Chapter 41

1.2K 156 16
                                    

_KOME DA LOKACIN SA_*
https://my.w.tt/rrR4b6Zc7ab
              Chapter 41

 
If I had asked people what they wanted, they would have said ‘faster horses.
         

Ina kukene maza da Mata masoya kasuwanci, ga dama ta samu! Nesa tazo kusa! Ina masu sayan d'ai d'ai ko sari karku sake a baku labari, da arziki a garin su har gwara a garin mu, kai gwara a  dakin mu, karku sake wannan damar ta wuce Ku
Ku garzayo kampanin *Greenleaf biotech* domin ya tanadar muku kayayyaki sama da guda 4500, Kama daga abubuwan amfanin yau da kullum kamar sanitary pad, pampers, baby wipes, sabulan gyaran jiki, man shafawa, magungunan qarin lafiya da magance cututtukan zamani kamar (infection, BP, diabetes da sauransu), kayan kwaliyya, sinadarin rage kina da tumbi, takalma, jakunkuna, air frying pan (baya buqatar Mai wajen suya) da ma wasu da dama.

Zaku iya siya domin amfanin kanku da iyalan ku, sannan kuma zaku iya yin sari domin saidawa ku samu riba me albarka.

Domin qarin bayani ku biyo mu ta wannan link din👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

https://wa.me/message/XMECES32SQEPK1

Ko ta WhatsApp group👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
https://chat.whatsapp.com/BebpPIrkAPj1bfiqfZkkjH

     -------
Kallon ta yayi a raunane, kamar zai magana, sai tsintar kanshi yayi da jin tausayin kan shi ya tako a hankali ya zauna bai kuma d'ago kai ba, har ta gama abinda zata yi ta bar falon yana falon. Wasa wasa wuni guda yayi a falon sallah yake yadda shi. Sai da ta sauko ta gan shi zaune inda ta bar shi. "Baka tafi gidan ka ba? Na zata ka tafi ai." Gyara zama yayi tare da gyada kai yace mata.
"Aikin ce kar na tafi ko ina!" Murmushi tayi sannan tace mishi. "Ba haka nake nufi ba, kayi tafiyarka, kawai kasar ne bana son ka bari, ka zauna muma muna bukatar ka, gida babu mahaifinka babu wani namijin babba bayan kai, shi nake nufi bawai ka zauna ba.". D'agowa yayi a sanyayye zai mata maganar Inayat ta zuba mishi ido, "Bana son jin kome akan Inayat!" "Naji amma kiyi hakuri nayi Kuskure!" Yadda yayi maganar uwa ce kawai zata iya fahimtar kome akan halin da d'anta yake ciki. Amma adalci Inayat ta nima, sai yanzun ta kuma fahimtar dalilin da yasa Inayat bata kaunar maganar Uban yaranta, da take mata.
     Bayan kwana biyu tana lura dashi idan ya shigo dakin Inayat yake shigewa,dan tun ranar da ya leka yaji kamshin turaren ta, gabaki daya ya tare a dakin ko barci zai a dakin yake kwanciya. Haka ya kuma kara mishi kewar ta, da tsiwarta.  A sannu a hankali ya sauya daga yadda baka zato baka tsamani, ya zama mara son shiga mutane, sanan duk wani abinda yake mai muhimmanci ya ajiye, kawai ya zauna jiran abinda Ammyn zata ce mishi. Sannan tsakanin shi da Zeeh hantara, da tsana ƙarara yake nuna mata. Haka bai dame ta ba, dan ita kadai tasan shirin da take mishi.
            
           ---
Na shiga cikin dangi na, har gidan su Baba  naje, mutanen gidan. Sai kuka suke suna roƙon gafarar mu. Nayi murmushi tare da cewa. "Wacce kuka yiwa nasan koda tana raye, nasan ta yafe muku dan haka, ni babu wani abinda kuka min Allah ya yafe mana baki daya." Daga nan na dawo gida. Kusan kowa yasan na dazo ga Balkisu da muke tare kamar zamu koma cikin juna. Ina ta lissafin zuwan Ishaq. Dan haka nake ta kara Addu'o'in Allah ya tabbatar mana da bukatar mu.       Yarana har Mantawa nake dasu, wani lokaci kuwa so zo min sun sha danyen madara. Har mamaki suke bani, sun sake sai uban kiba suka yi kamar suna gidan Ammyn.

         ---
Tsautsayin cin duka ya kawo Dr Jamil  yasa zuwa Abuja, asibiti yazo ya shiga rashin hankali da yadda zaune tsaye. Cak kuwa Allah ya aiko MALIK, dai-dai Jamil yana faɗin. "Ina Inayat take! Yarinyar da ta gama zaman kanta, tare da tsarabar shegu, shi ne ɗan b'ata sunan Asibitin...". Wani iri duka aka kai mishi a keya, sai da yayi gajeriyar suma, kafin Malik ya farfaɗo dashi da duka kamar hauka, sai da Ishaq yazo ya janye shi. Yana nunawa Jamil yatsa. Na gargad'i. Dan zuciyarshi ta kai makura na b'acin rai. Jikin Ishaq ya kuma sanyi indai Har za a aibata Inayat ya haukace haka, toh ya ke nan? Dole ya fara jin wani irin yanayi akan auren shi da ita.

KOME DA LOKACIN SA {COMPLETE}✓Where stories live. Discover now