Chapter 30

1.4K 168 20
                                    

*_KOME DA LOKACIN SA_*
  https://my.w.tt/xAclmmBiXab
            Chapter 30

I think if you do something and it turns out pretty good, then you should go do something else wonderful, not dwell on it for too long. Just figure out what’s next.
Koda na shiga d'akina, kiran Khady nayi na labartar mata kome! Kai ban tab'a ganin b'acin rai irin na ranar ba, ban tab'a ganinta cikin damuwa irin na ranar ba, tayi min fadar da ko Mamah idan tana raye ba zata min ba, sannan ta kawo min misalai da yawa akan halin da nake ciki, da kuma yadda Mamah tayi tarbiyyar mu, ko sau daya ta taɓa nuna mana mu wulakanta baban mu, yadda take maganar sai naga tabbas ban kyauta ba, dan haka nayi kokarin bata hakuri amma ina tayi fushi. Haka nayi ta damuwa akan halin da nake ciki, har dare. Bayan nayi sallar isha na daura da shafa'i da wutiri, sannan na kama yaran nayi musu wanka tare da saka musu kayan barci. Na kwanta a tsakiyar su, ina nazarin abinda na aikata yau. na jima a gurin kafin barci yayi gaba dani. Tunda na fara barci nake wani irin mafarki, na firgici amma dake kafin nayi barci ina azkar, sai ban ji tsoron mafarkin ba sai dai yadda naga wata mata da MALIK, hannunta cikin jini, tana rike da wuyar shi ta hana kowa kusantar inda ya ke, ya sani firgita har zan farka Naji kamar an danne ni, sunan Allah na shiga kira, ba kakkautawa, sai ji nayi an d'agani, a hankali na bude Idanuna naga kofar dakin a bude, mik'ewa nayi cikin addu'o'in niman tsari, na shiga ban daki nayi alola ina fitowa na kuna wutar lantarki dake d'akin,  karfe biyu na dare, yadda sallar nafilla nayi, ban fasa ba ban kuma daina ba, har karfe uku saura na mike akan abin sallar na koma gado, na jima ina tofawa yaran addu'a, sannan na kwanta, zuciyata ta samu nutsuwa, babu wani abinda zai dame ni... Washi gari har sai da na kusan makara, dan kafin na tashi bar masu kula da yaran sun zo sun dauke su, ina barci. Jijjiga ni Anoosh yayi tare da cewa. "Ammah aduwa!" Da sauri na bude Idanuna, na kamo kan shi nayi mishi Addu'a sannan na kira Anoosha itama nayi mata, kafin suka fita. Na koma na kwanta yau sai karfe biyu nake da aiki dan haka na kuma mai da kai naja Ragona da tushe. Tunda bani da fitar wuri.
     ***
LONDON
Kura mata ido yayi, suka kwance. Ta wani narke a jikin shi, ga zafin da jikinta yayi, duk ta sake mishi har tausayi ta bashi, sai dai haka ba zai hana shi niman mace da zata bashi abu uku ba. Juriya a gado, abincin da zai rike tumbin shi sai kuma haihuwa. Su abinda zai sanya ya nimo Inayat! Dole ya karasa cin Sadakin shi. *Haba Malam ka ci sadakinka da?* Wani bata rai yayi kamar yana magana da wani ne, har da hararar gefen shi.  A hankali yace . "Wannan da magani nayi shi so nake naji yadda kalar ta yake." Yadda yayi maganar a sanyayye sai ya baka tausayi. Sai da yayi dogon nazari kafin ya, yanke shawarar karshen sabon shekara, Insha Allah zai tafi yaga Ammyn shi. Dan yana matuƙar kewar shi, janye jikin shi yayi daga na Zeeh, ya zauna tare da kunna asalin wayar shi da yake da number yan gidan. Ya jima yana kallon yadda take yi kafin ta kawo wuta, hostpot ya bude na wayar sannan yayi connect din shi da wifi na gidan, abin da ya fara dubawa sakonin gida, tare da hotunar kanen shi, a hankali ya rubuta a Status din shi na Whatsp. *Ina kewarku! Ina kewarta! Sosai!* Tweeter ya duba yaga rubutun Ammyn su, murmusawa yayi sannan ya kuma duba sakon Hajnan! Kafin ya bude sakon, yaji an kwace wayar tare da kallon shi, wurga wayar tayi a cikin ruwan da yake glass cup, juyowa yayi zai mata magana ta kwantar da kanta a kirjin shi. Dole ya hakura, ba dan kome ba sai dan wata Mahaukaciyar hikimar da aka musu, wai zata iya daukar ciki. Shine aka kafa mishi sharudda, wanda ita ta sanya likita ya kafa mata, ba wai likitan dan kanshi ba, asalima ta kirkiri wannan al'amarin ne dan ta raba mishi hankali gida biyu., Kuma hakan ya faru, sai dai ko sati ba ayi ba ta soma zubda jini, dole suka nufi asibiti, koda suka je aka ce mahaifar ba zata iya rike d'an ba komi kankantar shi, dan haka ya haifar mata da zazzabin da ciwon jiki tare da cikinta zuwa mara.  Kwal kwal tayi mishi da ido ya bude mata hannun shi ta shiga jikin shi. Dake tana yawan shiga damuwa yasa likita bashi shawara a karo na biyu, da ya bata lokacin shi sosai, domin haka ce zata rage mata raɗaɗɗin da take ji na rashin haihuwa. Haka dai suka kasance har yamma likis, sannan ya dauke ta suka fita yawo,tun a gurin shan shayi taga wata baturiya, tazo kusa dasu, tana kallon MALIK. Har zata wuce sai ta dawo tace mishi. "Mr MALIK Aliyu! Kaman kaine naga BBC sunyi hira da kai ko?" Murmushi yayi sannan ta mika mishi takarda ya saka mata hannu, zuciyarshi daya ya amsa tare da saka mata sannan suka kuma gaisa tare dayi hoto. Wannan abun yayi mugun bakantawa Zeeh rai dan haka ba tare da suna ganinta ba, ta dauki daya daga cikin kofin da suke gurin ta saka a kasar tabirin, tayi ta kwalawa gwiwar ta, har matar tayi tafiyarta, sannan Malik ya nufi gurin biyan kudin coffeen da suka sha. Koda ya dawo ya mikawa Zeeh hannu, ta mike tana d'aga kafa daya ta nemi zuɓewa kasa,r daukarta yayi tare da nufar gida, dukda tana jurewa bata son ya fahimci halin da take ciki, bai hanata jin ciwon gwiwar ba, dan ji take kamar kafar ba nata bane, suna isa gida ta fito daga motar abu ya gaggara. Dole ya duba gwiwar ta kumbura, kallonta yayi cikin nutsuwa sannan yace mata. "Me kika aikata?"  Kallon shi tayi na wani lokaci, kafin ta kauda kanta hawaye na zuba, juyawa yayi suka nufi asibiti, dakyar aka mata gyaran gwiwar da kokon gwiwar ta goce baki daya. Koda suka dawo gida, nan ta samu damar juya shi sosai. Domin shi yake mata kome, minti ɗaya zata fara kiran shi, ga aikin shi, a lokacin suka kuma dinkewa da Tabawa inda ta buge da koya mata girki tana baza sharri a gidan tare da saka ido, akan damuwar MALIK. Ranar ya dawo da yamma, ya zauna a falo ya kalleta yace mata. "Baby! Mamar baby. Allah ya bamu Haihuwa koda daya ne mu samu." Dai dai tabawa zata shigo gidan kenan, dan haka ta tsaya na wani lokaci, kafin taji Zeeh ne kuka. "Ince kaga bana Haihuwa shine kake gaya min magana, na gode." Wani tsallen dad'i tabawa taji, "Dama na gaya miki kome da lokacin sa, yanzun lokacina ne. Zaki ga yadda Sa'ida zata zo tayi ta Haihuwa." Dan haka ta juya tabar gidan ya nufi gidan Lilih ta zauna a gaban Lilih ta koro mata jawabi. Kallon Tabawa tayi, tare da lumshe idanun ta, ta jima tana wasu sambatu, kafin ta bude idanunta jajjur. Har da ruwan kwalla, muryanta na rawa tace. "Karki tura Yarki da kika daura buri akanta rayuwar Malik! Domin matar shi tayi nisa, kuma zata iya kashe ta, ba tare da kin mata kome ba, ki kyaleta lokacin ta ne, tana tab'a kowa zata tab'a wanda zai dame ta, domin akwai burin da ake niman tagazawar wata akai, sai dai al'amarin da kamar wuya domin Malik ya samu abinda yake nima. Ki rabu dasu. Karki saka rayuwar Yarki cikin damuwa, ki barta zata sami mijin da zai sota koda bai kai Malik ba arziki ba." Dake tayi imani da matar, domin kuwa Zeeh tayi nisa djinn suna tare da ita masu masifar taurin kai, karki kai Yarki gurinta, dan zata kasheta ta kashe banza." Godiya Tabawa tayi mata, sannan ta juyo zuwa gida taso ta kure Iskancin Zeehmalik..

KOME DA LOKACIN SA {COMPLETE}✓Where stories live. Discover now