Chapter 36

1.1K 125 9
                                    

*_KOME DA LOKACIN SA_*
 https://my.w.tt/Twv71uXZ3ab
            Chapter 34

There are two powers in the world, one is the sword and the other is the pen. There is a great competition and rivalry between the two. There is a third power stronger than both, that of the women.

Ina kukene maza da Mata masoya kasuwanci, ga dama ta samu! Nesa tazo kusa! Ina masu sayan d'ai d'ai ko sari karku sake a baku labari, da arziki a garin su har gwara a garin mu, kai gwara a  dakin mu, karku sake wannan damar ta wuce Ku
Ku garzayo kampanin *Greenleaf biotech* domin ya tanadar muku kayayyaki sama da guda 4500, Kama daga abubuwan amfanin yau da kullum kamar sanitary pad, pampers, baby wipes, sabulan gyaran jiki, man shafawa, magungunan qarin lafiya da magance cututtukan zamani kamar (infection, BP, diabetes da sauransu), kayan kwaliyya, sinadarin rage kina da tumbi, takalma, jakunkuna, air frying pan (baya buqatar Mai wajen suya) da ma wasu da dama.

Zaku iya siya domin amfanin kanku da iyalan ku, sannan kuma zaku iya yin sari domin saidawa ku samu riba me albarka.

Domin qarin bayani ku biyo mu ta wannan link din👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

https://wa.me/message/XMECES32SQEPK1

Ko ta WhatsApp group👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
https://chat.whatsapp.com/BebpPIrkAPj1bfiqfZkkjH

    ~~~~~~~~~~~~~~~~
Rike hannunta yayi da karfi kamar zai b'alla ta, ta kuma rike maganaɗisun shima ya kuma damke hannunta, tana shirin murɗawa shima ya murɗa hannunta, kamar zai ƙaryata, aikuwa ta ci da zuci, ya kai mata duka a cikin ta, dan tana shirin kashe shi ne. Faduwa tayi ya mik'e tare, nufar gurin kayan kallo ya zare wayar wuta ya shiga zane ta, tashi tayi suka kama dambe kamar sa'anta, duk da yana dukarta amma bakinta bai mutu ba, kuma bai fasa dukarta ba, bata kuma fasa janyo mishi jarfa ba, sai da ya ji jikin shi na ciwo. Ya yar da bulalan ya barta kwance tana kuka tana haki tace mishi. "Ba dai akan wancan ƙaruwar ka dake ni ba? Wallahi sai na kashe ta har lahira, baka san wacece ni ba."

           "Banza dake meye amfanin saninki keda baki da hankali. Sha-sha-shar banza sha-sha-shar wofi, idan kin isa ki tun kare ta, Inayat ba matsoraciya bace Ni kaina bata kyale ni ba, balle ke din banza. Idan kin isa mace ce ko tari Inayat.".  "MALIK Ni kake ciwa fuska?" Ta nuna kan ta, cikin gurnanin kamar zaki.  Takowa yayi gaban ta yace. "Me kike tsammanin zan gaya miki? Nace miki don Allah karka illatata? Toh bari na gaya miki kowa ni dakika soyayyar Inayat kara samun mafaka yake a zuciyata! Kinga nan." Ya nuna mata kirjin shi, "yana bugawa ne a duk lokacin da na ambaci sunansa? Wallahi kika Kuskura kika mata wani shirme sai na wulakantaki kamar yadda kika wulakanta Yaran Jama'a a kaina banza sha-sha-shar wofi wacce ba Allah a cikin zuciyarta. " Yana fadar haka ya bar mata falon. Wani irin kuka ya kwace mata tare da dukar Center table. Ta mike ta shiga wurgi da kome, tana fasawa. Kitchen ta wuce da gudu, ta dauko wukarta sabuwa fil ta shige da mugun gudu. Garin haurawa step kamar wacce aka ja kafarta ta fado daga sama, sai da wukar ya caki kafarta, wani irin ihu ta saka.  Yana jinta, amma yayi banza da ita, wanka yayi sannan ya fito ya shirya cikin dark green shadda, ya fito da sauri a bakin step ya ganta tana kuka, bai ji tausayinta ba, dan yanzun abubuwan da tayiwa Yaran mutane yake dawo mishi, yana ji yana gani ta kashe yar mutane a Mall kuma ya wanketa da arzikin shi. Yayi imani da Allah wutar shi na daban ne, domin ya san gaskiya ya take ta, ba tare da uzuri ba, wukar na cikin kafarta, zama yayi tare da shafa kanshi. " How you feel The pain?" Hawaye hade da majina suke kwaranya a fuskarta, sake danna wukar yayi ta fasa ihu, "kamar haka yarinyar da kika kashe a Mall taji, kamar haka yarinyar da kika watsawa ruwan battery! Taji kin san me yasa kike abin da yayi miki? Sabida hakokin jama'a dake Kanki. Wallahi idan kika bari na ji a raina zan dawo da Inayat rayuwata, hmm" sannan ya mike tare da dauko wayar shi ya kira motar asibiti. Su zo daukar Matar shi da ta hau bishiyar kace.
              Gidan da Inayat take ya nufa, inda yazo yayi parking da motar shi, yana jiran fitowar Inayat, tun yana cikin motar shi. Har ya gaji ya fito, ya tsaya gashi ko rigar sanyin bai dauko ba, ya fito haka, daga shi sai shaddar jikin shi. Bayan minti goma sha biyar, sai gasu tare da Mahir! Akan bike da gayya na rungumo bayan Mahir tare da kai kaina kafad'arshi, ina dariya kasa hakuri, yayi da mugun sauri ya tawo inda muke ya fincikoni ban gama sauka a mashin din ba, ya d'aga hannu zai mare ni Mahir ya rike shi. "Malam meye matsalar ka da mu? Zak...". Kan Uban bala'in can, naushi Malik ya kai mishi duka. Nan dambe ya nemi kacamewa a tsakanin su, na shiga tsakiyar su. "Malam ban san ka ba! Ban san waye kai ba. Don haka ka rabu dani! Nayi rayuwata da wanda suke bukata na..." Fincikoni yayi tare da kura min ido! Jikin shi na rawa, dai dai lokacin Dr Ishaq ya iso gurin. "Ke har kin isa ki hana magana akan ki?,". Cike da tsoron shi na fincike hannuna daga nashi nace mishi. "Kai din banza! Kai din wofi! Waye kai har ka isa hanani rayuwata! Baka isa ba Malik , wallahi baka kai ba, idan kuma kana ganin ka isa bismillah!" Na faɗa da karfi ina huci. "Ni kike d'agawa muryan?" "Kai waye da bazan d'agawa murya ba?" "Inayat!!!" Ya daka min tsawa, Sai da hanjin cikina ya juya, na kura mishi idanuna wanda suke cunkushe da abu biyu, tsoro da tsiwa. Huci yake nima ina hucin, zan juya mu bar gurin ya sake fincikoni tare da hada bakin mu, lokaci guda kome ya nemi dauke min. Sakamakon jin bakin shi cikin wannan, wani irin yanayi naji a lokacin Dr Ishaq ya juya zai bar gurin. Sabida zuciyar shi tana bugawa kamar zata fado. Haka kuma Mahir wanda ya gama sarewa da Malik, shima ya juya zai bar gurin na riko hannun shi tare da kwace bakina. "Iya wannan kasamu daga gare ni! Har abada ba zaka kuma samun wani ba, dan na haramta maka har duniya ta tashi. Ka fita a rayuwata bana bukatar ka, Malik me na tsare maka? Meye nayi maka? Bana son ka, ban tab'a jin soyayyarka ba, Malik ka rabu dani dan wallahi zan maka abinda baka zata ba." Daga haka na ja hannun Mahir muka shige cikin gidan, muka bar shi a gurin tsaye, ina shiga cikin gidan na wuce d'akina, ban daki na fada tare da kunna ruwan wanka na fashe da kuka, sosai kamar zan fadi tare da budewa kara karfin ruwan a kaina, ina kuka ina kome. Brush na dauka tare da wanke bakina ya kai sau goma.  Kafin na fito na zauna na shafe jikina tare da gyara gashina.

         .... Bayan kwana biyu, ina ganin shi kullum zai zo, ya tsaya a kofar gidan. Bai tab'a samun damar tsayar dani ba, sabida bana kula shi wani lokaci Dr ya rako ni, wani lokaci kuma Mahir. Malik ya fita hayacin sa, fiyye da yadda ake tsammanin, matar shi kuwa tana asibiti. Ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon Dr Ishaq. "Ishaq! Na san nayi Kuskure. Amma ka taimaka min na sameta a karo na biyu mana! Don Allah!" Shiru yayi tare da zuba mishi ido, kafin ya gyara zama yace. "INAYATU RAHMAN! Bata da riko, kai ne baka san yadda zaka lallabata ba, amma bata da Matsalar kome! Kuma duk abinda ya faru, sabida laifinka ne! Da ace tun farko ka nuna mata kulawa, a ranar da kayi mata laifi da zata saurare ka, da ace ka waiwayeta da babu abinda zai hana bata saurare ka ba, yanzun kuwa tana kulace da kai ne! Kayi hakuri amma samun Inayatu ba a bu me sauki bane dan shine abu mafi daraja da zaka iya rasawa! Ina gaya maka haka ne a karon farko da na karshe." Mikew Dr yayi zai bar gurin ya riko hannun shi, tare da magana cikin budadd'yar murya yace. "Kace min kun shirya min mugunta shi yasa kake gaya min ba zan same ta ba. Meye nufinka da Ni?" Kallon juna suka yi sannan Ishaq yace masa. "Ina son ta ne? Tun a karon farko ka fahimci Ina son INAYAT! Amma son kai Yasaka dakile ni, yanzun kuwa zan iya hakuri da kome ban da Inayat! Don Allah ka rabu da ita kamar yadda ta roke ka."
      "Ishaq! Yaushe ka zama mara adalci? Yaushe ka zama me mugun son kai ne?"  "A'a! Malik kai ka koya mana! Kaine ka nuna mana hanyar yin maka haka, wallahi da baka raba mu ba, da yau muna tare da junar mu! Amma rabo da ƙaddarar, shi yasa lokacin ban kuma shiga tarihin abin da kai mana ba, tunda ka datsi ƙaddarar mu. Kayi tafiyar ka, tunda ka fahimci Inayat bata da arzikin da zata iya rike yaranka, itama ni da sauran dangin mu sa bamu da arziki mu rike ta? Ina son Inayatu Rahman! Ina kaunar Inayatu Rahman! Malik Kayi wasa da damar ka, yanzun kuwa damar da muke dashi dai dai yake da.." "baka isa ba! Baku isa ba. Wallahi kunyi kadan ku tozarta ni. Wallahi ko da karfin tsiya sai na kuma rayuwa da Inayat! Mu zuba mu gani!" Daga haka ya saka kai ya fita a dakin Ishaq din. Wannan rikicin shi ya kuma ririta alamarin ya girmama, ya zamana Malik ya saka mana kahon zuka, ba halin mu fita da Ishaq yana bin mu, kuma suyi ta faɗa kamar wasu yara. Haka a gidan shi matar shi da ta gama jinya itama ta shiga layin bala'i sabida yawan ganin mu da mijinta. Haka ya kara ririta mata tashin hankali, har take ji gwara ta kashe ni ta huta, yau mun fito daga aji ina takawa a hankali, dandazon dalibai na gani ana ihu, cusa kaina nayi naga ashe wata mata ce suke wani wasa, dan haka na cusa kaina ina murmushi, tare da zuba musu ido. Na dan sunkuya zan dauki abin da suke yi kawai naji wata ta fasa ihu, lokaci guda muka d'ago kai. Dai dai juyawar wata mata, rike da wata kwalbar ruwa a hannunta ban san lokacin da nabi matar ba, har ta shiga motar da ya kawo ta. Take yanayin fuskar matar Malik ya zo min wato Ubangiji ya kare ni ne, duk yadda aka yi ni aka zo watsa min aka watsa mata a fuskarta, jikina ne yayi sanyi na koma aka nufi asibiti da ita, tabbas matar Malik ce, da yan sanda suka zo ni ce na bada shaida. Na kuma bada Number motar da ya kawo ta, sannan na bar gurin. Na dawo gida. Ina gayawa Ishaq a waya, fada yayi min Sosai akan me zan saka rayuwata a hatsari. Ban kuma cewa kome ba, na bashi hakuri tare da cewa ba. Na kashe kiran ina bashi hakuri.

      Ina zaune a daki Mrs Muhmood ta shigo dakin tare da cewa. "Inayat kizo kinyi bako!" Kallon ta nayi sannan nace mata. "Aunty ba kuma Ishaq ba??"  "Kizo dai, ki gan shi." Ta faɗa min haka. Mik'ewa nayi na yafa mayafi, na fito. Kallonshi  nayi tare kauda kaina, sannan na juya zan koma dakin ya taso tare da riko hannuna. "Abin da ya faru a makarantar koyar da ilimin rayuwa! Kuskuren ne, ki taimake ni ki janye shaidar da kika bada, akan Mata na, ki janye sabida bana son tashin hankalin da zai faru dake, nasan wacece matar da nake aure. Ta kashe mutum akai na ba abu me sauki bane! Shi yasa nake baki shawara ki rabu da kanki cikin damuwar mata ta, please ba dan tsoro ba, sai dan Aliyu da Rukayyah!"
_Anya zata saurare shi kuwa? Kuyi hakuri bamu da wuta ne! Amma Insha Allah na sami power bank, banyi alqawarin baku da dare ba, wasu dalilai. Indan kome yayi Kyau zaku ji.... Thank You 🙏🏼💋

KOME DA LOKACIN SA {COMPLETE}✓Where stories live. Discover now