Chapter 20

1.2K 154 15
                                    

*_KOME DA LOKACIN SA_*
        
https://my.w.tt/rIRF00voOab
            Chapter 20
    Na MrsUsman400
     Happiness is when what you think, what you say, and what you do are in harmony.

"Kin wannan shi zaki saka min a cikin basket din nan, sannan duk abinda ake bukata na sayi kome babu abinda ya rage min don Allah, a zaman taren da muka yi idan nayi miki kuskure ki yafe min."matsowa gabana tayi tare da rike hannuna, tana kallon fuskana tace min, "tun daga lokacin da na ganki, ban tab'a jin ko ganin laifin ki ba dan kina Kawata ba, sai dai ke din ma'abociyar adalci ne, dan haka ki kwantar da halinki ina tare dake.". Murmushi nayi tare da saukar kwalla daga cikin Idanuna na rike hannunta. Ina faɗin "nagode sosai!" Daga nan muka cigaba da hada kayan muna gamawa na mike a hankali naje ban daki na dawo, anan naga Maman Abba, tana amai. Kauda kaina nayi a hankali na cigaba da tafiya tace min."Inayat ko zaki taimaka min ne,.tun safe amai nake!" Ban da zuciyar musulinci yaushe zan kalli wannan matar, dan haka na dawo gabanta, na fara tambayar ta. "Me kika ci?" Nan tayi min bayanin yadda take ji shareta nayi sannan na koma daki na rubuta mata magani da allura ta sayo na mata.. sannan na koma na samu Khady ta gyara kome har ta zuba mana abincin. Zama nayi muka Ci, sannan ta shirya ta bar gidan, dake aikin dare ne da ita. Ana kawo kayan Maman Abba, nayi mata allura sannsn na barta taji da sauran. A hankali rayuwa take kara tafiya, zuciyata da hankali na yana tare da yan uwana da Mahaifiyata, haka kawai sai naji maraici ya kamani, ban tab'a jin kewar Baba ba, kawai na ina kara jin haushi abin da ya aikata min, sosai. Sabida abinda yayi ba haka iyaye na gari suke ba. Dan haka na fita hanyar shi.
  Gombe
Mutuwar Maman Inayat bai sawa Baban Inayat yayi hankali ba sai ma ƙoƙarin ganin ya mallake gidan baki d'aya wanda take dan haka ya shiga kawo musu sayan gidan, yana cikin wannan yanayin Allah ya hada shi da hatsari, wanda yayi sanadin karyewan kafarshi, ya taru a guri guda. Anyi dauri yafi sau uku bai gyaru ba. Karshen kafar ashe kwayar cutar tsatsa ya shiga cikin kafar (TT), dan haka aka yanke kafar daga idanun sawu zuwa kwanji, karshe abokan shi da suke kai shi su baro shi suka daina zuwa gurin shi. Matan shi kowacce ta gaya mishi gaskiya ba zata iya daukar nauyin shi ba. Ya zata wasa ne sai da Hamisu yace a dinga bashi abunci sau biyu a rana, daya da safe daya da yamma, wai shine mai dama dama, domin duk iyayen su mata sun hana yaran taimaka mishi, wai kowacce tana fadin ai ba Ƴaƴanta kadai ya haifa ba, dan haka babu wanda zai bauta mishi tunda shima bai bauta musu na, sakayyar Allah yana daki ga ciwo ga yunwa abinda ya shiga barazana da lafiyar shi kenan, kafar da aka yanke ta cigaba da ruruwa, har zuwa gwiwar shi. Nusaiba da Mariam basu sani ba, sai wani Jumma'a da suka shirya zuwa mishi wuni, dan ko da suka gaya mishi mutuwar Maman su. Cewa yayi. "Ina ruwana, kune kuka rasata ni ai ina da wasa matar" wannan maganar yayi musu ciwo sosai, dan haka suka yi alkawarin ba zasu tab'a zuwa gidan shi ba sai dalili babba. Mijin Nusaiba ne yake gaya mata yaje gidan yaji baban ta bai da lafiya. Shine ya gaya mata, suka lokacin zuwa sake mazajen su, suna da rufin asiri, nan ya bata kudi yace ta saya mishi wani abu. Rike kudin tayi bata sayi kome ba, tafi son sai ta gan shi tasan me zata saya mishi, ko ta bashi kuɗin. Baba ya wulakanta yaran shi mata, dan gani yake koda ya kyautata musu, karshe Uwarsu ce zata more su, shi yasa koda aka fara batun auren su. Yaja ya noke, musamman Yaran Mama, dan yasan ba zata tab'a d'aga mishi hankali ba, kamar sauran matan shi. Sauran matan idan suka tashi aurar da Yarana yana ƙoƙarin shi sosai. Amma ban da Mama.      Karshe Allah ya taimaka ita da Inayat suka yi ta adashe, ana kwashewa zasu tafi kasuwa, kafin wannan al'amarin ya faru da ita, tare suka yi sayayyar kayan auren kanenta, aka zuba kayan a gidan wata makociyar su. koda auren yazo kome anyi shi cikin walwala dukda babu Inayat, amma shi kan shi sai da yaji kunyar duk abinda aka yi, sabida Mamah tana da jama'a, kuma Allah ya sanyawa mutane soyayyarta a zukatar su. Dayawan mutane basu san soyayya ba. Basu san daukaka ba. Gani suke kamar soyayya itace daukaka. Ko daukaka itace soyayya. Kowanne da cin gashin kan shi, zaka daukaka amma baka da soyayyar mutane toh daukaka ba zai amfane ka ba, da mamah ta fahimci, Allah ya bata jama'a da soyayyar su, sai ta kwantar da kanta ta kuma rike kimarta, sai gashi har gida suke biyota suna mata shatara na arziki, daga baya kishiyoyinta suka shiga gaya mata tana maula da rokon sune, bata tab'a magana akan haka ba, ta barwa Ubangiji sanin shi akan bata abu uku da yayi, Jama'a, soyayyar mutanen, da kuma Daukakar mutanen, babban abin alfahari ne ka samu irin abu a lokaci guda. Wannan kenan, a kofar gidan suka haɗu kowacce mijinta ya kawo ta, mijin Maryama yana da mota shi ya kawo ta a cikin shi, mijin Nusaiba a kashin, roba roba. Lokacin da suka iso farin ciki ne ya cika su, kamar zasu me, Sannan Isah mijin Nusaiba ya isa gurin motar Hamid mijin Maryama, ya mika mishi hannu. Bai karb'a ba sai da ya fito, suka gaisa sannan suka ja gefe suna tattaunawa. "Yallabai da fatan baka gaya mata halin da yake ciki ba! Dan nima ban gayawa Nusaiba ba, na fison su ganshi da idanun su." Murmushi yayi kasancewar shi ya dan girma kadan, dan zasu kusan sa'a da Malik, shi kuma Isah ba zai wuce irin ashirin da takwas zuwa tara ba."kai haba, ai basu sani ba, kawai dai na mata bayanin bai da lafiya, kaga kenan zata fi fahimtar halin da yake ciki, ban da fitar hakkin shi na Uban da wallahi babu abinda Maryama zata zo yi a gidan mugun uba irin shi ba." Murmushi Isah yayi sannan yace mishi, "haka zamu yi hakuri mu taya su kyautata mishi,." Da haka suka juya gurin matan su, suka ga sun zuba musu ido, cikin mamaki suna kallon juna. "Ba dai gulmar mu kuke ba?" "A'ah Baby, akan me zanyi gulmarki kawai Yallabai isa ne yake bani shawarar ko zan nimo wata yar budurwa ce!" "Hubby! Maza kayi zubda yawun bakinka, domin naga baka da lafiya." inji Maryama da mijinta, satar kallon juna Mijin Nusaiba suka yi, tare da sakewa juna murmushi, domin basu iya bayyana soyayyar su a gaban mutane, amma kuma a bayan fage, mijinta mugun dan soyayya ne, idan yana gida rufe get yake yayita Zungure ta.
            Sallama suka yi musu, kowanne ya kama gaban shi, domin kowa yasan yan Gombe da ƙoƙarin yin aikin Gwamnati da kuma kasuwanci. Bayan tafiyar mazajen su suka shiga cikin gidan da sallama, kallon su matan Babansu suka yi musamman yadda suka shigo cikin fara'a, tare da gaishe su, dakyar suka amsa, sannan suka zauna a kujeran yar tsuguno, suna kallon yadda gidan kamar ba ana suka rayu ba, ko ina ya mutu, babu wani Cigaba. "Inna Jumala, ina Baban yake?" Nuna musu kofar suka yi, a hankali suka nufi bakin kofar, wari da zarni ya musu sallama, daga bakin kofar suka tsaya. Suna kallon ikon Allah, da gaske dama hisabi tun ba ajiye lahira ba ake yin shi. Rufe baki Nusaiba tayi saboda amai da ya tawo mata,"munafukai nasan jifana Hammadada yayi dan yana zargin ni na kashe Rukayyah, shi yasa yake ta min jifa tsohon banza, yasa ka ido yaga yadda zan mishi. Ku fitar min a gida kafin na taso na dake ku da sandar hannuna, uwarku da ya gama ince zaman kanta ta koma sabida ta isa, toh jinin matsafa ya'yan karuwa". Wani irin kuka ne ya kwace musu, a hankali suka ja da baya, Maryam na girgiza kanta tace. "Ba zaka tab'a sauyawa ba, ba zaka saduda ba. Mun fita hakkinka a matsayin mu na ƴaƴan ka, Allah ya baka lafiya." Daga haka ta ciro kudin da yake cikin jakar ta, ta ajiye mishi sannan ta ja hannun Nusaiba da take ta amai. Suka fita a gidan.
      Kashare
Yau na tashi da nakuda, duk wani abinda ya dace na bukata duk na hada, sai ruwan zafin da nake sha a kai a kai, sannan na turawa Khady sakon ina nakuda ko zasu zo tare da Maman Tawah ta duba ni, babu b'ata lokaci suka iso. Tare da kayan aiki, dubani nurse din tayi sannan tace min. "Sister Inayat da saura ko zamu tafi asibiti ne?" Gyada mata kai nayi muka nufi asibitin. Tunda matan gidan suka ga mun fito Maman Ummi ta raka mu, suka kafa gulma, tare da cewa zasu zo su duba ni, ko ina kuka da ihu. Haka suka har suka tafi basu ganni ba. Haka na wuni ina fama da abu har zuwa karfe biyar na yammacin Laraba, kafin Allah ya nufa na haihu, cikin sauri suka shiga gyara jaririn, duk karfina ya kare, kafin su yanke cibi, wani ya kuma faɗowa, a raina nace. "Mugu Azzalumin! Ba daya ba har biyu ka zuba min ka tafi kabar ni da wahala." Mahaifan suka cire, tare da duba min sister Khady nacewa. Maman Tawah, don Allah ku dinke min ita, sosai." Cikin sauri na harari Khady sannan nace mata. "Baki da imani ne! Ban karu ba ai."  Dariya tayi sannan tace min. "So nake idan Baban two yazo ya kuma miki barnan da yayi, wallahi ya dagargaje bakin ki. Ya" kwafa tayi, cikin jin dadi. Tana goge Yaran, dinki kan nasha shi, dan kamar yadda Khady ta bukata haka aka dinke ni, ina kallon yaran cikin wani irin soyayya, "Allah sarki Mamah na, ko a wani hali kike?" Murmushi Khady tayi tace min. "Duk inda  take tana cikin amincin Allah." "Nagode sosai Khady kinfi karfin kawa sai Yar uwa." Murmushi tayi bayan ta sanya min babyn farko a kirjina, "Aliyu MALIK Mai Nassara Anoosh! Shine na farko" Ta faɗa min kai tsaye. Sannan ta kuma dauko dayan ta daura min a kirjina. "Rukayyah MALIK Mai Nassara Anoosha"  kwalla ne ya cika min ido, na fara kyaftawa tace min. "Bana son wani kukan shauki ki gaya min kin yafewa MALIK?" Daure fuska nayi cikin jin haushi nace mata. "Har abada bazan yafe mishi ba." Tab'e baki tayi sannan tace min. "Toh haka yafi tunda ba zaki yafe ba, da alamu har yanzun kayan aikin shi bai ladabta mana da bakin ki ba...💋 Zamu sha suna

KOME DA LOKACIN SA {COMPLETE}✓Where stories live. Discover now