Chapter 19

1.1K 131 6
                                    

_KOME DA LOKACIN SA_*
        
https://my.w.tt/2E8h0g7BNab
            Chapter 19
    Na MrsUsman400
I don’t create companies for the sake of creating companies, but to get things done.

Ban tab'a kukan da nayi ba a yau, har muka gama aikin ranar ban daina kuka ba, suka dame ni da tambaya sai dai na kuma rushewa da kuka, daga karshe suka daina damuna. Ina kwancen har dare, ina tunanin Mama da yan uwana, ina son zuwa amma tsoron tozarcin Baba ya hana ni zuwa. Amma yau naji kewar kowa da kowa, kuma ina matuƙar buƙatar su,dan haka zan roki pass gobe Insha Allah naje na gansu. Ina jin wani baƙin al'amari a tare da Ni, har na dawo gida, bana dai dai, kuma bana son damuwa. Ina jin matan gidan mu suna gulma amma haka bai dame ni ba, dan ina ji a jikina kamar nayi rashin me girma a rayuwata. Har dare ko waje ban leko ba, haka yayi matukar basu mamaki, duk da bani da yawan shiga cikin jama'a, amma ina ƙoƙarin idan anyi wani abu nayi musu Jajjen ko sannu, haka ya rage kaifin k'iyayyar da suke min. Ina zaune akan abin sallah Maman Ummi ta d'aga labulen tare da cewa. "Hmm! Inayat lafiya kuwa, naga yau gabaki daya baki da walwala, ko rasuwa aka miki."  Ban san ya aka yi ba, ko dan kalmar mutuwar ce ta fadar min da gaba, amma naji wata irin tsoron da ban tab'a ji ba, a razane na kalle ta. Kafin naji wata irin rauni nace mata.."Wallahi ban sani ba." Shiru tayi na wani lokaci, kafin tace min, "toh ai ya dace ki kira gidan ko? Kiji lafiyar su." Kamar wanda nake jiran cewar haka kawai idanuna ya shiga zubda kwalla. Cikin D'an dana sani nace mata toh. Na amsa ne kawai, amma bani da hanyar da zan same su, tunda na goge Number su a wayata bayan nayi blocking dinsu. A yau naji na tsani kaina fiye da yadda na tsani MALIK, bana son ganin kaina, wai me yasa ma nake raye ne? Nayi wannan tambayar yafi sau goma, amma babu amsa, sai juyin da d'an cikina yake na alamun yana azabtuwa da yunwa, bude wata jug nayi na dauko karamin kofi na cika da kunun koko. Na fara sha ina zubda kwalla, ina kuma jin kewar gida sosai. Har kusan karfe ɗaya na dare idanuna yaki barci,sai da na tashi nayi alola zan gabatar da sallah, sannan na fara jin barci. Amma ban kwanta ba sai da nayi isha tare da shafa'i da wutiri, sannan na daura sallar nafilla akai. Inda na jima ina addu'o'in sosai, na kai kuka na ga Allah na kuma san zai share min hawaye, na kai ƙarar duk wanda ya shirya zalintana, gurin Allah. Shima Malik na kai shi kotun Allah, inda babu kudi ko wata mukami da zata bashi kyautar gaskiya, a hankali nayi kwanciya ta. Ina jin kewar Mahaifiyata, kaunarta yana kara samun karfi a zuciyata, haka na kwanta cike da tunani wanda ya haifar min mafarkin Mamah, cikin fararen kaya. Tana zaune na daura kaina akan cinyarta, murmushi tayi cikin jin dadi. Ba zance ga abin da muke tattaunawa ba, amma naji dadin ganinta. Haka tayi ta murmushi amma bata ce min kome ba, karshe dai haka na farka sakamakon jin sallama a masallacin Unguwar mu.

    A hankali na tashi,  duk jikina a mace, nayi alola sannan nazo na gabatar da sallar, ina idarwa na daura ruwan wanka. Ina samu yayi zafi na dauko miyar da na ajiye, na kasa kome, kiran layin Khady nayi na gaya mata ina son pass zan je Gombe, aikuwa tace min naje. Ina gama cin abinci shima dan abin cikin ne da babu abin da zai sani cin abincin. Na shirya da wuri na nufi tasha,
              Mun isa da wuri, dan haka na duba jakata, na dauko babban hijab na saka,sannan na nufi inda ake sayar da nikab na saya, a hankali na saka. Sannan na nufi Unguwar mu,  daga nesa na hango kofar gidan mu, na nime wani yaro yaje min gidan ya kira min Mamana, koda yaje suka ce mishi yaje sun tashi, daga gidan take kaina ya kulle, Mama ne suka tashi ko har da Baban mu, gabaki daya bani da amsar tambayar kawai na juya na bar garin ma, sabida ban san me zai iya faruwa ba.   Koda na koma kashare ban wani damu da mutanen gidan mu ba, sai dai ina jin suna cewa." Ai taje zubda cikin ne sai kuma bazai fita ba," Maman Ummi tace musu."A'a kawai dai bata da lafiya ne, domin tana cikin damuwa sosai, kuma ni wallahi bazan kuma zaginta ba, dan shekaranjiya. Ita ta biya mana kudin wuta dana magani da baban Ummi yaje asibiti bai jin dadi. Dan haka Ni na zubda damuwa akanta, yarinya nan bata tab'a shiga damuwar mu ba, amma mu, mun shiga nata, idan gari ya waye zamu gaishe mu, ta tambaye mu yaran mu, toh meye laifin? Ba rokanku take ba, ba shiga hurumin ku take ba, meye nata da bazamu kyaleta ba. Don Allah mu kyale Inayat ta huta, tana cikin damuwa kar mu kara mata matsala akan wanda take dashi ciki ne da ita, kuma tana bukatar nutsuwa domin rayuwarta da na abin cikinta. Amma idan bai muku ba, bismillah." Daga haka ta bar musu tsakar gidan, ni dai ina kwance a d'akina.

           Cameroon.
    Abun tausayi, idan kaga yadda su Zehrah suka koma, dangin Baba sun zo ta'aziya dukda ba wai zuwan na Alkhairi bane sun zo ganin abinda Rukayyah ta dawo dasu, ladar bariki. Sai dai suna zuwa zasu ga su Zehrah babu abinda suka bari nasu. Har jikin su yayi sanyi, basu gama rud'ewa ba sai ranar addu'o'in uku, zuwan su Nusaiba da Mariam. Tare da mazajen su. Jikin su yayi mugun mugun sanyi, haka suka gama zaman su. Suka bar gidan.

Satin su Mariam daya suka juyo zuwa Gombe, lokacin da zasu rabu ne abin tausayi, domin kowa sai da ya zubda hawayen dan kasa janye jikin shi yayi daga d'an uwan shi, abin so touche heart, dakyar aka raba su da juna suna wani irin kuka me ban tausayi.... Suna ji suna gani suka tafi suka bar su, lokaci guda maraici ya sauko musu, dama sun girma amma kullum zaka same su a jikin juna, Kan Zehrah akan cinyar Balkisu.

               Dole Baffa yake zama dasu, sun saba dashi ba iya shi ba hatta sauran jama'ar gidan sun saba sosai, Dr Ishaq yana kawo musu duk abinda suke bukata kuma zai zauna dasu ya d'an tambaye su me suke bukata, abu daya suke gaya mishi Aunty Inayat.
           London.
Durkushe yake gabanta, cikin damuwa da tashin hankali, ya riko hannunta, muryan shi na rawa yana ce mata. "Wallahi ban san ta ba, kawai naji sunan ya zo min ne, sannan ba zan iya tuna kome akan sunar ba. Ki yarda da Ni babu macen da ta isa tsayawa a gabana har naji wani abu akanta ba a haifeta ba, lafiyata dan ke daya aka yita, don Allah kiyi hakuri bazan kuma ba." Tab'e baki tayi tare da barin d'akin ta nufi d'akinta. Abinda ya faru kuwa wai, mafarki yayi. Tare da zabgawa Inayat kira shine zuciyarta ya dauki zafi. Akan yana niman mace, komawa gadon shi yayi cike da bakin ciki, dan shi kadai yasan yadda yake ji akan Zeemalik. Duk ranar da ya sami damar kamata sai yayi mata asalin jahilin duka, wanda jikinta zai gaya mata, irin dukar nan da zai mata. (😜𝐊𝐚𝐧𝐚 𝐫𝐮𝐰𝐚) haka ya gama masifar shi a ran shi sannan ya kwanta tare da tab'a little Malik, iskar bakin shi ya furzar sakamakon jin yadda tayi dumm, tana niman abokin haɗin ta. A yanzun haukar Zeemalik ya laffa sai dai bai da ikon kallon mace kullum yana manne kusa da ita,matukar ya dawo aiki. Bata fada da kowa. Amma shi bai isa yayi rayuwar shi cikin jin dadi ba ne.

          Cameroon.
"Yanzun sabida rashin hankali yarta shi ya bada ita ga mutumin da bai sani ba, toh yanzun ta ina zaa same ta?" Cikin sassayyatar murya tace. "Ai yace karta zo gidan shi sai ta samo mijinta, gashi Mama ta rasu bata sani ba, kuma bamu san wani hali take ba." Inji Zehrah, wacce take bawa Yan uwan Mamah labarin abin da ya faru, zata kuma magana, Balkisu ta riketa, kallon juna suka yi sannan girgiza mata kai. al'amarin tai shiru haka. Sunkuyar da kai suka yi, dukkan su jikin su yayi matukar sanyi, sabida ko babu kome mahaifin su ne, su taya mahaifiyar su kare kimar shi. Haka da suka yi sun kuma kara sayan zukatar dangin su baki daya, ya zama na kowa so yake ace su je su zauna dashi.

        * Abuja.
"Don Allah Ammin kiyi addu'a, taya zaki ce babu ruwanki, sannan ki zauna kina fada ya tafi ya barni da damuwa, ki tuna ke uwar shi ce, taya Allah ba zai jarabce shi ba,.kin manta da damuwar shi ki dauki na wasu kin daurawa kanki." "Mahnoor!" Dakatar da ita tayi sannan tace." Ki fahimci wani abu, babu yadda zai manta dake, bayan yana matukar damuwa dake, taya zai tafi abin shi don Allah kiyi nazari da kyau, Malik addu'ar mu yake nima ba fushin mu ba, domin dagula kome yake, kuma zai iya Mantawa da kowa matukar bamu bashi muhimmancin gurin sanya shi a cikin addu'o'in mu ba, Ammih kiyi nazari dakyau." Daga haka ta kashe wayar. Shiru Madam Azizah tayi tana auna abinda Mahnoor ta faɗa mata sai ta ga kusan gaskiya ce. Domin itace ta shagala da yawa, kuma gashi nan D'anta yayi nisa da ita.

     Dan haka taji a ranta zata mike ta fara mishi Addu'a..
      *** Bayan wata uku...
Dake an bani hutun sai na haihu zan koma, na kira Khadi muna lissafin abinda za a buƙata idan haihuwar tazo cikin sauki, na mika mata katin bankina, na kuma gaya mata code din sabida halin Rayuwa, na gaya mata kome dan kar na mutu a rasa inda za akai min abin da na haifa.
     "Ki duba kayan babyn kome yayi ko? " Na tambayeta ina kallon sani set din Unsex yayi min kyau pink dashi, tun kala biyu na saya, sabida tun cikin na wata shida suke ce min ana tsammanin ko biyu ko uku zan haifa, Ni dai na sayi koma meye. Na saya, nayi imani da Allah da yau Malik yasan da cikin toh ba makawa da yanzun ya hanani zaman lafiya, yana mamuke da mulki, hadi da nuna min fin karfin. Ajiyar zuciya na sauke tare da jin babu dadi, kwanciya nayi tare da kallon Khady nace mata. "Na gaji da wannan a aikin. Domin ina gab da sauke shi na huta!". Cikin ko in kula tace min! "Amma ai munyi alkawarin duk abin sa suka min, dan haka ku biya ni ko kuma na fara niman rigima." Dariya tayi sannan tace min!" Kibar ganin dan ina lallaba ki, sabida dole ayi jigila damu, ko kuma mu tashi muyi ta rikici tun kafin muzo duniyar ma!.." kuyi hakuri don Allah muna fama da rashin wutar nepa ne..

KOME DA LOKACIN SA {COMPLETE}✓जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें