Chapter 9

1.3K 145 14
                                    

*_KOME DA LOKACIN SA_*
   https://my.w.tt/TgIw7a4Byab
            Chapter 9
        MrsUsman400

*Wow Zeemalik team members thank You for The comments  💝💖💋 I'm think that Kome da lokacin sa! Zan iya ce mishi Super hit story👻*

"Kana hauka ne? Matar tawa make dangantawa da shashin binciken ƙwaƙwalwa! Zaka bar asibitin nan how are you! Da zaka danganta Matana da cutar hauka."
"Yallabai! Ba haka bane, listn to me, Matarka tana dama da cutar birkicewa ƙwaƙwalwa ne, shi yasa take iya cutar da kanta, and nan gama zata iya kirkiro abu tace ya faru, kuma bai faru ba. Cutar tayi tsananin dayawa, tun ba yau ba na fara nazartan matsalarta. Idan ka kawota ta had'iye wani abu me kaifi!"  Cikin mamaki ya zubawa Dr Tony ido, ya tako gaban shi sannan yace mishi. "Ka gama aiki a cikin asibitin nan zaka barshi." Duk yadda likitan yaso fahimtar da shi, abun yaci tura, a fusace ya fita daga ofishin likitan ya nufa dakin da Zeemalik take Barci in peaceful! Shafa kanta yayi tare da kallon agogon karfe goma saura. Gaban shine ya fadi lokacin da ya tuna ya bar Inayat a kwance, kuma bai gayawa kowa ba, cizon lips din shi yayi. Sannan ya lallubi wayar shi, ya fara niman layin Dr Ishaq, bai dauka ba, sai dai ya tura mishi sakon kamar haka.
_Ka tura nurse suje su daukota domin na gama abinda zan yi da ita! Ishaq Abdul Qadr! Karka kuskura ka dibo that poor lady ka kawo ta gidan mu, domin idan Zeemalik ta ganta babu abin da ya dame ni, idan ta gadama zata iya cigaba da aiki a Mai Nassara clinic, kai dalla waye ita kawai ku dubata idan bata mutu ba kayi watsar da ita a bakin hanya, kayi tafiyarka, ita ta sani, ni zan bar kasan yau dan mata na bata da lafiya_ Cikin nutsuwa ya cire layin Dr Ishaq ya karya bayan sakon ya tafi, sannan ya koma kan Zeeh yana shafa kanta cikin yanayi tausayinta.  Fita yayi daga dakin ya samu wasu likitocin suka shiga hada musu takardun shaida lafiyarta, zasu wuce wata asibitin a garin London. Kuma dama reshen kamfanin shi na sarrafa magunguna yana can. A cikin awa biyu aka gama hada musu kome, sai da ya shiga private Jet din su, sannan ya turawa da Ammin shi sakon basu ƙasar shi da Zeemalik ba lafiya. Kai hannun shi yayi ya shafa kanta, fuskarta yayi fayau.
_Toh ya kenan duk ranar da Zeeh dinka tasan kayi aure a wata duniya fa?_ dafe kirjinshi yayi cikin tashin hankali tare da tirr da Inayat, duk ita ta janyo mishi wannan masifar, kai shi kan zuwa gombe bai amfane shi ba, sai masifar da ya jangwalawa kansa. Cikin zuciyar shi yake jawa Inayat jafa'i yafi kwando dubu...
              *** Yana dab da zai shiga cikin gidan shi, yaji sako ya shigo mishi. Yana dubawa ya sakon cikin tashin hankali ya juya da motar da mugun gudu, tsabar yana hada kashi mutane sai zagin shi suke, ana gaya mishi magana ba haka bane a gabanshi. Kamar mahaukaci haka ya isa Estate din, a gigice ya shiga ƙoƙarin shiga gidan.
     Masu gadi suka so hana shi sai da ya gaya musu akwai mara lafiya a cikin gidan Malik. Dan haka suka bishi, koda suka shiga cikin gidan ya wuce master room din Malik. Daga bakin kofa ya tsaya sabida yadda yaga gashin kanta ya buzu a saman pillow, fuskarta na kallon sama, da sauri ya kira metrol Sis Rukayyah.
      Wani irin bakin ciki yake ji kamar zuciyarshi zata fashe ya karanta sakon yakai sau goma, can sai ga motar asibitin da Sis Rukayyah, suka shigo ita da Abidah da sauri suka shiga dakin, d'ago kanta suka yi. Suka ga ya koma baya. "Dr Ishaq ka shigo fa, domin bata numfashi fa." Da sassafar ya shigo kamar zai zube kasa, ya ma rasa yadda zai yi da ita. "Metrol kawai ku kintsata mu tafi asibitin." Ga baki daya suka rasa yadda zasu yi da ita, karshe kallon shi suka yi Abidah tace. "Dr babu kayan da zamu saka mata."  Cikin wani irin zuciya yazo ya dauketa cak ya fice da ita, Yarinyar da yake dab da furta mata kamar so! Yarinyar da ya gama jingina burin shi akanta, yarinyar da yake mata kallon macen da yake so! Itace yau a matsayin matar Aminin shi! Abokin shi. Itace Amininshi yayi mata sassari da auren shi. Wani irin zalinci Malik ya shiryawa yarinyar da babu ruwanta. Da wannan tunanin ya sakata a cikin motar, sannan ya shiga motar shi, ya zauna. Motar asibitin tana gaba yana bin su har cikin asibitin. Inda ya hana kowa tab'ata shi da kan shi ya shiga da ita har cikin emergency room, tare da metrol da wasu Nurse har uku, suka shiga duba ta. Kasa zama yayi tunda ya sa mata ruwa da kanshi ya fita, dan ba zai iya zama yaga halin da take cikin ba. Dan ya fara jin abinda Dr Umaimah take fada.

           "Gaskiya wanda yayiwa Inayat Ahmad wannan cin zarafin yayi yawa, haba jama'a dabbancin yayi yawa  wallahi, kalli yadda gaban yarinyar nan yayi, haba don Allah sai kace ya samu jaka. Don Allah taya zan dinke  jikin yarinyan don Allah. Ni kam ban san ya zan dinke ta ba, don Allah kai Allah ya isan mata." Tana aikin fada, Metrol sai da ta shiga zubda kwalla, sabida yadda gurin ya kumbura sosai. Sai da suka cire tausayi suka mata dinkin sosai, sannan suka mike a hankali bayan sun shifa mata cream. Tattara mata gashin kanta Abidah tayi sanan ta tufke mata shi, suka turata wani daki. Dr Ishaq yana tsaye suka wuce da ita, fuskarta yayi wani irin.

              ---
Sallamar shi na biyu Zehrah ta leko, kallon shi tayi sannan tace. "Kamar na sanka, ka tab'a kawo Aunty a motar ka." Murmushi yayi sannan yace mata. "Eh ni ne, Dr Ishaq. Idan da hali ina son ganin Mamanki!" Kallon shi tayi cikin tsoro. Zata yi magana yace mata " Please" shiga tayi cikin gidan jikinta a sabule, ta kalli Maman su kafin tace mata. "Wannan abokin aikin Aunty yana waje, wai kizo." Kallon ta tayi kafin tace mata. "Toh!" Zuciyarta yana wani irin bugawa, take tasoma jin numfashina yana kaiwa da komowa, da sauri sauri. Hijab ɗinta taja, daga bakin kofar ta. Ta fito jiki a sanyayye. Ta d'an leko tana kallon shi kafin tace mishi."sannu bawan Allah."  "Hmm!  Mamah gashi dare yayi, ko zaki zo muje asibiti Inayat tana can bata san waye akanta ba." Yace mata a hankali. Kasa magana tayi sabida rudewar da tayi ta ma rasa inda zata saka ranta kiran Nusaiba da Balkisu, sai Mariam da Aura suka fito tace."muje!"  Kallon yadda ta rufe yayi ta kasa amsawa yaran tambayar da suke mata. Sai dai tace musu. "Muje" a hankali suka shiga motar shi, duk ya kwashe su. " Ya Allah! Mun tuna da wulakanta amanar da ka bamu, Ubangiji ka taimake ni kar Inayatu ta rasa rayuwarta, ban san me zance maka ba." Sai kuma ta rushe da kuka. "Yana daga cikin dalilan da matan kabilu suka fimu nesa ba kusa ba, Iyaye matan sukan sadaukar da Rayuwar su domin yaran su, duk abinda d'an zai yi bazai tab'a mantawa da Mahaifiyar shi ba, amma ku Allah ya wanke ya baku Ƴa ta gari, kuka wulakantata, kuka ci zarafin ta, toh kuje kuga nakasar da kuka ja mata. Idan Allah ya kare lafiyarta." Daga haka yaja bakin shi yayi shiru, har suka iso asibitin, ya kai su dakin da take. Gwanin ban tausayi, gashin goshinta yayi luf luf, ya kwanta. A hankali zaka fahimci tana fidda numfashi, idanunta da bakin ta sunyi jajjur. Sai gefen fuskarta da ya kumbura ga shaidan hannun da ya fito sosai. Dukkan su kuka suke tare da jin tashin hankali, dan gani suke kamar ma ta mutu. Haka suka sha kukan su, anyi anyi su bar Asibitin suka ki, dole aka bar su a bakin kofar ta, kowa na barci amma ban dasu, karshe ma shiga dakin suka yi dukkan su, suka zuba mata ido. Mama da Maryam suka shiga ban daki suka dauro alola, suka fara nafilla, har zuwa asuba. Sannan suka daura da raka'atul fijri, kafin suka yi sallar asuba. Zama Mamah tayi ta shiga addu'o'in. Har rana tayi, tana kuka tare da nimawa Inayat sassauci. Dan haka tana idarwa, tacewa su Balkisu."maza ku koma gida, nasan yanzun babanku yana can yana fada, don Allah ku gaya mishi halin da take ciki a nutse, sai ku tawo mana da kayanta, sannan ku biya ta gidan Uwani akwai kudin adashena ta baku, insha Allah zan tsayawa Inayat ba zan kuma barin wani abu ya tab'ata ba." Fita suka yi tace Nusaiba ta zauna. Bayan fitar su. Gadon da Inayat take kwance ya shiga jijjiga, kamar ana jonata da wuta, har sai da Metrol suka zo suka mata allura, sannan ta koma ta kwanta idanunta a kafe, wani irin ajiyar zuciya taja bakinta yana wasu yana motsi, kai kunne Metrol tayi. "Allah kana ganin abin da yayi ya Rabbi Kabi min hakkina" a hankali kuma tayi shiru tare da lumshe idanun ta, bayan ta sauke ajiyar zuciya a nutse.  ** A gida kuwa su Balkisu suna isa Baban su ya nemi zai musu magana, Zehrah tace."toh daga asibiti muke Aunty Inayat ta mutu." Sake karfen duga yayi akan kafarshi ba tare da ya fahimci akan kafarshi ne ba sai da ya fasa mishi babban d'an yatsar shi ya sake salati tare da  durkusawa. Jini na zuba sosai,  kasa jure abun da Zehrah tace ne ya kalleta. Cikin raunin murya yace mata."toh yanzun batun ginin gidan da tayi kusan dai dole dani a cikin gadonta. Sake baki kowa yayi sabida a farkon abin sun zata nadama ce tazo mishi sai da ya tona kan shi sannan suka fahimci ai hali a jikin rai ne, babu mai sauya maka sai Allah. Dan haka wasu suka shiga gyara dakin su, Balkisu da Maryam suna cikin dakin su. Zehrah ta hura wutan abinci. Sai lokacin mutanen gidan suke tambayar su lafiya, nan suka gayya musu basu da lafiya, take suka juya kan Babansu Inayat da cewa. "Kai ma malam yarinyar nan kamar wacce ta tsare maka wani abu, gashi nan ta haɗa da wanda zai lashe ta. Tunda ai kace mutumin attajiri ne, waye ya sani ko dan yan kankai ne." Inji Jumalo, nan suka yita tsagalgale shi, tare da ganin laifin shi., Kallon shi su Balkisu suke babu wacce ta kuma magana,... A can asibitin kuwa, har yanzun bata farka ba, dan gabaki daya, suma likitocin sun sare da ita, sai da aka shafe awa goma sha biyar, kafin ta shiga ƙoƙarin farkawa. Duk suna bakin kokarin su, amma sai da suka so razana, domin tana buɗe idanunta zata kuma maida shi ta rufe. Komawa har....👻

KOME DA LOKACIN SA {COMPLETE}✓Where stories live. Discover now