Chapter 31

1.3K 165 20
                                    

*_KOME DA LOKACIN SA_*
  https://my.w.tt/7vnB4fQkYab
            Chapter 31
Truth, like gold, is to be obtained not by its growth, but by washing away from it all that is not gold.

Zaro idanu nayi waje, tare da b'ata fuska, na duba wayata na turawa Dr Ishaq sakon. _Ni fa babu inda zani! Don Allah kayi wani abu mana!_  sannan na mai da wayar cikin jakata, take naga wasu daga cikin mutanen da nazo na samu, suna min kallon kaskanci, ko a jikina da sun san wacece ni a nan Asibitin ba zasu damu kansu dani ba, ina isa Office din mu zan ajiye jakata, naji suna magana. " Baki ga yadda ta makalewa Dr Ishaq ba? Shegen girman kai, sai kace tafi kowa kyau, an naji wai yar alfarma ce?" "Hmm! Hafsat kyale ni da takaici yaushe tazo da za a
turata  karatu kasar waje, yau shekaru biyar ina aiki da Asibitin ban cancanci zuwa bane?" Cikin takaici, na juya na kalle su na ga duk sun juya zasu fita nace musu. " Kuyi kokarin ganin kun nemi abinda zaku rufawa kanku asiri ba hassada da kyashi ba, idan da zan bayyana muku matsayina a cikin asibitin nan, toh wallahi baku isa a dauke aiki ba, dan haka kuyi hidimar ku nayi nawa, idan kuma kuna sha'awan a sallame ku ni toh ba damuwa." Daga haka na juya nayi ficcewata, na Barsu tsaye suka jin haushina, Ni ina ruwana.  Su suka sani tunda suke da wahala, duk inda na gifta maganar daya ce daga zuwa an min alfarma har na samu damar tafiya course wannan abin ya musu ciwo, ganin baki yayi yawa ya sani tafiya har office din Admin! Mutumin kirki. "Inayat Ahmad ko?" Gyada kai nayi sannan na gyara zama na, nace mishi. "Baba! Don Allah a janye suna na a cikin masu tafiya London,ni bani son don Allah."  Jan numfashi yayi sannan yace. "Bani ce na zab'e ki ba, Madam Azizah ce ta bukaci hakan. Bani ba sannan idan wani yana jin zafin haka toh ya sami Madam Azizah ba ke ba, dan haka ki kwantar da hankalinki mutane haka suke."  "Shi kenan!" A hankali na bar Office din, dukka inda na gifta na gifta sai anyi magana abun har ya dame ni, babu shiri na bar asibitin na dawo gida. A gajiye na zube a manyan kujerun falon, ina sauke ajiyar zuciya. Saukowa Ammyn tayi tana murmushi tace. "Yanzun ake ce min kin shigar da korafi baki bukatar  zuwa London. Akan me?" Gyara zama nayi sannan nace mata. "Dayawa suna ganin kamar karfi da yaji aka sanya ni, shi yasa na shiga gurin Baba, sai yace min wai kece kika kawo ni!" Zama tayi sannan ta kura min ido, sannan tace min. "Nice na bukaci hakan? Domin ai ilimi zaki karo," shiru nayi sannan nace mata. "Ni bana son tafiyar! Sabida kawai bana jin haka aka  a raina, don Allah ku taimake ni a cire zuwa na din nan."  Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace min. "Toh bari na duba, Insha Allah kome zai zo miki daidai kinji ko?" Gyada kai nayi, sannan na mike zan tafi daki tace min. "Akwai wata kawata a can Mrs Muhmood! Zaki zauna a gidanta, zata miki duk abinda kike bukata domin ina son ko zama high classic lady, wacce duk inda zaki zauna babu wanda ba zai daraja ki ba, ina son ki zama wayayyar mace, me matuƙar aji da sanin ya kamata, yadda koda wancan mijin naki ya dawo ba zai iya gane ki ba, akwai Class na musamman da za a koya miki yadda zaki kula da kanki da kuma mijinki, duk na biya saura ke ki isa a fara karatu, kuma sau uku ne a sati, idan kin dawo daga makarantar ku, zaki shiga wannan ajin da yamma, Inayat kiyi kokarin bawa mara da kunya, don Allah kiyi kokarin ganin kinyi Karatun ki, sai kuma kimarki, ki tayani kare kimarki. Don Allah." Kusan nasihar da tai min ya kashe min jiki, asalima sai jin ba dad'i nayi, gyada mata kai nake kawai, har ta dama na mike tsaye na nufi dakin mu, Littafin da na gani a d'akin Neemrah na dauka tare da kadewa. Na shiga ban daki. Ina gamawa, Uzuri na fito na  gabatar da sallar, ina idarwa na kwanta. Tuni barci ya dauke ni. Diro min kai Anoosha tayi tare da saka ihu, tashi nayi na ganta kwance, a jikina tana sauke ajiyar zuciya, rungumo ta nayi muna cigaba da.
   ***
Daga nesa ta hango matar ranar, da tazo suka gaisa da MALIK, murmushi tayi sannan ta dauki mayafinta ta rufe fuskar ta, tare da ɗaukar wani abin gyara farce dake cikin jakarta, ba tare da damuwa na, ta nufi hanyar da matar ta shiga, tabi bayan Matar, a tsora ce ta juya. Kafin yayi magana Zeeh ta dauki wannan abun ta yanka mata fuskarta sai da ya fara zubda jini, ta kuma saka abin ta yanke gefen wuyar matar, sannan ta nufi hanyar fita abinta. Ba tare da ta damu da shure shure, bata damu ba. Bayan fitar ta daga Mall din, canza kayanta tayi ta samu wani guri ta juya ta bar gurin.  Ta koma cikin motar su. Can sai ga Malik yazo suka bar gurin. Cikin jin dadi ya harari mall din. Tunda suka isa take kallon shi ganin bai da walwala yasata had'iye yawun takaici, tace mishi. "Wai meke damunka ne?" Murmushi yayi sannan yace mata. "Kawai bana ganewa jikina ne!" Ya kwanta a doguwar kujeran da ya kawata falon, wuce shi tayi bata ce mishi kome ba, tana shiga d'akinta ta cire wani hand gloves, daga hannun ta, ta shiga ban daki tayi wanka, sannan ta fito. Tana kallon kanta a madubi, cikin nutsuwa ta gama shafa mai da turare, sannan ta saka dogon riga me armless, ta falon da yake, ta zauna tare da kunna tv tana kallon wata tasha da suke dan sukarka. Waƙoƙin batsa. hankalin ta yayi nisa, aka shiga buga kofar gidan, mik'ewa Malik yayi sannan ya fita, yan sanda ya gani, suka gabatar da kansu. Juyawa yayi tare da kallonta, itama shi take kallo. A sanyayye ya koma tare da cewa. "Ki haura ki dauko mayafinki, ki zo muje." Ji tayi jikinta ya kama rawa, tabbas abin da tayi bata bar shaida ba, amma taya kome ya faru. Da sauri ta haura sama ta dauko mayafinta suka fita, har office din yan sanda suka je da ita, Malik yana bayan su. Tunda suka shiga, ake mata tambayoyi tace bata san kome ba, karshe dai suka nuna mata videon dake nuna alamu ita daya ta shiga dakin da aka samu gawar matan, bayan matan ta shiga da minti biyar. Cikin damuwa Malik ya kira lawyer din shi ya gaya mishi sannan suka je gida aka dauko takardun ta na asibiti, take aka shiga tattaunawa, tare da nuna musu shaidan tana da birkicewar ƙwaƙwalwa. Yadda likitan yayi bayani, sai ya baka mamaki, bawai sun boye gaskiya bane, sai dai basu da amfani idan basu gayawa yan sandan Matsalar ta ba, kawai. Dan haka abinka da turawa aka kuma kaita asibitin sakamakon daya ne, dan haka da tace ba ita bace sun yarda kuma suka tabbatar da cewa, koda ba ita bace tayu lokacin da abin ya faru ciwon ya motsa,kuma da aka sake bincike akan abinda aka yi kisan babu zanen hannunta, wannan ya kara wanke ta, kallonta Malik yake, jikin shi har tsuma yake, ya saka an wanke ta ne, dan ya nuna mata iyakarta, koda suka dawo gida, wucewa yayi zuwa dakin shi ya rufe kofar, a hankali hoton Neemrah ya fado daga wardrob din shi na dakin, tsugunawa yayi ya dauka, tana sanye da kayan ta na aikin Jinya, idanun shine suka cika da kwalla, sabida tausayin yarinyar, wadda yake kuma nazarin mutuwarta, banbncinta da Inayat! Dan kadan ne! Tana da wushirya siriri, haka hancinta yana da tsayi sosai, yayinda na Inayat wushiryan yake da dan fadi kadan, hancinta yana da tsayi ba sosai ba, amma zagayen fuskar su iri daya ne, kwayar idanun su ya sake dan banbanta su, ita nata kwayar idon Blue eyes ne, Inayat kuma brown ce wacce wasu suke kiran shi zaiba! Sai Eyelashe ɗin su iri daya ne. Goge hoton yayi, sannan ya ajiye tare da kallon laptop din shi, ya fara duba wasu abubuwan, a hankali ya mike zuwa ban daki yayi alola, sannan ya gabatar da salla. Yana zaune a gurin Zeeh tayi ta buga mishi kofa, banza yayi da ita dan bai ga amfanin mata magana ba, karshe da ta ishe shi ya bude kofar. Ya caka mata bakar magana wanda yasata tayi ta ihu, kallonta yayi tare da cewa. "Ke bakar ƙaddarata ce, ban da ikon tsallake ki, shi yasa nake zaune dake alatilas,  ke a tunanin ki, dan ki kashe Suzzaine, zai sanya gaskiya ya boyu ne, na kin kashe ta, sabida ranar mun yi magana da ita,bayan ni dake muka yi alkawarin babu kishiya, kema kuma babu cutar da wata mace, wai na tambaye ki sabida ke daya aka yi Ni ne? Sabida kece aka halicce ni ne? Me kike so na miki? Bana bin mata? Bana ra'ayin mata? Ke Ni mace bata ra'ayina, amma sabida jahilin tunaninki zanyi aure ko nace zan duba Alamarin sai ki mutu don Allah, sakarya sha-sha-sha, wacce ya kasa, rike kanta tunda kika nemi kashe kanwarki wacece zata tsira a hannun ki, dabobbi basu aikata abinda kike aikatawa, kin nisanta ni da kowa, sabida ra'ayin kanki, ke ba haihuwa ba, ko ba iya girki ba, ke ba juriya a gado ba, sakarya me abun kunya, toh ko kina so ko baki so, aure anyi shi tuni. Wawuya kawai b'ace min da gani, ki fara niman taimakon Allah kafin kome ya lalace miki mujirima wacce ibada bai dame ta. Kar na kuma ganinki a kofar d'akina." Sake baki tayi, tana kallon shi, hawaye na zuba mata, yau zata yi ta ta ƙare, ba zai kuma, cin mutuncin ta ba. Tana dawowa d'akinta ta rufe, a hankali ta bude wardrob ɗinta, kwalbar da ta saka Zuciyar namijin kare ta dauko alluran ta tayi ta cakawa, har sai ta ta gama, sannan ta mai da. Tana kuka, zoben hannunta ta cire ta yanka hannunta jini ya zuba a kai, sannan tayi wasu surutu, sai ga shi ya tashi sama bude mishi kofa tayi ya fita. Can tana tsaye ya dawo, murmushi tayi domin zoben ya fita da jini, a wannan lokacin da ya tafi gurin Malik yana cikin b'acin rai, sosai dan ya a tsaye ya kasa zama, dan haka koda ya shigo dakin shi, diga mishi jinin yayi sannan ya juya ya fita, shi kuma MALIK b'acin rai yasan ya shi kasa zama,  karku manta Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, ya umarce mu, da zaran ran mu ya b'aci toh mu zauna, muna niman tsarin Allah akan ingiza mu da shaidan yaƙe, idan haka bai damu ba, mu Kwanta. Muna ambaton Allah. shi kuma MALIK ya manta ko nace zafin zuciya ya hana shi sukuni, dan yana kara jin kamar yayi ta dukarta har sai ta daina numfashi, kawai yana cikin wannan yanayin yaji kamar ana rufe mishi bakin shi, lokaci guda yaji kome akanta ya manta, sannan wani tausayin ta da dan shakkar ta, ya darsu a zuciyar shi. Ga baki daya ya manta da kome, sai ma kauda zancen abun da tayi yayi a ranshi, yana kuma tabbatarwa ba ita bace... 
                Lokacin da zoben ya dawo ta maida shi hannun ta, tare da kallon wardrob ɗinta, take abinda Neemrah ta gani ya dawo mata. Mu koma baya... A ranar da Neemrah zata rasu, lokacin da ta isa cikin gidan tayi ta kwad'a sallama babu wanda ya amsa mata, har sai da ta isa sama, sannan ta bude dakin da take tsammani na Malik ne, kawai ta hango Zeeh da Baby Nadra, tare da wani mutum, suna yanka kare, ana watsawa Zeeh jinin shi. Abinda ya fito bakin Neemrah. "Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun Ubangiji na tuba." Da sauri ta rufe Kofar, kafin ta sauka ƙasa, an rike ta tayi tayi ta sauka. Ta kasa sai da Zeemalik suka fito, riketa suka yi zuwa dakin Zee ɗin, sannan suka danne ta, sai da Bokan ya gama lalata da ita, ya tari jinin gaban ta aka hada da aikin, shi yasa wani lokaci Malik ke tsananin tausayin Zeeh, dan sun fahimci yana  tausayin Nimrah. Haka bai musu ba,suka saka aka kunce birkin motar ta, Zeeh tace mata. "Zaki iya tafiya, amma ina me baki labarin ki ya kare, domin akwai ma'aikata na suna jiranki." Daga haka suka kunna mata motar, ta fita a gidan, duk. Har zuwa hatsarin da suka kirkiro mata. Murmushi Zeeh tayi tare da kwanciya, domin ta gama abin da zata yi, ta kuma yi imani zai biyo ta, sallah kuma tun da bai da gidan wuta da aljanna ba zata yi ba, taga me sata. Tana barci kamar a mafarki taji kamshin turaren shi, bude ido tayi cikin mamaki, ta shiga ture shi yana rarrashinta, yana bata hakuri. Can ta fashe da kuka, ta shiga mai maita mishi abinda ya gaya mata, tare da cewa. Ya rabu da ita, ta gaji. " Wallahi mutuwa zanyi idan na rabu dake, don Allah kiyi hakuri!" "Toh ka daina sallah akan lokaci!" Kura mata ido yayi sannan ya girgiza mata kai yace mata, "mafi kyawun aiyukan bawa ranar alkiyama, itace Sallah tayi kyau idan tayi kyau duk wasu aiyukanka sun yi kyau, idan bata yi kyau ba sauran aiyukanka sunyi kyau babu wani abu facce wahalar da kai a duniya, dan haka ko zabi wani abu ban da ibada ta.". Kallon shi tayi cikin kokwanto, anya maganin nan yayi aiki akan shi, mutum sai kace waliyin masu taurin kai na duniya baki daya, gefe guda kuma ya narke mata, yana bata hakuri. "Toh ka daina azkar!" Kallonta yayi tare da matsa boons ɗinta, yace mata. "azkar! Makamina ne? Kuma nayi imani dashi, duk wani Sharri da zaka tunkaro ni dashi Ubangiji yana bani nasara akan shi, dan haka, ki nemi wani abu. Ni kamar bawanki ne!" Shiru tayi sannan tace mishi. "Karka kuma min batun kishiya! Ko Haihuwa." Murmushi yayi, sannan ya rabata da kayan jikinta yana me sumbatar wuyarta yana fadin. "Ina da irinki me zanyi da wasu matan, me nake bukata a jikin wata mace. Bayan gaki a gabana, karki manta ni naki ne har duniya ta tashi, ba zan kuma b'ata miki rai ba, sai a rashin sani. Dan haka kiyi min duk hukuncin da ya dace idan nayi miki laifi."  Yana fadar haka yana natural exercise, sosai yake bump dinta yadda ya dace, kafin wani lokaci ta gaji, shi kuma bai kai inda ya dace ba. Dole ya cire tausayi ya murzata son ran shi. Kafin ya tsallake ta. Murmushi tayi domin duk yana cikin aikin maganinta, dole zai ta Binta kamar kare, domin an samo karen yana barbara ne, bai da hankali a jikin shi aka mata aikin da shi. Kuma kwalliya ta biya kudin sabulu, dan duk lokacin sa tayi amfanin da maganin, manta duk abinda tayi mishi yake yayi ta bita, wani lokacin idan taso wulakancin ta sai yayi kaza. Zata bashi kanta, ko yayi kaza. Haka zata yi ta bashi wahala kafin ya bashi haɗin kai, shi kuma yana samu sai ya sanyata kuka yake Kyaleta, yaji shi a gajimare. Sosai yana yawo yake Kyaleta... Koda ya fito magabri tayi dakin shi ya wuce ya tadda sallah, yana idarwa ya yayi addu'o'in, sannan ya koma aikin shi. A kasan ran shi yana jin haushinta, amma ba zai iya mata koda tari ne, sabida cika mishi ido take, dan haka ya tattara ta ya watsar a gefe, amma yayi alqawarin ba zai kuma Binta ba, tunda bata jin maganar shi. Sai abinda yayi mata take aikata, shi yanzun damuwar shi abu daya ne, amma ya manta abun.
    ***
,Yau da murna na tashi, ga Mariam da Nusaiba zasu zo min, ga kuma Khady da zata dawo. Dan har Ammyn ta roketa da tayi aiki da asobitin su, tace sai ta iso. Dan haka nice nake ta aiki, ina bada Umarni ayi wannan, a sauke wannan, dama jiya Hasshir yazo, Brother din Neemrah, tunda ya ganni yake mamaki, sai da ya Hadani da Mamar su, tana gani na ta shiga zubda kwalla, dan haka na shiga bata hakuri, ina gaya mata addu'a Neemrah take buƙata, toh yau tare muke dashi a kitchen din har su Kuwwah da Hajnan, tare dasu Anoosha, muna aiki. Duk abinda na sauke sai an zuba musu, koda Ammyn ta shigo gidan, dake tana yawan zaga ma'aikatan su da Asibitin su, duba wasu abubuwan, tana shigowa taga falon Babu kowa ana hayaniya a kitchen, dake dinning table guda biyu ne, idan zasu tafi makaranta sukan ci a kitchen din, idan masu aikin sun makara, idan kuma basu makare ba, akan jera a waje. Dan haka duk abincin da nazuba musu, sun dukufa akai, Haysam yace min. "Wallahi Addah, da na girma ko? Mata irinki zan samo, wacce zata cika min tumbina da abinci, ni fa wallahi ba zan yarda na auro mace me kyau irin su Hajnan, zan auro wacce idan abokaina suka zo, zasu kwashi dad'i, dan nima nan, irin wannan girkin. Ubangiji yasa Ya Malik ya dawo ku hadu ayi muku aure kullum naje gidanku kwasar Gara..." Faduwa serven spoon din hannuna yayi, kirjina yayi wani irin bugawa, na kasa aiwatar da kome, make keyar shi Ammyn tayi musamman da taga jikina yana rawa, tare da sake cokalin, "tafi can sakarai kasamu abinci sai surutu kake zabgawa kamar wanda ya samu wani abu, Hajnan me yasa baku mishi waiji ba, Inayat Nima zuba min abincin da Yasaka Aura sambatu, Nima naji irin dad'in da ya hana Hasshir magana." Murmushi yayi sanan ya cigaba da cin abincin. Baka jin kome sai karar cokala, "Ammah a kala mai!" Bayan na zubawa Ammyn, har zuwa lokacin jikina bai daina rawa ba, ina cewa a raina. "Da zaku san cewa dan uwanku ne ya cutar dani, da zaku juya min baya." Haka na gama na koma daki nayi wanka, tare da yin simple makeup, na fito, hango wayata tana ringing ya sani dauka. Na saka a kunne na." Toh ranki shi dad'e gamu nan mun iso, Dr Ishaq ya dauko ni, tare da Mariam da Nusaiba."  Cikin fara a nace mata. "Toh sannunku da zuwa."  Nace mata. Sannan naje na kamo Anoosha, nayi musu wanka na saka musu kaya, sannan na koma kitchen na samu Ammyn tana, cin abincin. Zama nayi a kusa da ita, murmushi tayi sannan tace min. " Duk mace idan ta isa mace! A guri hudu ake gane isarta! Daga jikinta! Daga girkinta! Sai mu'amalar ta da mutane, sai iya sarrafa harshe ta, wannan shine abin da zan kuma cewa ki mai da hankalinki, domin kuwa, dashi zaki rike wuyar kowani namiji." Duk sun watse ni daya ce sai ita. Ina tattara kayan da aka ci abincin. Sannan tace min. "Mazan yanzun suna son a bautawa tumbin su! Suna son a girmama cikin su, Kinga ya zame min dole na taimaka miki gurin  janyo hankalin duk wanda zaki zauna dashi.  Idan namiji yaci abinci yana niman hanyar da zai rage nauyin cikin shi, dan haka. Dole ki koyi juriya tare da hakuri, ki koyi shanye bukatar mijinki, yadda bai isa ya miki wulakancin ta bangaren tattalin shi ba, dan yasan yana moranki, kuma kema ya zame miki dole ki iya sarrafa harshenki, tare da nuna mishi  kina tare da shi. Bawai ina gaya miki dan Zaki yi aure yanzun ba, sai dai ina gaya miki yadda zaki rike wuyar mijinki ne." Murmushi nayi kawai, dan nasan tayi gaskiya take gaya min,tare da nuna min dabarun irin nasu na manyan mata, haka kawai zata zaunar dani, tana nuna min fitattun matan NGO, tare da gaya min irin gwagwarmayar da suka sha, da kuma zaman su Exclusive Ladies. A duniya da yadda suka rike career din su,  tanan take ce min duk wata fashion designer, tana son zama Best lady, dan haka suka fi mai da hankalin su gurin zama  model, dan haka ita zata so na duba daya daga cikin manyan attajirai na larabawa da turawa na gaya mata, wacce nake son role model dinta,, murmushi nayi sannan nace mata. "Ammyn dukkan su, anan duniya suke. Amma ni roling model dina, Suna dayawa da ba daya bace! Dan haka zan so nayi koyi da Nana A'ishah matar Manzon Allah, sai Nana Fatimah yar Manzon Allah, sai Khadijah matar Manzon Allah, sai Maryam Mahaifiyar Annabi Isah, tare da Asiya matar Fira'oun, wadannan sune roling model dina, dan halayyar su abin koyi ne a duniya,!" Rike hannuna tayi, sannan tace min. "Kinyi gaskiya! Kuma nayi imani kina da kyawawan halaye, kuma zaki zama hakan, tare da koyi dasu.  Sai dai ina son ki sani, ance ka nemi duniya kamar zaka barta ba, ka kuma nemi lahira kamar yanzun zaka tafi kabar ta, ki duba maganar da kyau, so nake ki zama tauraruwa wacce duniyarki take haskaka.. 
Don Allah kuyi hakuri! Muna hidimar biki ne! Insha Allah zaku ji ni zuwa dare🙏🏼 shi yasa ba baku dogon page

KOME DA LOKACIN SA {COMPLETE}✓Where stories live. Discover now