Chapter 10

1.3K 150 14
                                    

*_KOME DA LOKACIN SA_*
        
https://my.w.tt/6rcnMVdfAab

            Chapter 10
    Na MrsUsman400

"Dr Ishaq! Har yanzun numfashinta yaki." Inji Dr Umaimah, wacce take ƙoƙarin ganin numfashin Inayat ya dawo dai dai, cikin ikon Allah dakyar numfashin ya dawo yadda ake bukata allurai suka zuba mata a drip ɗinta, sannan suka fita jan kujeran yayi ya zauna. Daga jiya zuwa yau ga baki d'aya ta motse kamar ba ita ba, sai dishewan da tayi. Kar'ar hancinta ya fito zirr. Sai kwarmin idanunta da suka fada kamar wacce tayi jinyar shekaru. Kamar wanda aka tsikare shi da allura. Ya fita da sauri dan bai ga amfanin kallon matar da bana shi ba. Yana fitowa ya kalli Mamah tana fama da share kwalla. Kamar zai mata Magana, sai ya fasa yayi tafiyar shi.  Bayan awa biyar cif. Na bude. "Ƙaf ƙaf!" Naji karar tafiyar agogo, juyawa nayi a hankali na sauke akan agogon da ya ke jikin bangon. A hankali kome yake dawo min daki-daki. Kome yana zuwa min kamar majigu kome na rayuwa yana da mafari kome yana da farko rawa farkon itace kaddarar mutumin da ban sani ba! Tawa mafarin itace iftila'in MALIK!!! Shine kalmar da zuciyata ta ambata, wani irin siririn hawaye ne yake bin gefen idanuna. A hankali na d'an motsa jiki na da yayi min tsami, sannan na lumshe idanuna a karo na biyu. Sannan na bude shi lokacin da naji muryan Metrol Mommy Rukayyah naji na bi kofar dakin da ido, sannan na mai da idanuna na rufe. Duk sun shigo suka gama min gwaje-gwaje ban bude ido ba, ina jin su. Suna fita Dr Umaimah tacewa Dr Ishaq. "Inayat tana fusace tunda bata yi wani abu ba, ka gayawa danginta su kula da abinda zai d'aga mata hankali, dan yanzun tana cikin damuwa sosai."  Shiru yayi sannan ya juya ya sami Mamansu  da Maganar kar a shiga ma yace dan ba abun mamaki bane ya iya birkice musu. Suna cikin tattaunawar sai ga Baban su Inayat. Baza idanu yake yana jiran karin bayani. Itama Maman ce tayi mishi bayanin halin da Inayat take ciki. Kallon Maman Inayat yayi sanan yace mata. "Amma da kuka kawota asibitin kudi kunsan ba shi nake da ba! Sannan kuma ita Inayatun ba haka kowacce mace take hakuri a gidan mijinta ba, ko tallatar kai, ban da lalacewar duniya har guzuma irin Inayatu zata suma sabida an raya sunnah fiyayyen halitta da ita tirr, kuma ina miki kashedi magana na yanan idan kina son aurenki kar naga kafar Inayatu a gidana. Sai ta nimo mijinta, idan ba haka ba toh wallahi a bakin aurenki."  Kad'e babban rigar shi yayi abin shi ya cikawa bujen shi iska. Shiru Maman tayi tana jin ciwon abinda yayi masu, ita bazata iya barin Inayat haka,,, duk abin da yake faru duk naji su. Murmushin tausayin kaina na sake, a hankali nace. "Zan tafi nayi nisa daku, zan muku tazara tsakanin mu. Zan tafi inda ba zaku kuma jina ba sai dai idan nice naso haka.. daga nan na share kwallar da take kokarin zuba min, ina kallon kofar d'akin. A hankali na  d'an mike k'adan sannan na sauka daga gadon. Na shiga ban daki nayi wanka da alola, sannan na fito naga kayana a gefe a hankali nake takawa har na isa gaban kayan na dauki doguwar riga na saka. Sannan na kuma dauki hijab na yafe, salollin da suke kaina nake son saukewa.
*A garin London kuwa Madam Zeemalik ce ta bude idanunta ta zubawa mijinta su, musamman yadda ya d'an faɗa. Kwanaki hudu da zuwan shi ya faɗa sosai, dan wani irin zazzaɓi yake ji. Tun ranar da yayi tarayya da Inayat. Shi kansa yana son ganin likita, amma matsalar Zeemalik ne a gaban shi. Shafa sajen shi tayi cikin jin dadi. Sannan ta ture kan shi kad'an, bude idanun shi yayi tare mik'ewa a hankali yana murmushi yace mata. "zeemalik!" D'aga mishi hannu tayi sannan tace mishi." Wacece ita? Nayi mafarkin wata mace kuma wallahi ina jin ka boye min wani sirri, gaya min wacece ita da take ce maka raggon maza! Ka gaya min wacece ita?" Ta faɗa da karfi, "Kinga Zeeh babu wata mace na gaya miki kallo nayi, kuma a"  cikin fusata tace mishi. "Kayi min shiru! Munafuki, annamimi, wato wannan shine abinda kake aikatawa. Da sunan kayi tafiya, kaje kana sheke ayarka, meye na rage ka dashi wallahi ko ka gaya min wacece ko kuma na kashe ka na kashe kaina. Kuma ina tabbatar maka sai na kwashe maka Manhood dinka, idan baka gaya min ba." Wani irin zufa ke karyo mishi kamar wanda ya shiga ruwan sanyi. Ya bude baki zai magana tace mishi. "Kayi min shiru! Ka kuma gaya min wacece karuwar ka? Na rantse da Allah sai na mata tsarki da ruwan battery, ba zaka gaya min ba!" Yadda take zare ido hancinta na huruwa kawai zai tabbatar maka da ta zare, amma ba zarrewa bane abu ne da take da yakinin ya faru, tsabar kishi ya rufe mata idanu. Shigowar likitocin da suke dubata ya taimakawa Malik ya fita, tunda fita yake zaga cikin asibitin sabida yadda brain ɗin shi ya dauki charger, kacokan ya daura laifin faruwar kome akan Inayat, ita ta shigo rayuwar shi ta lalata mishi kome nasa, gaskiya da zai kuma ganin ta, sai ya kuma mata rashin mutuncin da zai sanya ta gane Allah daya ne. _Amma kuma wani hali take ciki?_  wani shashi na zuciyar shi ta sheko mishi tambayar tsaki yayi a fili yace"oho idan taso ta mutu ma, Insha Allah daga yau ba zan kuma tuna abinda ya shafi Gombe da kewayenta ba. Dan kar wancan farar kazar taji a ranta ina bibiyar ta." A hankali yake wannan maganar,  haka yayi ta zaga asibitin, can ya tafi wani shashi ya biya kome sannan yaga likita saboda zazzaɓin da take bibiyar shi, tsoro ma yake ji kar ya lakato wata masifa a jikin Inayat, wacce zata hallaka shi. Bayan gwaje-gwajen da aka mishi gyara zaman Medical glass din shi yayi sannan yace mishi. "A gaskiya baka da wata matsala, sai dai ta zubar ruwan jikinka, wanda hakan ya faru ne sabida kasha wani abin karin kuzarin, dalilin jimawa da kayi kana biyan buƙatar ka, ruwan da kayi ta fitarwa ya shafi na jikinka sosai. Shi yasa kake jin zazzaɓi. Badan maganin ya sake ka ba da jini zaka yi ta zubdawa, sannan ka kiyayye tare buƙatar ka, itama tana haifar da haka duk ranar da ka fitar da ruwan da yawa haka. Toh kusan hakan ce zata kuma faruwa don Allah ka kiyayye lafiyarka!" Magani ya rubuta mishi sannan ya fita ya saya shima lokacin da ya koma dakin Zeemalik ya sameta tayi shiru, tana kallon kofar, a hankali ya shiga dan wani masifaffen tsoronta yake ji. Kallon shi tayi cikin kuka tare da mika mishi hannu, da sauri ya isa gabanta, ta faɗa jikin shi tana kuka, tare da gaya mishi. "Ina jin tsoron Allah, ina jin tsoron ranar da zaka fada komar wata mace, dan nasan zan wahala, don Allah stay with me!" Cikin tausayinta tare da kwashewa Inayat Albarka ya shiga shafa kanta yana faɗin. "Insha Allah kece Mata ta , a duniya kece a lahira. Bana fatan na miki kishiya har karshen rayuwata." Ya fadi haka tare da rintsa idanun shi, yana jin wani irin ciwo na zalintar matar shi da yayi, "kai Allah ya Isar min ban tafe mi.."  a gigice ta d'ago kanta, idanun ta rau-rau tace mishi. "Meye nayi maka?!".  Shafa kanta yayi sai yanzun ya fahimci ashe a wajen yayi Allah ya isan!.. "Ni da mafarkin da kike yi ne akan kishiya, shine nake tsinewa mafarkin tare da ja mata Allah ya isa, akan lallai." Rufe mishi bakin shi tayi da nata, sun jima a duniyar romasiya, kafin suka tsaya daga nan dai aka dinke ya shiga mata alqawarin duk duniya babu waya sai ita, kuma babu ita babu kishiya, har duniya ta tashi, abun tausayi haka yayi ta mata alqawari kamar babu gobe.
* A hankali sauki yake samuwa, ina kuma kara aniyar barin kowa, ranar da na cika kwana takwas, aka sallame ni. Ina zanje tunda Baba yazo ya saka Mama a gaba sun tafi, dan haka na dauki wayata da yake cikin jakata, na turawa Dr Ishaq sakon. *_Idan ba zaka damu ba ina don Allah ina son kayana zan koma gida._*  shiru shiru har kusan awa daya sai da na tashi a hankali nake tafiya har na isa bakin Office din sa, naji kamar an kira suna na. "Bafa zina bace kuma ba fyade bace, Yallabai ka fahimci wani abu, Ni na amshi aurentawa M. A auren ta, kuma ga sakon shi nan yace a mai data bakin aikinta, matar shi ce dan haka ina ganin ko bata yi aiki da Asibitin ba, dole mu ware mata kuɗin da zata yi ta buka...."  Kamar Mahaukaciya na shiga cikin office din ina kallon su, kafin nace. "Dr Ishaq ina kayana suke? Zan koma gida ina sauri."  Kallona yayi sannan ya kauda kan shi yana faɗin. "Kije ina zuwa!"  "Babu inda zani! Kawai ka bani kayana, dan wallahi matukar baka fito ka bani kayana ba toh tabbas gawata zaku fitar a cikin asibitin, bana kaunar jan numfashi a cikin asibitin mai Nassara, bana kuma fatan na bude idanuna na ganni anan idan ba haka ba wallahi zan muku asarar indai ban kashe kaina ba." Fita yayi na juya gurin MD na asibitin, daukar marke nayi naje gaban kofar da zai kai ka Office din Malik na rubuta. Kome da lokacin sa! Sannan na fita a hankali daga cikin office din, kuka nake dannewa amma bana tunanin zan iya rike shi, dakyar na fita daga asibitin, Na samu Ishaq ya bude min kofa motar shi kauda kaina nayi, sannan na bude bayan motar na dauki kayana, "Amma dai ki min adalci! Meye laifina, kizo zan taimaka mi..." A fusace na juya tare da watsa Mishi harara, "taimako! Taimaka min zaka yi? Sabida ga nakasashiya, wacce bata da amfani, Iyayen ta sun gudu daga gareta, bayan an wargaza min farin cikina, toh dama ai bani da shi, Ishaq bana bukatar taimakon abokin halitta, kaje kaji da damuwar ka." Daga haka na dauki kayana na fara ja a hankali. Biyo ni yayi tare da cewa."Inayat!" D'aga mishi hannu nayi sannan nace mishi."Ni matar aure ce! Nima kuma ban yiwa igiyar dake kaina adalci ba, na haɗaka da Allah ka bar bina, sabida martaban aurena, karka ja min tsinuwar Ubangiji bayan wanda nasha a gurin Mutane nagode sosai da kulawar da kayi min." Daga haka nayi juyawa ta da sauri na bar asibitin, dukda hakin da nake, saboda har zuwa yanzun gurin bai gama warkewa sumul ba, kafin na isa bakin hanya nayi hutawa ya kai bakwa...
Sorry 💖

KOME DA LOKACIN SA {COMPLETE}✓حيث تعيش القصص. اكتشف الآن