakon yayi da cewa. *Karki kuma min magana*  tab'a bani Khady tayi sannan na dawo nutsuwa ta, bayan sun gama na wuce dasu, shi kuma Dr na dawo na raka shi waje, har ya manta abinda nayi mishi, ya kalle ni cikin jin dadi yace min. "Kin yin farin cikin ganin su.?"  Murmushi nayi sannan nace mishi, "ban san yadda zan gaya maka ba, amma nayi farin ciki sosai!" Kallona yayi kadan sanan ya sake murmushi. "Inayat. Hmm yanzun  idan mun dawo zaki." Zuba mishi ido nayi ina jiran me zai ce. Sai kawai ya kada kan shi ya shige motar shi, kana ya cire glass din idanun shi, ya kalle ni kasa kasa, ya ce. " Insha Allah! Wannan karon babu wanda ya isa hanani Wuf da tsaleliyar macen da take gaba na.".  D'aga kai nayi sama, sannan nace mishi. "Kamar Ya Wuf?"  "Ai naga bestie dinki tazo, zaki iya tambayar ta ma'anar wuf." Dariya nayi  cikin jan aji nace mishi. "Lallai aiki ya same ka" sannan yaja motar, ni kuma na juya zuwa cikin gidan, kamar an kira suna na, na d'ago kaina na kalli window dakin Neemrah, na ganta tsaye. Shiru nayi tare da kauda kaina, ina kuma kallo naga bata nan, a sanyayye na shiga gidan, ni dai Allah bai daura min tsoron ta ba, duk da jina da wa'azin Kabir Gombe yace babu fatalwa a musulunci,  amma Ni wannan matar tana da damuna, dan ina yawan jinta a kusa dani, koda ban leka window ba. A bakin step na ganta. Ta juya zata koma tashi sama tayi na tabbatar da hasashen na, dan haka na bita da sauri bakina dauke da addu'a. Na bi bayanta, koda naje na same ta tsaye a saman iska. "Ki daina min Addu'a! Bana bukatar addu'arki, taimako daya zaki min idan zaku tafi London zaki tafi dani!" Kallon yar renin hankali nayi, sannan na juya zan fita ta rufe kofar, "kin san me yasa baki jin tsoro na?" Ban juya ba,  kuma ban bata amsa ba, tawowa tayi gabana tace min. "Sabida bata baki da tsoron abokin tarayya, kina da rashin kunya, shi ya dauke miki karfin tsoron ki, amma ki taimake ni!"  Matsawa nayi zan wuce. "Inayatu Rahman!" Tayi min magana da muryan Khady, juyawa nayi ta saka kanta akan kafad'arta. "Kiyi hakuri ba zan iya daukar ki ba, don Allah ki barni nayi rayuwa ta babu damuwar kowa.".  "Toh shi kenan Nagode." Nayi ficcewata, ina jin shashekar kukanta, tsayawa nayi sam bana jin dadin rayuwa da irin wannan damuwar, dan haka nayi sauka na kasa, nan.muka baje hira, wanda ra bishi duk akai na ne,, har aka yi sallar magarib, da isha, sannan muka kuma buɗe hirar wasu suka yi wanka. Anan muka makale juna da Dr.
KWANA BIYU.
Kwanan su Nusaiba takwas, suka koma sabida na gaya musu nima tafiya Zanyi, amma shekara daya zan Insha Allah, na dawo kar su damu. Bayan tafiyar su dan har da Khady, wacce Hasshir ya makale mata, Mu kuma muna an shirye shiryan mu, na barin ƙasar. Matar dakin Neemrah, kamar zata yi hauka, ina jin ta naki kula ta, sai dai tsakanin na da Dr, kamar mu had'iye juna, tsabar son da muke wa juna, dan har yan uwan na, sun taya ni murna, tare da Fatan Alkhairi, yadda Hashshir, domin yana masifar kaunar Khady, idan bana manne da waya, zaka same ni ina  manne da waya ta, sabida son da muka kasa furtawa, sai dai muyi tawa  junan mu sako ta waya. Alaƙar mu tayi wani irin karfi da duk wanda ya zauna samu sai ya fahimci, mun son junar mu,  koda wasa babu rashin fahimta, asalin fahimtar juna muke, Dr Ishaq Ahijo, mutumin kirki ne, yana da kamewa sosai, dan yake gaya min cewa, ai a gida kallon shi ake akan mutumin da aljana ta aura, shi kuwa lafiyar shi lau, kawai wata yake jira. A hankali lokacin tafiyar mu na karatowa, muna kuma sabon shiri sosai, domin kuwa zan bar yaran a hannun Ammyn Khady ma zata zauna a gidan domin Hasshir yace shi yaga matar auren shi.  Munyi magana da Mahaifiyar Dr Yayar Mamah,tace nazo fa. Na gaya mata an tura ni karatu ni da Hamma Ishaq, ai kuwa nan tayi ta min nasiha, har da cewa, idan Ishaq yayi min rashin da'a na gaya mata, dan ina da uwa a raye. Murmusa mata nayi sabida ban ga wani abun da zai min rashin da'a ba, mutum ne kamili, sam zai yi wuya kaga ya kalli mace sau biyu, idan naga yana sunkuyar da kai hararar shi nake nace mish. "da zaka daina wannan pretending da yafi maka, da kake wani sunkuyar da kanka, ni bana son gulma." Murmuasa min yake tare da shafa sajen shi zuwa gemun shi. "Malik ya bude miki baki dayawa, amma idan da nisan kwana, wata rana zan rufe miki bakin kin nan domin kina yawan magana da shi, ni kuma bana son yawan Maganar nan" d'aga kai nayi sannan nace mishi. "Gaskiya na manta abinda yake buɗe bakin mutum ko zaka gaya min na nimo shi, dan wallahi sai ka gaya min meke bude bakin mutum." Mik'ewa yayi zai bar Office din shi. Nace mishi. "Kunyata kake ji? Toh madalla gwara da ka nuna min irin macen kunyar da kake ji, Kutt." Murmushi tayi yayi sannan ya bar ni a Office din Ni daya zai zabga murmushi nake.

       Ana saura sati zanu tafi, naji bana son tafiyar dan ina yawan nazari akan tafiyar karshe na watsar, ana gobe zamu tafi Ammyn tayi min nasiha me shiga jiki inda ta nuna min girma da darajar da Allah yayiwa dan Adam, tare da nuna min kimata,  nasiha dai kamar yadda mahaifiya zata yiwa yarta haka tayi min, sannan muka yi sallama, da dare.. na kwanta . Washi gari haka na rungume yarana na cike da tausayin su. Muka yi sallama da mutanen gidan. Tare da kowa, sannan aka wuce dani airport, inda na sami Dr Ishaq yana jirana, karfe tara na same jirgin mu ya tashi daga birnin tarayya Abuja.... Kuyi hakuri wallahi barci ya dame ni duk ma gama gajiya 🙏🏼🤧

KOME DA LOKACIN SA {COMPLETE}✓Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora