Chapter 29

1.4K 165 38
                                    

*_KOME DA LOKACIN SA_*
    https://my.w.tt/0rQUEQnPVab
            Chapter 29
Everyone thinks of changing the world, but no one thinks of changing himself.

.... Ban san yana gaba na, ba tunda hankalina da kaina yana bisa jakata, sai gara goshin mu, muka yi lokaci guda nayi baya zan fadi. Cikin wani irin zafin nama, ya kai hannun shi bayana, yayinda kome na hannuna ya watse, idanuna a rintse wani mugun tsoro ya kamani, dukkan hannuna biyu suna bisa kirjin shi. Kura min ido yayi cikin nutsuwa, ga kuma yadda ya tsaya ina stylish cike da mamaki tare da dinbun al'ajabi yake kallon Eyelashe ɗinta, wanda suka mike zara zara bakinta kuwa ta dan cune shi gaba,sannan fuskarta da ta kwaɓe shi kamar zata fasa kuka, har yanzun dai bata bar yaranta ba. Lokaci guda yaji zuciyar shi tana azazzalar shi da ya ambaci sunan ta, amma tsoron kar tace Mishi ba ita bace ya sashi shagala da kallon fuskarta wanda yake cike da annuri, shi kanshi ya manta da inda suke dan a bukace yake da niman wanda ya san inda take sai gashi Allah ya nufa taron nake kolin lafiya ta duniya ta haɗa su. Cikin wani irin yanayi da tsoron gudun karta ba ita bace, ya sashi bude bakin shi kamar me ciwon hakori yace "Inayatu Rahman Ahmad." Cikin wani irin yanayi na bude idanuna akan shi, tare da kafe shi da ido, cikin tsannanin kewar shi kura mishi ido nayi  ban san me zance nake ji ba, amma zuciyata har wani irin bugawa take, sake riƙe rigar shi nayi domin gani nake kamar bashi bane, sake lumshe idanuna nayi, sannan na kuma buɗewa a hankali, bakina na rawa, amma na kasa furta kome,  Tafin mutane ya dawo damu yanayin da muke ciki, cikin sauri na ture shi zan fad'i ya d'ago ni da sauri, sai da kirjin mu ya kuma haɗuwa, cikin tashin hankali na yi maza na janye daga jikin shi. Murmushi yayi tare da kallon fuskokin mutanen gurin a hankali ya furta " she is my Wife! Nurse Inayat Ahmad. Mrs Ishaq Ahijo." Take kowa ya watse tare da nuna mishi bajintar da yayi, ko da yajuyo nayi nisa, domin kunya ce ta kamani, abin da muka aikata. Da sassarfa ya iso gurina. Yana hakki." Kin yi mamakin gani na?" Banza nayi dashi sannan ya kuma wurgo min tambaya! "Me yasa baki waiwayi baya ba?" Wani b'acin rai ne ya kamani ban san lokacin da nace mishi."meye a bayan!" Na juya tare da niman bayan." Inayat!" "Please! Ishaq, bana son damuwa. Ina cikin wani Uzuri ne!" "Amma ki saurare ni!" "Koma meye kabar shi bana bukatar ji! Tunda da saka hannunka ya tozartani! Da wancan ranar kome bai same ni ba, da kai da Malik kun lalata min Futures dina, yanzun da ka..." "Bashi bane! Kin biye Mahaifiyar!" Murmushi me ciwo nayi sannan nace mishi."Duk cikin makircin da kuka shirya min,.ta hanyar bakanta min rayuwa da yayi sanadiyar mutuwar mahaifiyata!" Zaro idanu yayi waje, cike da mamaki, "waye ya gaya miki kece sanadiyyar mutuwar ta?" Banza nayi dashi na nufi inda zan sayi ruwa da drinks, "Inayat! Mahaifiyarki a gidan su ta rasu! A gaban mahaifinta da danginta!" "Ni wanda ya gaya min ba zai min karya ba, ya ce min sanadiyya tace ta rasu,tunda na shiga duniya!" Waya ya ciro a aljuhun shi ya bude ta tare da kira, tan shiga ya ajiye min, "zoka dauki abarka." Cikin b'acin rai da na sanya shi ya dawo gaba na, ya tsaya min. Sai duk na diririce! Zuba min ido yayi kafin yace min. "Ki buga wayar da kasa shine zan fahimci taurin kanki. Kuma aka tashi kika yi tafiyar ki, sai na gayawa Dattijo Hammadada, ba iya shi ba hatta Balkisu da Zehrah, tare da Nusaiba da Mariam. Fahimci abinda kika min, ruwanki ne ki amsa wayar ruwanki,ki fasata zan iya sayan goman ta ba tare da naji ko Dar ba." Cikin tsiwa na murguda mishi baki sannan nace mishi. "Waye ba zai iya saya ba, dadin abin ni ba." Yadda ya juyo min a zafaffe ya sani had'iye maganar, murmushi yayi sannan yace."karamar mara kunya na zata zaki iya cigaba da maganar ne." A kasan raina na ja tsaki tare da cewa. Dalla dube shi mutum sai kace bishiyar kuka, ba dole ba had'iye maganar ba, tunda ka tawo zaka mauje ni. Yadda na kura mishi ido cikin takaici da jin haushi. Ya sashi kyalkyalewa da dariya yana kallona. Duba wayar nayi tare da ganin sunan Mariam, a hankali nasaka a kunne na. "Hello Hamma Ishaq!" Ta faɗa a sanyayye, kasa magana nayi dan ban san me zan cewa kanena ba, a hankali na zare wayar ina kallon shi, idanuna cike da kwalla, na ajiye mishi wayar nace mishi. "Don Allah kace masu na mutu." Daga haka na barshi a gurin, fita nayi daga gurin taron baki daya, na nufi wani gurin na zauna, tare da kifa kaina, ina kuka. Zama yayi tare da cewa. " Bazan iya gaya musu kin mutu ba, amma zan baki lokaci idan kin bakaci sanin inda suke zan miki jagora, Ya mijinki yana nimanki kuwa.?" Juyawa nayi na kalle shi idanuna cike da kwalla nace mishi. "Mutumin da ya iya Mantawa da Mahaifiyar shi, Ni wacece da ba zai iya Mantawa dani ba."  Shiru muka yi kafin ya kalli agogon shi ta zallar silver, saura minti goma a koma taron, "kina nufin kin san kome akan shi kenan?" Girgiza kai nayi ina ƙoƙarin share kwalla ya mika min hanky, "ina tare da mahaifiyar shi.." cike da mamaki, yake kallona, kafin ya mike, "i holp dai babu wani relationship mai tsayi a tare da ku, bayan abinda ya faru?" Shiru nayi tare da share zancen na kauda kaina. Yayi saurin tare ni, "tambaya nayi zaki wuce Ni?!" "Amsarka bata nan, idan kana bukatar shi. Sai ka bari idan an tashi." Ji yayi kamar zuciyarshi zata daka tsalle ta diro waje, tsabar tashin hankali, ba dai Malik ya ja mishi hanyar rasata ba kenan? Ya tambayi kanshi, ganin bai da me bashi amsar ya sashi bin bayanta. Koda suka koma ciki. Anyi jawabai tare da nuna musu muhimmancin, basu horo da za ayi na tsawon wata shida, idan sun kammala zasu kuma zuwa kasar Ingila taron kasa Da kasa, amma dole sai wanda suka samu damar yin nasara a bada horon. Haka muka tashi lokacin Sa'idu yazo ɗauka na, Babu yadda Ishaq bai so mu tafi ba naki, saboda kare kimar aurena, muna isowa gidan. Na samu Mahnoor tazo. Murmushi ta sake min sannan tace min. "Don Allah zoki tayani Bawa Ammyn hakuri, na kawo kaya amma taki saya wai sai ta dauki na kudinta da take bina." Murmushi na sake mata a karo na biyu, sannan na kalli Ammyn nace mata.", amma dai." "Jeki huta ki rabu da ita, aron kudina tayi kusan shekara daya, shine da Allah ya tashi kamata, ta kawo min dan ta kome da lokacin sa, lokacin da ta amsa ta manta zata biya, idan na tuna mata sai ta kau da kai wai na yafe mata shine Allah ya matse min ita yau ta kawo kayanta sun mata yawa, wai dan renin Hankali wai na biya, Ni kuma ba zan biya ba, tayi lokacin ta nima lokacina ne yanzun" kallon su nayi sun bani sha'awa, yadda take sakewa da yaran sai ta tuna min da Mama, murmushi nayi sam na manta da Dr Ishaq a waje, sai da Haysam yazo yace min. "Ammah Anoosh, kin manta da bakon ki fa." Dafe goshi nayi sannan mike nace mishi, "don Allah kace yayi hakuri, yaje kawai."  "A'ah kace ya shigo" kallonta nayi ta ce min. "ba ayin haka!  Ki tawo da mutum ki barshi yanzun kuma kice ya tafi." Fada tayi min sannan tace na wuce na sauya kaya sai na fito. Wucewa dakin nayi na fara gabatar da sallah sannan nayi wanka na sauya kayana, sannan na fito na same shi har lokacin yana zaman jirana, sai hira suke da Ammyn, murmushi nayi mata. Ta harare ni. Sannan tace min."Yanzun yake gaya min ashe kun san juna tun a gombe,. Shine kika bar shi a waje."  Sunkuyar da kai nayi tare da addu'a Allah yasa bai sake baki ba.  "Eh! Hmm!". Zan yi magana yan makaranta suka shigo da mugun gudu, tare da hayewa cinyata, "Amma yau munyi tuwatu! Da bulutu. Hal muka jana oton wannan bad man da yayi hurting dinki, ya m caki kuuka." Zaro idanu nayi tare da toshe mata, baki kallona Ishaq yayi cikin nutsuwa, tare da tabbatar da zafin haushin abinda Malik yayi mata, mik'ewa yayi zai fita, ya kalli Madam Azizah yace mata. "Ammih zan tafi, Yaran ya sunan su?" Itama jikinta yayi mugun sanyin tace masa. Namijin Aliyu Anoosh Macen Rukayyah Anoosha! Baki gaya mishi sunan su bane?" Ta jefo min tambayar,"a'ah em na ga" murmushi tayi sannan tace min, "ki nutsu ki  rakashi." Yadda tayi maganar ya sani fahimtar ranta ya b'aci, ina raka shi waje ya juyo a fusace, kamar zai mare ni, sai da nayi baya kad'an, " me kike nufi? Mahaifiyar shi ce fa! Kike gayawa Yarki ta tsane Ubanta, dama yayi miki shaidar rashin tarbiyya! Kuma kin nuna hakan! Wannan ba halin Inani bace, Inani ta rasu, mahaifin ta yana me yafe mata, haka ta tarbiyyar ta da Yaran da suka sadaukar da farin cikin su domin goge laifin Mahaifiyarsu, amma ke har kin sami damar, kara aikata abinda wancan Mahaifinki ya aikatawa kanwar Mahaifiyata, wallahi kinci darajar auren dake kanki, da sai na miki shegen duka. Sakarya kawai!" "Eh naji ina ruwanka! Kamar yadda ya ja min tashin hankali wallahi nima sai na rama, gwara tun wuri ka juya kabar nan." "Ni kike gayawa magana?" Murguda mishi baki nayi na juya zan tafi ya dawo dani tare da falla min mari, "na hukuntaki a matsayina na dan uwanki, ki jira kiga yadda zanyi dake, a cikin Asibiti daya muke ba, zaki gane baki da hankali. Sakarya an gaya miki. Kuma ki je ki goge haukar da kika koya mata ko kuma na gayawa Itama Maman shi tasan da sha-sha-shar da suke zaune da ita, wannan rashin kunyarki shi zai ja miki tashin hankalin a rayuwarki tunda baki horu da abinda Malik yayi miki ba.". Yana gama fadar haka ya juya yabar Ni cikin zubda kwalla. Dan na bashi haushi inji shi. Ni kuma ban ga abin jin haushi ba. Koda na dawo, cikin gidan na goge fuskana ta, bani labarin yadda ta dawo da Ishaq abuja tayi sannan cikin nasiha, ta shiga min fada, tare da nuna min illar muzanta mijina, kasa hakuri nayi sabida har yanzun ina jin zafin marin da Ishaq yayi min,  a hankali na bata labarin irin wulakancin da Malik ya min, amma ban gaya mata sunan shi ba, cikin kuka nace mata. "ammyn tafiya yayi ya barni ban san wanda ke kaina ba, sai da na kwana na wuni ban san meke faruwa ba, Karshe mahaifina ya kore ni, bayan ya aureni a wulakance, Mahaifinta ta rasu Sabida bakin cikin abinda ya faru, wai don Allah idan ban gina k'iyayyar shi a zukatan yarana ba dame zan fanshe abinda yayi min, nifa baki daya ya lalata min, tare da sanyawa kowa ya guje ni, taya bazan rama abin da yayi min ba." "Amma ayita sara ana duba bakin gatari kiyi hakuri da abinda yayi miki, sannan ki saka a ranki zaku shirya. Mrs..." Inji Mahnoor, takaici ta kara min dan haka ta juya tare da ɗaukar yarta, sannan tafita tana mana sallaam, miki min wasu kaya tayi. Sannan tace min. "Wannan man shafawa ne, sai Vitamin E. Kingan su ba sha ake ba, toh zakina shafawa ne da bai, musamman face dinki, sai kuma. Wancan feminine. Shi na tsarkine.". Jan hannuna tayi muka fita cikin dariya tace min "wai! Kice Yayana bai miki ta wasa ba first night! Wai har na hango irin wulakancin sa yayi miki, shi yasa nake saka Ammyn ta haɗa miki har da maganin gyaran jiki domin kafin ya dawo ko ina ..." "Allah yayi min tsari da rayuwa da mutumin da bai san ciwon kanshi ba, kiyi hakuri, ko duniya ta rage daga ni sai shi, bazan koma gare shi ba, Ba zan tab'a ba, Malik ya cuce ni! Kiyi hakuri da abinda na fada amma, dan uwanki ba abokin rayuwata bane, tuni na manta da Pagen shi, don Allah idan kina son na cigaba da zama a cikin gidan nan ki bar kawo min zancen Malik dan na manta dashi baki daya, na manta da rayuwar shi. Nagode" na juya a hankali tare da barinta a tsaye. Tana mamakin abinda na gaya mata.🤦🏼‍♀️ Na gaji...

KOME DA LOKACIN SA {COMPLETE}✓Onde histórias criam vida. Descubra agora