Chapter 27

1.2K 160 24
                                    

*_KOME DA LOKACIN SA_*
         https://my.w.tt/k7BxNgYhUab
            Chapter 27
If you want your children to be intelligent, read them fairy tales. If you want them to be more intelligent, read them more fairy tales.

   🤔 '''Zaku karanta labarin ne ko kuma Marubuciyar kuke nima? Idan kuka dame ni da na bayyana kaina! Toh zan ajiye rubutun 🙏🏼 Don Allah ku karanta labarin Na zabi haka ne kawai sabida ra'ayin kaina, ba suna nake nima ba! Rubutu muradina ne! Ba population ba, Please karki dame ni da sai na bayyana kaina! Idan nayi haka toh wallahi zan canza ra'ayina akan labarin! Dan zan bayyana kaina amma ba zai muku dad'i ba! Please karki dame ni da wacece ni🙏🏼🤔'''

Sake damke hannun shi tayi, wani irin mugun kishi yana dabaibayin a cikin zuciyarta, idan ta kama tayi Sacrifice da rayuwarta domin Malik ya zama nata zata yi, a shirye take ta aikata kome dan ya zama nata, dan haka dole tayi iyaka kokarinta gurin muna mishi ta amince, wasu irin fake teas ne suka zuba da mugun gudu, ta bude bakin ta dakyar tace mishi. "Na amince! Insha ALLAH" murmushi yayi domin da yana tsammanin zata botsare mishi ne, sai yaga ba haka ba. A hankali ta rungume shi. Cikin tsananin kishinsa tana hango yadda wata mace ta lafe a jikin shi, rintsa idanun yayi sannan ta kalle shi, tana faɗin. "Bani da kowa sama da kai." "I know, shi yasa nake son ki kama kanki akan damuwa da mutane,.kawai kiyi hakuri da kauda kan ki, akan duk wani abinda zai faru."  "But MALIK!" "Shiii! Silent. Kiyi shiru bana son magana." Sake mai da kanta tayi kirjin shi, tana sauke kwalla, goge kwallar yayi da hannun shi, sannan ya rike hannunta suka bar dakin, yadda ya rungume kafad'ar ta, yasanta relief! Dan ko babu kome ya samu kan shi, na wani lokaci. Daga nan gida suka wuce, koda suka isa, d'akinta ta shiga shima ya shiga nashi cikin sauri ya dauro alola, yazo ya gabatar da sallar la'asar. Ajiyar zuciya ya sauke dan da jin shi yake a uzurce, yana idarwa ya zauna ya fara aiki da laptop din shi, yana shigar da wasu abubuwan, har ta shigo d'akin, kallon juna suka yi, tare da sakewa juna d'an murmushi, tana haurawa gadon ta zauna, kallon yadda gashin kirjin shi ya kwanta luf luf tayi. Tana kuma hango iyakar yadda wata mace zata gigice, idan gargasar jikin shi ya hadu da boons din ta, "Neva! Ba zai taɓa faruwa ba!" Kallon ta yayi tare da zare Medical glass din shi, yana kallon yadda take zare ido, "Lafiya?" Turo baki tayi. Sannan ta kai hannun ta, boxes ɗin shi. Janye hannun ta yayi cikin nutsuwa, tare ɗage mata gira daya. "Ina hutu ne, a barni na gama gabatar da wani project don Allah!" Murmushi tayi, sannan kuma shige jikin shi bayan ta sauke laptop din akan cinyar shi, tana kallon shi cikin wani irin yanayi, janye rigar jikinta tayi wani gown ya bayyana, babu abinda bai fito a jikinta ba,  murmushin mugunta tayi mishi sannan ta kuma matsowa tare da zare zaren da ya rike boons ɗinta, suka kuwa sake kansu, murmusawa yayi. Sannan ya cigaba da aikin shi,  sabida a duniya ba zai kuma ganin boons masu matukar burgewa da daukar hankali irin na Inayat ba, suna tsaye kam. Gashi da laushi kamar auduga, had'iye yawun yayi, cike da takaici zata daddo mishi batun Inayat. Sosai take jan hankalin shi, yana kin biye mata karshe sai da ta kai, da ta lallaba shi kamar me, shi bawai wani abu bane, kawai baya sha'awan alaƙar su tayi nisa a yanzun ne, ba dan kome ba, sai dan yadda yake matukar bukatar haihuwa, kuma da Inayat. Duk da bata da kunya idan ta haihu dashi zai sallame ta ya bawa Ammin shi yarinyar ko Yaron, dan yadda yaga mahaifinta nan yayi imani bawani tarbiyyar arziki zai basu ba, balle ita da take idanunta a soye kamar, penut. Sai kuma ya sake murmushi, abu daya da ya cuce shi a rayuwar shi. Yadda har suka rabu bai sumbaci bakin ranshin kunyar nan ba, yayi imani da Allah, ya sumbaci Bakin da duk wani rashin kunyarta ya kare, yarinyar tayi kome Matsalar ta rashin kunyar da take dawainiyya da ita, ko ina nata ba laifi domin ta isa a kirata da kome Compelet. Shafa shi Zeemalik tayi ranshi ya b'aci kamar wanda aka dodana mishi wuta take mood din shi ya sauya haka yayi matuƙar razanata sai ta kame kanta ta koma gefe, tana share kwalla, duk na yaudara ne, bai sani ba. Gabaki daya sai yaga rashin dacewar abin da yayi mata, karshe ya ajiye laptop din tare da mika mata hannu, da sauri ta zo gurin shi tare da fadawa kirjin shi, kara rungumo ta yayi, a hankali kome yake tafiya. Duk dauriyar da take kokarin mishi sai da ta kasa domin tayi kuka ba kadan ba, kafin ya rabu da ita,yana me sauke ajiyar zuciya, sosai yake jin wani irin yanayi domin bawai ya gamsu bane, kawai yadda take nuna ta gaji yasa shi, kyaleta. Bayan sati biyu.  Sun shirya sosai har suna fita cin abinci, bai hana idan Malik yaga yara a hannun iyayen su yayi musu hidima, abun yana masifar mata ciwo, dan haka ta shiga bin dukkan hanyar da zata samu abinda zai katange Malik, da dawainiyya akan yara, cikin wannan yanayin wata rana, sun je beach. Suka haɗu da wasu yara masu kyau duk mata, nan Malik yayi ta kashe musu kudi ita kuwa ta dawo, gefe tana kallon su bakin ciki yana kara turnuketa. "A duniyar nan zaka iya chanza kome ban da ƙaddarar, domin kuwa ba zaki tab'a canza ƙaddarar ki ba,  kuskuren da kika aikata shi yake bibiyar shi, karki sake ki barshi ya tsallake kasar nan, domin daga ke har shi zaku ga samu zaku ga rashi, kuma kece zaki janyo haka " daga haka ya juya abin shi da jajjayen kayan shi, da sauri ta mike tabi bayan shi, tana mishi magana. Kallonta yayi sannan ya ce mata. "Bani tafin hannunki!" Mika mishi tayi ya dade yana kallon hannun kafin ya bude baki yace mata. "Kin kashe yarinyar da bata san kome ba! Sai soyayya. Lallai karki sake mijinki ya bar kasar nan, domin kuwa burinta zai cika. Kuma cikar shine ƙarshen ki, karki yarda ya bar nan ƙasar sabida kafin kashi yana jikinki, karki sake ya san inda kika ajiye kwalbar tare da zoben hannunki. Karki sake karki yarda ki rabu dashi."

       Shiru tayi jikinta yana kara mutuwa, anya zata iya barin Malik ya numfasa kuwa, tsoro take ji, kar wata rana kome ya kwab'e mata, mika mata wata sarka yayi, tare da cewa ta sanya a wuyarta, jikinta na rawa ta amsa, sannan yace mata. Karki rabu da sarkan. Muna nan zamu tayaki." Gyada kai tayi sannan ta bar gurin shi dan bai nemi kome daga gareta ba, ya dai bata abinda zata iya rayuwa da Malik ne.  Sai dai kash! Malik kowa ya tashi tsaye akan shi musamman mahaifiyar shi.
         ***
Kwanaki na tafiya mu kuma burinmu yana kara yawaita, wasa wasa yara na tun suna kiran sunan Kaka, har suka daina, gashi bata zo ba. Asalima kamar tayi battar dabo ne a raina nace. Tabbas! Da ba bata yarana ta gudu dasu fa? Allah Nagode maka da baka bani ikon bada su ba, ai da na mutu da kwanaki na, dan nayi imani sata rana Malik zai nime ni. Dan haka ya cigaba da sana'a na ina kuma kokarin kulawa da Yarana na saka ido akan su, dan bana yarda da nabarsu da kowa, wani munmmunan al'amari da ya same ni, kawai ina kwance aka kira ni a gurin aiki, dan haka da wuri na tafi, ina zuwa na samu munyi baki. Nan suka shiga mana tambayoyi, tare da wasu abokan aikina, ba tare da wani abu ba, kawai akace an dakatar damu, sabida muna cikin ma'aikatan bogi. Kamar zan fadi dan tashin hankali, karshe suka tura mu, ministry. Wai muyi comfirming kanmu, nayi kuka a ranar. Sabida wata nawa basu biya mu hakkin mu ba, yanzun kuma dakatarwa kuma babu ranar mai damu. Ina barin asibitin na nufi gida, dakyar na kira Khady ina kuka na gaya mata, ita da kanta tace min, "baki musu kome ba?"  Shiru nayi kafin na tuna ashe akwai wani likita da aka turo shine, asibitin mu aiki. Abun haushi yadda kuka san taure haka ya takura mana, kuma babu ruwan shi da budurwa ko matar aure, dan haka kusan mu hudu da yasa aka dakatar damu. Nan na gaya mata, hmm ! Tace min sannan tace min. "Karki damu, amma Allah zai saka muku, sannan naji ai dayawa sun fada cewa, bawai shi yake bin matan ba, sanya shi ake yana nimo yan matan, kiyi hakuri kome da lokacin sa, kuma Maman Malik bata zo bako." "Bata zo ba, idan tazo kiyi hakuri ki bita domin san zata bukaci hakan, shi kuma d'an iska karki damu karshen cin abincin shi yazo!" Haka muka tattauna, sannan muka yi sallama, ina zaune na saka yaran a gaba. Ina girmama laifin da nayi, domin na manta da iyayena. Na bar kowa nawa. Kamar wacce aka ya kusa na tashi na shiga hada kayan mu, zan tafi gombe. Yadda muka shirya tsaf, ba zaka ce muna cikin damuwa ba. Muka bar garin kashere. Koda muka isa unguwar mu, kai tsaye na nufi gidan mu. Duk da akwai nikab a fuska na, sabida bana son damuwar mutane, ya sani sakawa, ina shiga gidan mu na d'aga tare da sallama. Juyawa suka yi ganin yaran dake biye dani. "Ayeeriri nanaye! Lallai ribar bariki ya tabbata, Baban Inayatu zoka ga Inayatu har da ribar bariki, lallai lale maraba, irin wannan tagomashin arzikin haka?" Sunkuyar da kaina nayi, tare da kallon yadda Baba ya koma kamar mahaukaci, kallona yayi sannan yaga ina kallon kofar d'akin Mamah, murmushi yayi sannan yace min. "Da alamu baki san uwarki ta mutu ba, sabida bakin cikin shigarki duniya! Dama ai ba wani abu bane mai zafi gado kika yi! Kuma kin tabbata tunda ta iya biyo namiji ta tsallake maganar iyayenta, kema ai baki yar a kasa ba, Kai ji yara  wannan Baturen ne da ya aurenki kuka haihu dashi ko a bariki kika kwaso shegu kyawawa haka." A hankali na juya zan fita domin bana iya rike kaina, har na isa bakin kofa, na juya tare da goge fuska na, nace mishi. "A wannan lokacin niman kusanci ga mahaliccin ka ya dace dakai! Hmm! Yayi kyau Ubangiji yana jin mu yana ganin mu, shi zai fidda gaskiya kome d'acinta. Na Barka lafiya." Na rike hannun yarana na, ban san me ya hanani kuka ba,. amma kuka ne a cikin zuciya ta, Mamah na ta rasu bamu hadu na, wannan wata irin masifa ce.". Daga nan asobitin mai Nassara na wuce niman Dr Ishaq, aka ce min yabar garin, musamman asibitin, innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, Ya Allah..na fada a hankali. A gaggauce na koma kashare abinda idona ya hango min ya sani jin kamar zan fadi kasa, kayan mu aka watsar min a waje, Dr Jamil na zaune a samar motar shi, yana gani na ya sauko daga motar, "Inayatu Rahman! Toh dama na gaya miki bijire min dai dai yake da barinki kauyen nan, ga sakamakon haka,"  "Allah ka duba maraicina da yaran da ka bani Ya Allah karka bari wasu su wulakantanmu, Ya Allah na kame kaina daga fasadi Ya Allah karka bari wani ya cutar damu, Ubangiji kimata yake son tabawa, Ya Allah al'amarin aurena zan kar...." "Ammah! Kaka!"... Hello idanuna yana yaji sosai! Mu hadu gobe.

KOME DA LOKACIN SA {COMPLETE}✓Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin