Chapter 33

1.2K 166 9
                                    

https://my.w.tt/rAUzM8F4Zab

*_KOME DA LOKACIN SA_*
 
            Chapter 33
I don’t care what it is in life: listen to your heart. If you do, no matter what, you win.

Ina kukene maza da Mata masoya kasuwanci, ga dama ta samu! Nesa tazo kusa! Ina masu sayan d'ai d'ai ko sari karku sake a baku labari, da arziki a garin su har gwara a garin mu, kai gwara a  dakin mu, karku sake wannan damar ta wuce Ku
Ku garzayo kampanin *Greenleaf biotech* domin ya tanadar muku kayayyaki sama da guda 4500, Kama daga abubuwan amfanin yau da kullum kamar sanitary pad, pampers, baby wipes, sabulan gyaran jiki, man shafawa, magungunan qarin lafiya da magance cututtukan zamani kamar (infection, BP, diabetes da sauransu), kayan kwaliyya, sinadarin rage kina da tumbi, takalma, jakunkuna, air frying pan (baya buqatar Mai wajen suya) da ma wasu da dama.

Zaku iya siya domin amfanin kanku da iyalan ku, sannan kuma zaku iya yin sari domin saidawa ku samu riba me albarka.

Domin qarin bayani ku biyo mu ta wannan link din👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

https://wa.me/message/XMECES32SQEPK1

Ko ta WhatsApp group👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
https://chat.whatsapp.com/BebpPIrkAPj1bfiqfZkkjH
    ~~~~~~~~
Ranar Alhamis muka sauka a ƙasar London, cikin nutsuwa muke saukowa a jirgi ni da Dr, yana rike da jakata, muna tafiya. Kasancewar mun shiga garin an fara k'ak'ar sanyi sai gashi na fara rawan sanyi, dama kuma tun a gida sai da ya gaya min ki nemi rigar sanyi, nace mishi shigar da nayi ya ishe ni, kallon shi nayi jikina yana wani irin ta wa, a hankali ya zare sweater suit din shi ya bani, ina sakawa na wasu lokuta na sauke ajiyar zuciya, sabida naji dumi, ga kamshin turaren shi me shegen dad'i, murmushi nayi sannan nace mishi. "Nagode!"  Da idanun shi ya amshi godiyar. Hararar shi nayi sannan nace mishi. "Meye laifin bakin ka da ba zai amsa yace nima haka ba?" Share ni yayi dan ya fahimci tsokana ce kawai nake mishi kuma idan ya biye min zan ta damun shi da magana, har muka gama dibar kayan mu, muka fito. Yaron Mrs Muhmood muka gani, kallon Dr Ishaq nayi sannan nace mishi. "Toh ni zan tafi inda nafi wayo, kai kuma."  Murmushi yayi sannan yace min. "Yayi miki kyau" tsayawa nayi a gaban shi, jikina yayi sanyi, na kalle shi bai damu da sanyin da aka hurawa ba, "ki je yana jiranki!" A sanyayye na juya zan fita, ya rike jakar hannuna, ya amsa sannan ya bude min kofar motar na zauna, murmushi ya sake min bayan ya rufe kofar ya sunkuya daidai window motar, yace. "Shi kenan? Zamu hadu gobe Insha Allah, sai ki nuna min gidan da kike."  Kasa magana nayi sabida yadda nake jin numfashin sa a daidai fuskana ya sani kara sunkuyar da kaina, "ok kuje" ya buga motar bayan ya mike daga jikin motar, yana murmushi. Juyawa nayi bayan mun bar gurin ina kallon shi, Ishaq na musamman ne! Ina jin shi a raina da zuciyata,, Ni daya sai murmusawa nake...
    ***
Rashin nutsuwar da yake fama dashi kwana biyu ya ta'azzara, kwance yake daga shi sai Boxes ɗin shi, singlet ne a jikin shi irin me budadd'yar jiki, idanun shi lumshe kamar wanda yake barci, nan kuwa idanun shi biyu, ajiyar zuciya ya sauke lokacin da tunanin Inayat suka taru a zuciyar shi, ya rasa yadda zai bar kasar nan yaje ya ganta, koda kuwa bata yafe mishi ba, zai samu nutsuwar zuciya. Shigowa Zeeh tayi sanye da wata haf gown, ta nade hannunta a kirji, tana kallon shi, murmushi tayi sannan ta karasa inda take ta zauna a bakin gadon, bai bude ido ba dan yasan ma ita ce. Shafa cinyar shi tayi tare da sake mishi murmushi, kin buɗe idanu yayi ta haura saman shi, tare da kwanciya a jikin shi. Cikin sanyin murya. Tace mishi. "Ya MALIK!" Bude idanu yayi cikin gajiya da ita, dan wallahi ta gundure shi, niman kai yake da ita. "Ina son na shiga wani gasar da za ayi na red capter, don Allah.". Bude idanu yayi tarr akan ta, sannan ya mai da ya rufe. Cikin ko in kula yace mata. "Ina zaki kai min igiyar aurena?" Ajiyar zuciya ta sauke tare da zuba mishi ido,dan matuƙar ta shiga gasar toh ta kuɗin ce! Zata zama wata abu na musamman a kasar Ingila. Zata sake magana yace mata. "Luk ni ba jahili bane! Sannan ba zan lamunci ki shiga gasar ba, dan karshe haka zaki na fita babu hijab balle mayafi. " "Ya MALIK!" Ta fada a rauna ne, "na gama magana tace." Ya gaya mata haka tare da lumshe idanun shi, cikin bakin ciki ta sauka akan shi tare da cewa. "Zan yi fa! Ko kana so ko baka so" sannan tayi juyawarta, tana bakin cikin wannan lamari, ace mutum kwana biyu aiki yayi tasiri akan shi kwana biyu ya ɓalle kamar bauna, kullum aikin kenan yau tana mishi aiki zai yi wata biyu zuwa uku, kafin na hudu sai ya kusan mata shegen duka. Wannan abu yana bata haushi , shi yasa yanzun koda karfin tsiya sai tayi. Dan haka ta shiga hada wani shegen aiki akan shi, tana. Me jin dole zuwa dare yazo ya bata hakuri tare da amincewa. Haka ta gama aikinta bai zo ba har washi gari. Bayan yayi musu booking na abincin da zasu karya dashi, tunda ya sauka ya biya tare da zama ya fara cin na shi. Yana kallon kofar d'akin ta, dan bata fito ba. Kamar ya haura sama amma ya share ta, yana gana cin abincin shi yayi ficcewar shi. Ita ta sani. Haka suka ci-gaba da zaman doya da manja har na tsawon sati Daya. Ta kuma hada wani aikin. Wannan karon ta samo shi dan bu, sai gashi ya ajiye mata sako zata iya shiga gasar, abin mamaki wannan lokacin sai ya zamana basu samun haduwa da juna, sai suyi almost three days basu saka juna a idanun ba, kuma ba kowa ya bata shawaran haka ba sai Tabawa, domin tayi alqawarin sai ta fidda ta a gidanta yarta ta shiga, rashin zamanta ya janyo mishi yawon gidajen abinci. Tunda ba girkawa take ba, gwara shi yakan shiga yayi musu ko taliya ce, suci har da ita tayi ta cewa ashe dama ya iya girki. Shi kuma ba haka bane matsalar shi, yana bukatar mace a kusa da shi, koda zai yi abun toh a nuna yayi bajinta, idan Zeemalik ta yabi abincin tana durawa tumbin ta ne,.dan haka ya daina damun kanshi da girki, sai dai su sayi abincin waje..
    ''' Yau satin mu biyar da zuwa, muna daukar darasi yadda ya dace, idan na dawo Kum zan tafi makarantar da Ammyn ta sani, gashi Mrs Muhmood tana da kirki, itama  gwana ce a girki da iya tattalin rayuwa, haka yayi matukar kara min kwarin gwiwa, domin ita take yaba min da yadda nake kokarin gwada abun da nake ɗauka, sai Ishaq. Haka yana da nasaba da yadda muka yarda da junan mu, a idanun mu da zuciyar mu, ta yarda da soyayyar juna, amma a zahirance mun kasa gayawa juna, sai b'oyewa muke, zan iya cewa tun zuwan mu, yake kokarin ganin ya gaya min, Amma ya kasa, sai ya barshi Kawai, sai mun kusan kammalawa sai ya gaya min.  Kuma kowa ya ganmu zai kira mu da ma'aurata, amma kuma Ishaq yaki wani abu sai ma share ni da yake nima na watsar da shi a gefe.
    ***
Gombe.
Dakyar yaja da gindi ya fito bakin kofa yana fad'in. "Jumalo! Ki bani kunu mana, ko min kashin sai yunwa zata kashe ni."  Dariya suka saka mishi tare da shewa. "Yanzun Baban Inayatu! Har kai ne kake niman a baka abinci kar yunwa ta kasheka, bayan nan Yaranka suka kawo maka kudi domin kaci abinci kace baka so su kwashi tsiyar su, Ai dama hakkin Rakiya ba zai Barka ba, kuma mu zuba da kai. Abinci ne dai sai dai ka mutu amma ba zamu baka ba, dan haka ka mana horon yunwa, sai dai mu fita mu nima ba dai ka nimo mana ba, ina dalili tunda muma mutane ne, sai ka raba mu da gidajen iyayen mu, mu zauna haka*+ babu ciyarwa ka tab'a yadda muke ji." Kallon su Asabe tayi matar Hamisu, tace musu. "Amma baku tsoron Allah!  Duk fifikon da ya nuna muku akan Maman su Inayat,. Bai ishe ku ba. inayat taje aiki, ta dauki albashin ta raba daku, ai Allah ba azzalumin sarki bane, Yana nan yana ganin ku, kuka zauna kuyi ta cutar da bayin Allah. Yanzun kuce zaku gama da duniya lafiya, Wallahi sai kun biya abinda kuka aikata, domin Ubangiji yanzun tun a duniya yake hisabi ba sai an ji lahira ba. Kai kuma baban Inayat baka ga kome ba, nan Su Nusaiba zasu kawo maka kudi ka musu zagin kare dangin, sannan kayi tsammani Allah zai Barka lafiya, toh ga mala'ikun duniya nan Allah ya baka su, aiki ɗaya ya ishe ka, su kwashe kudin kuma su Barka a wulakance. Baka ga kome ba wallahi." Daga haka tayi wucewarta ɗakinta, dan ta gaya musu abinda yake ranta, kuma bata jin kome, dan ko kwanaki da Hamisu ya dake ta, yan uwanta maza yan kalare suka zo suka mishi shegen duka, tare da tsoma shi cikin kwata, suka kuma tabbatar mishi, wallahi ya kuma dukar musu kanwa sai sun sare shi gida uku, sun ajiye shi a kofar gidan, idan yana ganin karya ne bismillah. Haka Mahaifiyar shi, ya kwashe shi zuwa asibiti, yayi jinya dan kudin hannunta ya kare, ranar da suka dawo, Mariam da mijinta sun zo suka bawa Baban kudi yaki amsa bayan ya mata zagin wulakancin a gaban mijinta, haka suka fita suna tana kuka, sabida abin yayi mata cizo, shi kuma yaki daukar kudin Jumalo ta kwashe dubu biyar. Abinta,  dakin suka shiga ita da Kishiyarta suka kalli juna sannan suka Jumalo tace. "Nifa na sare da aikin Inayat nan kamar ya lalace, domin Kinga zuwanta nan babu wani abu da ya sauya, sannan Hamisu ya tabbata min da cewa mutumin da ya aureta ranar, yana cikin manyan masu kudin kasar nan, mun dai biya boka kudin shi, amma da alamu aikin bai yi ba, domin ai munce a  ranar da aka daura auren zai sake ta, tare da mata korar kare, haka zai sanya ta shiga duniya, amma sai ganinta muka yi da yara.". Wani harara Maman Hindu tayiwa Jumalo tana fadin. "Baki da hankali, ai tabbatar da aikin yayi kenan, in ba haka ba. A ina ta samo yara biyu masu shegen kyau ai sai dai karuwanci, kuma karki yarda ki sare domin karshen rayuwarta  kenan, Dan boka ya tabbatar min ba zata tab'a abin arziki a rayuwar duniya ba sai ta lahira idan ana yi acan tayi. Kai ko a lahira ba a fatan yarinyar tayi arziki domin duk sai tafi yaran mu daukaka." Shiru Jumalo tayi sannan tace. "Kuma haka yayi ba, domin nima na fara tsanar yar Banza, shi kuma wancan gurgun fa? Ko shima aikin bokan ne?" Tab'e baki tayi sanan tace. "Babu wani kawai halin shine, dan shi yace Yarinyar bata kama da zuri'arsa, ta dauko Zuri'ar mahaifiyarta ce shi yasa ya tsane ta, musamman yadda suka nuna basu son shi, kuma bawai ita daya bace hatta yan uwanta basu kama da shi, ai baki ga shegu duk mazajen su basu kudi be ba, hatta Zehrah da Balkisu, naji ance mishi duk masu kuɗi suka aura, Inayat ce bana kaunar naji ta auri me kuɗin nan." Haka suka yi ta zagin mutane, tare da kulla sharri son ransu, tare da alwashin ganin bayan Inayat da Yan uwanta. Sannan suka fito, inda suka tsayayyawa Baban su INAYAT kunu a wani ƙaramin kofi, suka dagwara mishi , sannan suka yi wucewar su.
      ***
A hankali take tafiya, Ni kuma sauri nake na fita daga mall din, sabida Ishaq yana jirana, banje juna muka yi lokaci guda wayar mu ta fadi, da sauri na dauko mata nata na mika mata sannan na dauki nawa. Ban tsaya kallon fuskarta ba nayi ficcewata, bin bayana tayi da ido, sannan ta ja tsaki... Ni kam kuyi min afuwa 🙏🏼🙏🏼🤦🏽‍♀️

KOME DA LOKACIN SA {COMPLETE}✓Where stories live. Discover now